A Rayuwa Babu Abin Da Ya Kai Haƙuri
Daga Bashir Yahuza Malumfashi

•••••••
Haƙuri ginshiƙi ne na nasara da kwanciyar hankali a rayuwa. Rayuwa cike take da ƙalubale, jarrabawa da sauye-sauye masu wahala amma wanda yake da haƙuri shi ne ke cin nasara a ƙarshe.
Haƙuri yana koya mana yadda za mu ɗauki lamarin rayuwa da natsuwa da kuma yadda za mu rungumi ƙaddara ba tare da gunaguni ba. Ba kowane abu ake samu cikin sauƙi ba amma haƙuri shi ne mabuɗin buɗe kowace ƙofa ta alheri cikin sauƙi.
Idan mutum yana da haƙuri, yana samun natsuwa a zuciyarsa, yana kuma guje wa fushin da kan iya jefa shi ko sauran mutane cikin zalunci da kuskure. Akwai lokuta da dama da mutum zai fuskanci asara, ƙunci ko cin zarafi daga wasu amma wanda ya yi haƙuri yana nuna ƙarfin hali da hikima, to zai samu sauƙi daga bisani.
Allah Ubangijin sammai da ƙassai yana son masu haƙuri kuma yana tare da su saboda su ne suka fi kusanci da yardarsa kuma masu samun lada mafi girma. Alƙur’ani ya tabbatar mana da wannan, a lokacin da Allah (swt) a Suratul Baƙara, 2:155–156 ya ce: “Kuma ka yi bushara ga masu haƙuri, waɗanda idan wata musiba ta same su, suna cewa: ‘Lallai mu daga Allah muke kuma zuwa gare shi za mu koma.’”
Haka kuma Manzon Allah (saw) a wani hadisin Sahih Muslim, ya ce: “Haƙuri haske ne.” Wato haƙuri yana haskaka rayuwar mutum, yana sa ya ga abin da ke gaba da basira da nutsuwa.
Wannan shi ke ƙarfafa mana zukata kuma yake nusar da mu a kan haƙuri. Saboda haka, ya kamata mu koya mu riƙe haƙuri a kowane yanayi. A yayin jarabawar talauci ko arziki, cikin nasara ko faɗuwa, haƙuri shi ne asalin imani. Ke nan duk wanda ya rasa haƙuri zai rasa kwanciyar hankali da amincin zuciya. Rayuwa za ta kasance daɗi ne kawai idan muka yarda da ƙaddarar Allah, muka rungume ta da haƙuri da tawakkali.
Ya Allah ka sanya mu a cikin masu haƙuri a kowane yanayi na rayuwa. Allah ka ba mu dacewa da abin da ka alƙawarta wa masu haƙuri. Amin-Summa-Amin.
_______________













