• About us
  • Advertise
  • Careers
  • Contact
Friday, April 24, 2026
  • Login
Taskar Gizago
Advertisement
  • Gida
  • Labarai
  • Sharhi
  • Gumbar Dutse
  • Dausayin Kauna
  • Gizago
  • Sarauta
  • Sinadari
  • Adabi da Nishadi
  • Barkwanci
  • Shanshani
  • Hotuna
Taskar Gizago
No Result
View All Result
Home Babban Labari

Matsalolin Tsaro: Ƙungiyar ‘Yan Jarida Ta Arewa Ta Shirya Taron Neman Mafita

BABBAN LABARI

Bashir Yahuza Malumfashi by Bashir Yahuza Malumfashi
November 7, 2025
in Babban Labari
0
Matsalolin Tsaro: Ƙungiyar ‘Yan Jarida Ta Arewa Ta Shirya Taron Neman Mafita

Ƙungiyar 'Yan Jaridar Rediyo Da Talabijin Ta Arewa ta shirya taron neman mafita ga matsalolin tsaro

17
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterWhatsappEmail a Friend

Matsalolin Tsaro: Ƙungiyar ‘Yan Jarida Ta Arewa Ta Shirya Taron Neman Mafita

Daga Bashir Yahuza Malumfashi

Related posts

Ɓatanci Ga Manzon Allah: Musulmi Sun Buƙaci Gwamnati Ta Hukunta Fasto Emmanuel Garba?

Ɓatanci Ga Manzon Allah: Musulmi Sun Buƙaci Gwamnati Ta Hukunta Fasto Emmanuel Garba?

April 14, 2026
Yadda Za A Magance Matsalolin Tsaro A Najeriya – Sanata Ndume

Yadda Za A Magance Matsalolin Tsaro A Najeriya – Sanata Ndume

April 8, 2026
Ƙungiyar ‘Yan Jaridar Rediyo Da Talabijin Ta Arewa ta shirya taron neman mafita ga matsalolin tsaro


                      _______________
A yayin da matsalar tsaro ke ci gaba da barazana ga zaman lafiya, cigaba da kwanciyar hankali a faɗin Najeriya, musamman a Arewa, Ƙungiyar ‘Yan Jaridar Rediyo Da Talabijin Ta Arewa (Arewa Broadcast Media Practitioners Forum – ABMPF) tare da haɗin gwiwar Gwamnatin Jihar Kebbi, za su gudanar da taron tattauna neman mafita dangane da matsalolin tsaro.

Taron, wanda zai gudana a Birnin Kebbi na Jihar Kebbi, za a gudanar da shi ne a ranar Litinin mai zuwa.

Taron, mai taken “Arewa: Barazanar Wanzuwar Ta Da Tsaron Ƙasa,” an tsara shi ne a matsayin babbar gudunmawar dabarun magance matsalar tsaro da ke ƙara ta’azzara a Arewacin Najeriya. Burin taron shi ne ya samar da dandalin tattaunawa, haɗin kai da ɗaukar matakai tare, tsakanin masu ruwa da tsaki wajen dawo da zaman lafiya da ƙarfafa haɗin kan ƙasa.

A wata sanarwa da shugaban ƙungiyar na ƙasa, Alhaji Abdullahi Yelwa (Ajiyan Yauri) ya sanya wa hannu, ya bayyana damuwa matuƙa kan mummunan tasirin da matsalar tsaro ke haifarwa ga rayuka, tattalin arziki da muhimman gine-gine a Arewacin Najeriya, tare da jaddada cewa yawancin matakan baya da aka ɗauka ba su haifar da gamsasshen sakamako mai ɗorawa ba.

Sanarwar ta bayyana cewa taron na bana zai haɗa ‘yan jarida da ‘yan majalisu masu tsara dokoki da jami’an tsaro da sarakunan gargajiya da sauran masu ruwa da tsaki, domin tattaunawa kan samar da ingantattun dabarun sadarwa da za su ƙarfafa amincewar jama’a, yaƙi da tsattsauran ra’ayi, tare da tallafawa don ganin an samar da ingantaccen tsaro a dukkan sassan ƙasa.

“Laluben hanyoyin zaman lafiya a Najeriya dole ya kasance mai ɗorewa, mai faɗi kuma mai tsari,” in ji sanarwar. “Saboda haka taron zai haɗa dukkan masu ruwa da tsaki domin duba dabarun kafofin watsa labarai wajen samar da zaman lafiya da ƙarfafa daidaito a ƙasa.”

A yayin taron, Gwamnan Jihar Kebbi, Dr. Nasir Idris ne zai kasance Mai Masaukin Baƙi, yayin da Gwamnonin jihohin Borno, Babagana Umara Zulum da na Kaduna, Uba Sani da na Katsina, Malam Dikko Umar Raɗɗa da na Neja, Mohammed Umar Bago da kuma na Sakkwato, Ahmed Aliyu za su halarci taron a matsayin Manyan Baƙi Na Musamman. Abin da ke alamta haɗin kai da ɗawainiyar shugabannin Arewa wajen fuskantar ƙalubalen tsaro da tattalin arziki a yankin.

Mai Alfarma Sarkin Musulmi, Alhaji Muhammad Sa’ad Abubakar (III) ne zai jagoranci taron a matsayin Shugaban Taro, yayin da Laftanar-Janar Abdulrahman Bello Dambazau (mai ritaya), tsohon Hafsan Hafsoshin Sojojin Najeriya kuma tsohon Ministan Cikin Gida, shi ne Babban Baƙo Mai Jawabi.

Fiye da wakilai 100 ne daga gidajen rediyo da talabijin na Arewa, tare da masana tsaro, sarakunan gargajiya, malaman addinai, ƙungiyoyin farar hula da jami’an gwamnati, ake sa ran halartar taron.

Tattaunawa a taron za ta maida hankali ne kan batutuwan da suka shafi yadda ake tsara rahotannin da suka shafi al’amuran tsaro, yaɗa bayanan ƙarya, tsattsauran ra’ayi, haɗin gwiwar hukumomin tsaro da ɗabi’un ‘yan jarida a lokutan tashin hankali a ƙasa. “Manufar ita ce, a sake daidaita kafofin watsa labarai a matsayin muhimmiyar hanya ta yaƙi da ta’addanci, zaman doya da manja, da ƙarfafa haɗin kai a tsakanin al’ummar Najeriya,” kamar yadda sanarwar ta jaddada.

Shugaban ƙungiyar ya jaddada cewa kafofin watsa labarai, kasancewarsu hanyoyin sadarwa mafi kusanci ga jama’a, dole ne a inganta su tare da haɗa su cikin tsare-tsaren tsaro na ƙasa. “Babu wata ƙasa da za ta ci nasarar shawo kan matsalar tsaro ba tare da ilimantar da jama’a, haɗa kansu da ƙarfafa su ba,” in ji shi.

A cewar Alhaji Yelwa, wannan taro na bana, zai kasance muhimmin mataki wajen sake tabbatar da rawar da kafofin watsa labarai suke takawa, a matsayin tushen kwanciyar hankali da ginshiƙin zaman lafiya a mulkin dimokuraɗiyya, wanda ke fuskantar barazana saboda yaɗuwar bayanan ƙarya da kuma yadda tsattsauran ra’ayi ke yaɗuwa.

Taron zai kammala ne da fitar da rahoton haɗin gwiwa, wanda zai ƙunshi shawarwari da tsare-tsaren aiki don ƙarfafa alaƙa mai ɗorewa tsakanin kafofin watsa labarai, hukumomin gwamnati da jami’an tsaro a Arewacin Najeriya. Haka kuma shugaban ya yi martani kan yadda ake ƙoƙarin canja labarin yadda matsalar tsaro take a Najeriya. Ya yi gargaɗi cewa a riƙa rarrabewa, a daina alaƙanta batun tsaro da addini ko ƙabila.

“Waɗanda ake kashewa a Najeriya sun haɗa da mutane daga kowane yanki, addini da ƙabila,” in ji shugaban. Ya ci gaba da cewa: “Saboda haka ba daidai ba ne a ce ana kai hari ne ga mabiya wani addini ko ƙabila ɗaya kawai. Kisan da ake yi a wasu sassan ƙasar ba kisan ƙare dangi ba ne, illa kisa ne da ya shafi ta’addanci da tsattsauran ra’ayi, waɗanda dole ne mu haɗu mu ƙyamace su gaba ɗaya.”

Ƙungiyar kuma ta yi gargadi ga duk wani mutum, ƙungiya, ko ƙasar waje da ke ƙoƙarin take ‘yancin Najeriya ko tsoma baki cikin harkokinta na cikin gida, da sunan fafutuka ko kare haƙƙi.

“Ƙungiyarmu ba za ta lamunci duk wani yunƙuri na barazana ga ikon Najeriya ba daga kowane shugaba, ƙungiya ko ƙasar waje. Najeriya ƙasa ce mai cikakken ‘yanci wadda ke iya magance matsalolinta bisa tsarin mulkinta,” in ji sanarwar.

Sanarwar ta ƙarƙare da sake jaddada haɗin gwiwarta da Gwamnatin Jihar Kebbi tare da ƙudurinta na wanzar da zaman lafiya ta hanyar samar da sahihin labarai, bayyana gaskiya, haɗin kai da bin ka’idojin aikin jarida. Shugaban ƙungiyar kuma ya yi kira ga dukkan masu ruwa da tsaki, da su mara wa wannan yunƙuri baya domin dawo da tsaro da aminci a Arewa da Najeriyap baki ɗaya.
_______________

Previous Post

Gwamnatin Jihar Katsina Ta Ƙaddamar Da Babban Aikin Samar Da Ruwa

Next Post

A Rayuwa Babu Abin Da Ya Kai Haƙuri

Related Posts

Ɓatanci Ga Manzon Allah: Musulmi Sun Buƙaci Gwamnati Ta Hukunta Fasto Emmanuel Garba?
Babban Labari

Ɓatanci Ga Manzon Allah: Musulmi Sun Buƙaci Gwamnati Ta Hukunta Fasto Emmanuel Garba?

April 14, 2026
Yadda Za A Magance Matsalolin Tsaro A Najeriya – Sanata Ndume
Babban Labari

Yadda Za A Magance Matsalolin Tsaro A Najeriya – Sanata Ndume

April 8, 2026
Yadda Babban Jigon Jam’iyyar APC Daga Kano Ya Mutu A Otel
Babban Labari

Yadda Babban Jigon Jam’iyyar APC Daga Kano Ya Mutu A Otel

April 2, 2026
Next Post
A Rayuwa Babu Abin Da Ya Kai Haƙuri

A Rayuwa Babu Abin Da Ya Kai Haƙuri

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

RECOMMENDED NEWS

NIJER DA ECOWAS DA NIGERIA: Wani Nazari Na Musamman

NIJER DA ECOWAS DA NIGERIA: Wani Nazari Na Musamman

August 13, 2023
BIU: A Visit to a City on a Plateau (5)

BIU: A Visit to a City on a Plateau (5)

February 9, 2024
VENOM

VENOM

August 6, 2024
ƘUNGIYAR HAUSAWA ZALLA: TA INA ZA A FARA KUMA DA WACE MANUFA? (5)

ƘUNGIYAR HAUSAWA ZALLA: TA INA ZA A FARA KUMA DA WACE MANUFA? (5)

May 24, 2025

FOLLOW US

BROWSE BY CATEGORIES

  • Adabi
  • Addini
  • Babban Labari
  • Barkwanci
  • Dausayin Kauna
  • ENGLISH
  • Gizago
  • Gumbar Dutse
  • Hotuna
  • Labarai
  • Nishadi
  • Noma Da Kiwo
  • Sarauta
  • Shanshani
  • Sharhi
  • Sinadarin Rayuwa
  • Siyasa
  • Ta'aziyya
  • Wasanni

POPULAR NEWS

  • Gwamnan Katsina Ya Ƙi Amsar Kyautar Raguna 100 Daga Hannun Attajiri

    Gwamnan Katsina Ya Ƙi Amsar Kyautar Raguna 100 Daga Hannun Attajiri

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • Ta Tsinci Naira Miliyan 60 A Saudiyya Ta Miƙa Wa Hukuma

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • LUWAƊI DA YARA 14: Yadda Aka Bankaɗo Asirin Kabir Ɗan Hisba

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • Sojojin Najeriya Sun Kama Makashin Sarkin Gobir

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • BINCIKE: Zahirin Abin Da Ke Faruwa A BBC Hausa

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
Taskar Gizago

Follow us on social media:

Recent News

  • Duniya Ba Gidan Zama Ba
  • Minista Dr. Muttaqha Rabe Darma Kana Bi Na Bashi
  • Governor Dikko Radda Commissions Community Development Projects Built by Muntari Sagir in Malumfashi

Category

  • Adabi
  • Addini
  • Babban Labari
  • Barkwanci
  • Dausayin Kauna
  • ENGLISH
  • Gizago
  • Gumbar Dutse
  • Hotuna
  • Labarai
  • Nishadi
  • Noma Da Kiwo
  • Sarauta
  • Shanshani
  • Sharhi
  • Sinadarin Rayuwa
  • Siyasa
  • Ta'aziyya
  • Wasanni

Recent News

Duniya Ba Gidan Zama Ba

Duniya Ba Gidan Zama Ba

April 24, 2026
Minista Dr. Muttaqha Rabe Darma Kana Bi Na Bashi

Minista Dr. Muttaqha Rabe Darma Kana Bi Na Bashi

April 22, 2026
  • About us
  • Advertise
  • Careers
  • Contact

© 2023 Taskar Gizago - Ilimi da Nishadi

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
  • Sharhi
  • Gumbar Dutse
  • Dausayin Kauna
  • Gizago
  • Sarauta
  • Sinadari
  • Adabi da Nishadi
  • Barkwanci
  • Shanshani
  • Hotuna

© 2023 Taskar Gizago - Ilimi da Nishadi

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
This website uses cookies. By continuing to use this website you are giving consent to cookies being used.