• About us
  • Advertise
  • Careers
  • Contact
Saturday, May 30, 2026
  • Login
Taskar Gizago
Advertisement
  • Gida
  • Labarai
  • Sharhi
  • Gumbar Dutse
  • Dausayin Kauna
  • Gizago
  • Sarauta
  • Sinadari
  • Adabi da Nishadi
  • Barkwanci
  • Shanshani
  • Hotuna
Taskar Gizago
No Result
View All Result
Home Labarai

KTSTA: HARKAR SUFURI A HANNUN GWANI (1)

RAHOTON MUSAMMAN

Bashir Yahuza Malumfashi by Bashir Yahuza Malumfashi
July 9, 2025
in Labarai
0
KTSTA: HARKAR SUFURI A HANNUN GWANI (1)

KTSTA: Harkar Sufuri A Hannun Gwani

38
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterWhatsappEmail a Friend

KTSTA: HARKAR SUFURI A HANNUN GWANI (1)

Daga Bashir Yahuza Malumfashi

Related posts

Gobe Gwamna Dikko Raɗɗa Zai Ƙaddamar Da Ayyukan Raya Al’umma Da Muntari Sagir Ya Gina A Malumfashi

Gobe Gwamna Dikko Raɗɗa Zai Ƙaddamar Da Ayyukan Raya Al’umma Da Muntari Sagir Ya Gina A Malumfashi

April 19, 2026
Ɓatanci Ga Manzon Allah: Musulmi Sun Buƙaci Gwamnati Ta Hukunta Fasto Emmanuel Garba?

Fasto Ɗan Ƙungiyar Hausawan Bogi Da Ya Zagi Annabi Ya Ɓoye

April 15, 2026
Harkar Sufuri A Hannun Gwani

 

Sufuri na ɗaya daga cikin al’amura mafiya muhimmanci a rayuwar al’umma. Duk wani al’amari na rayuwar al’umma yana da kaso mafi girma a harkar sufuri – misali, noma da kiwo don abinci, ilimi, kiwon lafiya da sauransu.

La’akari da muhimmancin harkar ta sufuri ne ya sanya gwamnati ta samar da hukuma sukutum domin bunƙasa harkar. Wannan hukuma kuwa ita ce – KTSTA – Katsina State Transport Authority (Hukumar Sufuri ta Jihar Katsina).

Tun da farko, an kafa hukumar ce a shekara ta 1987, lokacin da aka ƙirƙiro Jihar Katsina daga tsohuwar Jihar Kaduna, zamanin mulkin soja na Janar Ibrahim Badamasi Babangida. A ƙarƙashin Gwamnan mulkin soja na farko a jihar, Janar Abdullahi Sarki Mukhtar ne aka kafa Hukumar. Ya yi mulki daga shekarar 1987 zuwa 1988.

Daga Hagu, Janar Ibrahim Badamasi Babangida da kuma Janar Abdullahi Sarki Mukhtar (Masu Ritaya)

Hukumar ta KTSTA ta dakatar da harkokinta a shekarar 1990 bisa wasu dalilai, inda gwamnati a ƙarƙashin Gwamnan mulkin soja, Kanar Yahaya J. Madaki na lokacin ya rufe ta.

A shekarar 1992 ce aka farfaɗo da Hukumar KTSTA, a ƙarƙashin Gwamna Alhaji Sa’idu Barda – Gwamnan Jihar Katsina na farko a mulkin farar hula. Kamar yadda tarihi ya tabbatar, farfaɗo da hukumar ya samo asali ne bisa shawarar Gwamna Aminu Bello Masari, wanda a lokacin shi ne Kwamishinan Ma’aikatar Ayyuka, Gidaje da Sufuri.

Tsofaffin Gwamnonin Jihar Katsina: Alhaji Sa’idu Barda da kuma Kanar Yahaya John Madaki (Mai Ritaya)

Tun daga lokacin, hukumar ta ci gaba da gudanar da harkokinta. An samu ƙalubale da matsaloli masu tarin yawa a harkokin hukumar. A haka har aka zo kan Gwamnatin Alhaji Aminu Bello Masari. Shi ne ya miƙa mulkin gudanarwar KTSTA ga hannun Malam Haruna Musa Rugoji, a watan Nuwamba na shekarar 2018.

Tsohon Gwamnan Jihar Katsina, Alhaji Aminu Bello Masari, tare da Shugaban Hukumar KTSTA, Malam Haruna Musa Rugoji, yayin duba wasu sababbin motocin da hukumar ta sayo a can baya

Ya zuwa wannan lokaci da muke haɗa wannan rahoto, Malam Rugoji ne ke shugabancin wannan hukuma – mutumin da ya kasance ƙwararre kuma masanin harkokin sufuri.

Gwamnan Jihar Katsina, Malam Dikko Umar Raɗɗa, tare da Malam Haruna Musa Rugoji, yayin duba wata daga sababbin motocin da hukumar ta sayo, a kwanakin baya

Shin wane ne Malam Haruna Musa Rugoji? Ku biyo mu a rahoto na gaba, in sha Allah.
__________

Previous Post

A Review of “Leadership in the Nigerian Civil Service…”

Next Post

ƘUNGIYAR HAUSAWA ZALLA: TA INA ZA A FARA KUMA DA WACE MANUFA? (8)

Related Posts

Gobe Gwamna Dikko Raɗɗa Zai Ƙaddamar Da Ayyukan Raya Al’umma Da Muntari Sagir Ya Gina A Malumfashi
Labarai

Gobe Gwamna Dikko Raɗɗa Zai Ƙaddamar Da Ayyukan Raya Al’umma Da Muntari Sagir Ya Gina A Malumfashi

April 19, 2026
Ɓatanci Ga Manzon Allah: Musulmi Sun Buƙaci Gwamnati Ta Hukunta Fasto Emmanuel Garba?
Labarai

Fasto Ɗan Ƙungiyar Hausawan Bogi Da Ya Zagi Annabi Ya Ɓoye

April 15, 2026
Sheikh Mutawakkil Mustapha Ya Zama Alƙalin Kotun Shari’a ta Ɗaukaka Ƙara ta Jihar Katsina
Labarai

Sheikh Mutawakkil Mustapha Ya Zama Alƙalin Kotun Shari’a ta Ɗaukaka Ƙara ta Jihar Katsina

February 13, 2026
Next Post
ƘUNGIYAR HAUSAWA ZALLA: TA INA ZA A FARA KUMA DA WACE MANUFA? (8)

ƘUNGIYAR HAUSAWA ZALLA: TA INA ZA A FARA KUMA DA WACE MANUFA? (8)

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

RECOMMENDED NEWS

Malam Nasir El-Rufa’i: Guga Sha Kwaramniya

Malam Nasir El-Rufa’i: Guga Sha Kwaramniya

June 10, 2023
Yunkurin ‘Yan Ba-Zata/Hausawa Bogi Na Haddasa Ruɗani A Arewa (4)

Yunkurin ‘Yan Ba-Zata/Hausawa Bogi Na Haddasa Ruɗani A Arewa (4)

January 2, 2026
NAJERIYA A 65: MU SAKE DUBAWA

NAJERIYA A 65: MU SAKE DUBAWA

October 1, 2025
Hukunta Ɗan T+adda Victor Solomon: Madalla Da Gwamnatin Jihar Kaduna

Hukunta Ɗan T+adda Victor Solomon: Madalla Da Gwamnatin Jihar Kaduna

January 14, 2026

FOLLOW US

BROWSE BY CATEGORIES

  • Adabi
  • Addini
  • Babban Labari
  • Barkwanci
  • Dausayin Kauna
  • ENGLISH
  • Gizago
  • Gumbar Dutse
  • Hotuna
  • Labarai
  • Nishadi
  • Noma Da Kiwo
  • Sarauta
  • Shanshani
  • Sharhi
  • Sinadarin Rayuwa
  • Siyasa
  • Ta'aziyya
  • Wasanni

POPULAR NEWS

  • Gwamnan Katsina Ya Ƙi Amsar Kyautar Raguna 100 Daga Hannun Attajiri

    Gwamnan Katsina Ya Ƙi Amsar Kyautar Raguna 100 Daga Hannun Attajiri

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • Ta Tsinci Naira Miliyan 60 A Saudiyya Ta Miƙa Wa Hukuma

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • LUWAƊI DA YARA 14: Yadda Aka Bankaɗo Asirin Kabir Ɗan Hisba

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • Sojojin Najeriya Sun Kama Makashin Sarkin Gobir

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • BINCIKE: Zahirin Abin Da Ke Faruwa A BBC Hausa

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
Taskar Gizago

Follow us on social media:

Recent News

  • POSITIVE COMRADE
  • BUKAR USMAN: The Human Library
  • Sule Lamido’s Theme of Authenticity

Category

  • Adabi
  • Addini
  • Babban Labari
  • Barkwanci
  • Dausayin Kauna
  • ENGLISH
  • Gizago
  • Gumbar Dutse
  • Hotuna
  • Labarai
  • Nishadi
  • Noma Da Kiwo
  • Sarauta
  • Shanshani
  • Sharhi
  • Sinadarin Rayuwa
  • Siyasa
  • Ta'aziyya
  • Wasanni

Recent News

POSITIVE COMRADE

POSITIVE COMRADE

May 20, 2026
BUKAR USMAN: The Human Library

BUKAR USMAN: The Human Library

May 19, 2026
  • About us
  • Advertise
  • Careers
  • Contact

© 2023 Taskar Gizago - Ilimi da Nishadi

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
  • Sharhi
  • Gumbar Dutse
  • Dausayin Kauna
  • Gizago
  • Sarauta
  • Sinadari
  • Adabi da Nishadi
  • Barkwanci
  • Shanshani
  • Hotuna

© 2023 Taskar Gizago - Ilimi da Nishadi

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
This website uses cookies. By continuing to use this website you are giving consent to cookies being used.