• About us
  • Advertise
  • Careers
  • Contact
Sunday, April 26, 2026
  • Login
Taskar Gizago
Advertisement
  • Gida
  • Labarai
  • Sharhi
  • Gumbar Dutse
  • Dausayin Kauna
  • Gizago
  • Sarauta
  • Sinadari
  • Adabi da Nishadi
  • Barkwanci
  • Shanshani
  • Hotuna
Taskar Gizago
No Result
View All Result
Home Nishadi

MANYAN MATA: Fim Ɗin Da Ya Nazarto Matsalolin Rayuwar Malam Bahaushe

SHARHIN FIM

Bashir Yahuza Malumfashi by Bashir Yahuza Malumfashi
June 24, 2024
in Nishadi
0
MANYAN MATA: Fim Ɗin Da Ya Nazarto Matsalolin Rayuwar Malam Bahaushe

Fostar fim ɗin Manyan Mata

84
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterWhatsappEmail a Friend

MANYAN MATA:
Fim Ɗin Da Ya Nazarto Matsalolin Rayuwar Malam Bahaushe

Daga Bashir Yahuza Malumfashi

Related posts

TSAKANIN ALI JITA DA SOJABOY: WANE NE YA FI GASKIYA?

TSAKANIN ALI JITA DA SOJABOY: WANE NE YA FI GASKIYA?

February 15, 2026
Rasuwar ‘Yar Kannywood Jidda Fulani: Ko Furodusa Aminu Saira Ya Kyauta?

Rasuwar ‘Yar Kannywood Jidda Fulani: Ko Furodusa Aminu Saira Ya Kyauta?

December 27, 2025

(08065576011)

Fostar fim ɗin Manyan Mata

Sunan Fim: Manyan Mata.
Furodusa: Abdul Muhammad Amart.
Darakta: Sadiq N. Mafia.
Tsara Labari: Yakubu M. Kumo.
Kamfanin Shiryawa: ABNUR Entertainment, Kano.
Shekarar Shiryawa: 2023/2024.
‘Yan Wasa: Sadiq Sani Sadiq, Ali Nuhu, Hadiza Aliyu Gabon, Hafsat Idris, Jamila Nagudu, A’isha Humaira, Adam A. Zango, Rabi’at Sulaiman, Ali Ibrahim Dawayya, Maryam Yahaya, Halima Atete, Falalu Ɗorayi, Saratu Giɗaɗo, Abubakar Waziri Bado, Ladidi Fagge, Hadiza Muhammad, Balarabe Jaji, Rabi’u Rikadawa, A’isha Najamu, Tahir I. Tahir, Mommy Gombe, Tijjani Faraga, Mustapha Naburaska, Yusuf Sassen, Isa Adam Fati Washa da sauransu.

√ Gabatarwa:
A yayin da ake ta jira da dakon kashi na uku na fim ɗin Manyan Mata (mai dogon zango), bayan da tuni aka kammala nuna kashi na ɗaya da na biyu a gidajen talabijin da kuma tashar YouTube, bari a yau mu yi tariya da nazarin wasu manya da ƙananan darussa da za muka yi tsinkaye da su a fim ɗin. Za mu tattauna waɗannan darussa ne, kasancewar fim ɗin ya ɗauki hankali, kamar kuma yadda ya ƙayatar, ya faɗakar kuma ya nishaɗantar.

Fim ɗin Manyan Mata, bunƙasasshen shiri ne da ya binciko, ya tattara kuma ya bayyana manya da ƙasurguman matsalolin da suka daɗe suna addabar al’ummar Arewacin Najeriya a hannu ɗaya, musamman ma Hausa-Fulani da kuma ita kanta Najeriyar gaba ɗaya, a ɗaya hannun.

√ Wulaƙanta Da Danne Haƙƙin Mata:
Wani babban darasi da fim ɗin Manyan Mata ke nusarwa, shi ne illolin da ke tattare da wulaƙanta mata. Fim ɗin ya haska yadda mata a ƙasar Hausa suke fuskantar danniya da wulaƙanci da tozarci, musamman a gidajen aure. Hakan ya nuna yadda wasu magidanta suke doɗe kunnuwansu daga koyarwar Manzon Allah, Muhammadu (saw), wanda ya ce a kula da su sosai, a kyautata wa rayuwarsu cikin tausayi da tarairaya.

Dubi dai yadda Sadiq Sani Sadiq (Garba) ya riƙa tozarta da cin zarafin matarsa, Hafsat Idris (Na’ima), duk da cewa tana yi masa biyayya da kare martabarsa a gidanta na aure. Darasin illar haka ya fito sarai, bayan da ya sake ta, ya auro wata fitinanna, A’isha Najamu (Nafisa), wacce ta riƙa gasa masa aya a tafin hannu; har ma ta kusa halaka shi, a yayin da ta soka masa wuƙa a ruwan cikinsa.

Irin wannan halayya ta tozarta da wulaƙanta mata, ta bayyana a gidan Malam Kabiru, wanda ya yi ƙaurin suna wajen auri-saki, mai danne haƙƙin mata da na ‘ya’yansa. Babu abin da ya sani sai tara mata da haihuwar ‘ya’ya barkatai. Babu tarbiyya, babu abinci mai kyau, babu suturar kirki, babu muhalli nagari. Dalili ke nan ‘ya’yansa kamar Audu Tijara (Ali Ibrahim Dawayya) da Binta (Fatima S.U. suka lalace. A yayin da Audu ya zama ɗan ƙwaya kuma ɗan daba, ita kuwa Binta ta zama gagararrar budurwa, wacce ta raina iyayenta kuma take bin ‘yan daba. Haka kuma wannan halayya ta wulaƙanta iyali, ta jefa rayuwar ɗansa Nafi’u cikin garari. Yaron da bai wuce shekara biyar ba amma mahaifinsa ya tura shi makarantar allo da sunan almajiranci a wani gari mai nisa. A can ya fuskanci rayuwar wahala, ba uwa ba uba, ba abinci, sai dai ya yi bara, ba sutura, ba wurin kwana na kirki. A haka ya gamu da zaluncin wani malaminsa, Bawa (Mustapha Naburaska), wanda ya kusa halaka shi da bulala.

√ Muhimmancin Ilimi Ga Al’umma:
A fim ɗin, an nuna muhimmancin ilimi. Mu duba yadda rayuwar Laila Tahir (Hadiza Aliyu Gabon) da ƙawarta Nadiya (A’isha Aliyu Tsamiya/Rabi’at Sulaiman) ta kasance cikin tsari, musamman saboda suna da ilimin zamani da na addini. Haka kuma mu kalli rayuwar Jibrin (Ali Nuhu), Kamal (Isa Adam), Malam Muhsin (Falalu Ɗorayi), Zaid (Yusuf Sassen), waɗanda su ma suka kasance cikin tsarin rayuwa mai kyau, albarkacin ilimi.

√ Illar Jahilci:
A gefe ɗaya kuma an nuna illar da ke tattare da jahilci da jahilai. Mu duba yadda Karima (Jamila Nagudu) da Turai (Saratu Giɗaɗo) da Rabi (Ladidi Fagge) da mijinsu Malam Kabiru suke rayuwar jahilci da ƙasƙanci saboda rashin ilimi. Mu kalli kuma yadda jahilci ya taka rawa a rayuwar Lantana (Balaraba Abdullahi), yadda ta riƙa tunzura da tozarta mijinta Malam Adamu (Balarabe Jaji). Mun kuma ga yadda saboda tsabar jahilci, ta kasance muguwa, mai uzura wa ɗiyar kishiyarta, Sadiya (Fati Washa). Dubi dai yadda ta hana ta zuwa makaranta, har ma ta ƙona mata littattafai. Dubi yadda ta shirya mata auren dole da nufin mugunta.

Yana daga illar jahilci, yadda rayuwar Rabi’u Rikadawa ta kasance. Mun ga yadda ya uzura wa ‘yarsa Na’ima (Hafsat Idris), duk da cewa tana fuskantar tsangwama da tozarci a gidan miji. Dubi dai yadda ya kore ta daga gidansa, bayan mijinta ya yi mata sakin wulaƙanci. Allah ne ya kiyaye ta amma da ta shiga harkar karuwanci.

√ Muhimmancin Ƙungiyoyin Sa-Kai Cikin Al’umma:
Wani babban darasi da fim ɗin Manyan Mata ya haska wa al’umma, shi ne muhimmancin kafa ƙungiyoyin sa-kai a cikin al’umma. Mu duba dai yadda ƙungiyar Manyan Mata ta jajirce wajen ƙwato haƙƙin mata da taimaka wa marasa galihu. Ga yadda ta riƙa faɗakarwa da ilimantarwa da wayar da kan al’umma game da rayuwa. Mun ga yadda Laila Tahir da Nadiya suka tsaya kai da fata wajen yaƙi da azzalumai, masu ɓata ‘yan mata. Mun ga yadda ƙungiyar ta riƙa fafutuka wajen yaƙi da tu’ammali da safarar muggan ƙwayoyi, inda a sanadiyar faɗakarwar da suke yi, suka yi nasarar ceto rayuwar manyan ‘yan ƙwaya da ‘yan daba, kamar Audu Tijara da abokansa.

√ Illar Tura ‘Yan Mata Tallace-Tallace A Titi:
Yana daga cikin illolin da suka kassara al’ummar Arewa, yadda ake ɗora wa yara, musamman mata tallace-tallace, maimakon tura su makaranta domin neman ilimi na zamani da na addini, yadda ta haka za su samu ingantattar tarbiyya da kyakkyawar rayuwa. Mun kalli yadda rayuwar yara mata ke kasancewa a titi, yadda ake fasikanci da su domin neman kuɗi. Mun ga yadda a sanadiyar yawon talla, Bilkisu (Maryam Yahaya) ta shiga haɗari, inda Alhaji Tahir (Tijjani Faraga) ya yi mata fyaɗe, bayan da kawali, Ɗanliti (Tahir I. Tahir) ya yaudare ta.

√ Illar Tura Ƙananan Yara Zuwa Birane Domin Almajiranci:
Fim ɗin Manyan Mata ya yi tsokaci, jan kunne gami da faɗakarwa ga al’ummar Arewa, musamman Hausa-Fulani, domin su hankalta, su duba yadda zamani ya canja, su kawo sauyin da zai amfane su da sauran al’umma. Fim ɗin ya haska mana illolin da ke tattare da tura ƙananan yara zuwa manyan birane da sunan karatun allo (Almajiranci). Fim ɗin ya tunatar tare da jaddada cewa, haƙƙi ne na iyaye su kula da rayuwar ‘ya’yansu, ta hanyar ciyar da su, tufatar da su da ba su ilimi da kyakkyawar tarbiyya. Bisa ga haka, tsarin da wasu iyaye suke bi wajen tura yara birane domin karatun allo, babu abin da yake haifarwa sai lalacewar yaran da jefa su cikin ƙasƙancin barace-barace. Ta haka kuma suke haɗuwa da muggan mutane da suke lalata masu rayuwa.

Mun ga misali daga Audu Tijara, wanda ya lalace, ya zama ɗan daba, mashayin muggan ƙwayoyi, sakamakon tura shi da aka yi zuwa birni da sunan almajiranci.
Haka kuma, mun ga yadda aka tura ƙanensa Tasi’u zuwa karatun allo a birni, duk kuwa da cewa bai wuce shekara biyar ba da haihuwa. Hakan ta sanya ya faɗa hannun mugun gardi, Bawa (Mustapha Naburaska), wanda ya kusa kashe shi da duka saboda zalunci.

√ Illar Rashin Tsoron Allah:
Duk da cewa mafi yawan al’ummar Arewacin Najeriya mabiya addinan Musulunci ne da Kiristanci amma mutane na fama da halayen rashin tsoron Allah. Alhali dukkan addinan biyu suna kira tare da koyar da mabiya da su kasance masu tsoron Allah a dukkan lamurransu na rayuwa. Fim ɗin ya hasko yanayin da wasu mutane suke ciki, na rashin tsoron Allah, inda suka tsunduma cikin ayyukan mugunta da ƙuntata wa al’umma, domin biyan karkatattun buƙatun kansu na rayuwa.

Mun ga yadda wasu karkatattun mutane suke zaluntar mutane a sansanin ‘yan gudun hijira. Mun kalli yadda Oga Bala (Tijjani Asase) da yaransa suka uzura wa Samira (Maimuna Abubakar wato Mommy Gombe), inda saboda ta ƙi amincewa ya yi lalata da ita, ya hana ta abinci da magani – dalilin da ya sanya ƙanenta ya mutu cikin jinya. Haka kuma mun ga yadda a sakamakon ƙuncin da ta riƙa fuskanta, ya sanya ita da ƙawarta suka gudu daga sansanin, suka faɗa hannun masu safarar mata da yara; al’amarin da ya ƙara ta’azzara masu ƙuncin rayuwa. Fim ɗin ya hasko wannan a matsayin koke da tunasarwa ga jami’an tsaro da al’umma, domin su mai da hankali zuwa bankaɗo asirin irin waɗannan muggan mutane, domin magance matsalar.

Wani baƙin hali na rashin tsoron Allah da ya gallabi mutane a Najeriya, shi ne yadda wasu suka ɓoye a ƙarƙashin ƙasa, suna gudanar da aika-aikar safarar mata da ƙananan yara. Mun ga yadda Ladidi Tubeless ta haɗa kai da wasu karkatattu, suke gudanar da wannan baƙar harka, inda suke yin garkuwa da mata bisa zamba da yaudara, su tilasta su ga yin zina har su ɗauki ciki; bayan sun haihu kuma su sayar da jariran ga wasu mutane na daban. Mun ga abin da ya faru ga Mommy Gombe da sauran matan da suka killace. Wannan ma wani tsokaci ne da nufin jan hankali ga jami’an tsaro, domin su mai da hankali a wannan sashi, domin daƙile masu gudanar da wannan mummunar harka.

Yana daga rashin tsoron Allah, yadda wasu suke tu’ammali da bokaye da matsafa, domin neman abin duniya ido rufe. Mun kalli yadda Alhaji Tahir (Tijjani Faraga) da abokansa suke lalata ‘yan mata, domin buƙatar tsafi. Mun ga yadda shi Tahir ɗin ya yi wa Bilkisu (Maryam Yahaya) fyade, inda saboda takaici har mahaifinta ya mutu.

√ Tona Asirin Wasu Gurɓatattun ‘Yan Siyasa:
Fim ɗin ya tona asiri ta hanyar hasko rayuwar wasu gurɓatattun ‘yan siyasa, waɗanda suka ƙware wajen kafa tuggu, nuna rashin gaskiya da ta’addanci. Mun kalli yadda Sanata Idris Sango (Bashir Nayaya) yake amfani da wasu karkatattun ‘yan sanda wajen cin ma karkataccen burinsa. Dubi dai yadda ya ba Difi’o rashawa da hanci, domin a kashe maganar mummunan laifin da matarsa Hajiya Rayya (Halima Atete) ta aikata, lokacin da ta ƙona ‘yar aikinta, Falmata da tafasasshen ruwa. Dubi kuma yadda yake amfani da ‘yan daba, irin su Audu Tijara (Ali Ibrahim Dawayya) da Walƙiya (Adamu Muhammad Bala) wajen ta’addanci, bayan ya raba masu kuɗi da ƙwaya. Mun ga yadda suka farfasa ofishin ƙungiyar Manyan Mata da kuma yadda suka yi wa wani matashi ɗan shoshalmidiya barazana saboda yana rubutun silili ga Sanatan.

√ Illolin Harkar Karuwanci:
Karuwanci mummunar harka ce, wacce take gurɓata al’umma. Fim ɗin Manyan Mata ya hasko wasu daga illolin karuwanci. Mun kalli yadda rayuwar karuwai take kasancewa cikin ƙasƙanci da tozarci, kamar dai yadda aka nuno abin da ke faruwa a gidan Magajiyar karuwai. Wani darasi da aka nuna, shi ne wasu daga cikin dalilan da suke jefa yaran mata cikin harkar karuwanci.

Waɗannan kuwa sun haɗa da auren dole da kuma yadda wasu iyaye ke ƙuntata wa rayuwar ‘ya’yansu mata ta hanyar kyara da tsangwama. Dubi dai yadda Lubabatu (Fati Garba Shu’uma) ta gudo daga gidansu, ta shiga karuwanci saboda auren dole. Mu duba kuma yadda Na’ima ita ma ta shiga bariki saboda mahaifinta, Rabi’u Rikadawa ya tsangwame ta, ta kai ga har ya kore ta daga gidansa, bayan da mijinta, Garba (Sadiq Sani Sadiq) ya sake ta.

√ Muhimmancin Soyayyar Gaskiya A Tsakanin Ma’aurata:
Wani babban darasi kuma da za a iya fahimta daga fim ɗin, shi ne yadda soyayyar gaskiya take taka muhimmiyar rawa wajen kyautata zaman aure.

Magidanta maza da mata za su yi koyi da rayuwar Malam Muhsin (Falalu Ɗorayi), cewa duk magidancin da ke son samun ladar aure, yake son samun farin ciki da ƙauna daga matarsa, to ya yi koyi da rayuwar auren Manzon Allah (saw). Magidanci ya ɗauki matarsa tamkar abokiyar rayuwa, ba baiwa ba. Ya riƙa kyautata mata, ya nuna mata jin ƙai da tausayi. Ya kasance mai sakin fuska da walwala da nishaɗi da matarsa ko matansa. Ya kasance mai taya su aiki cikin gida. Ke nan miji ba zai zama mugu, maƙetaci ba, kamar yadda Garba ya kasance tsakaninsa da matarsa Na’ima.

Ta fannin matan aure kuwa, akwai abin koyi daga Laila Tahir (Hadiza Aliyu Gabon), cewa akwai fa’ida mace ta kiyaye duk abin da zai kawo matsala tsakaninta da mijinta. Mace ta kasance mai yi wa mijinta uzuri da kawar da kai daga kuskuren da ya aikata. Mun kalli yadda Laila ta kawar da kai daga kuskuren mijinta Kamal (Isa Adam). A lokacin da ta ga shaidar janbaki a rigarsa, duk da ta fahimci cewa wata ce ta yi masa kiss amma sai ta nuna cewa ita ba ta gani ba.

Akwai kuma abin koyi ga magidanta, a rayuwar auren Iliya (Adam A. Zango) da Safiya. An fahimci cewa farin cikin magidanta yana tattare da ƙauna da fahimta, ba wai a tarin dukiya ba. Dubi dai yadda Zango yake ɗawainiya da matarsa, duk da cewa shi ba attajiri ba ne, sana’ar ga-ruwa yake yi.

√ Illolin Shaye-Shayen Kayan Maye:
Akwai kuma darussan da fim ɗin yake nunawa da suka danganci illolin da ke tattare da shaye-shayen kayan maye.

Dubi dai yadda rayuwar matasa irin su Audu Tijara da Walƙiya take gudana, inda a sakamakon shaye-shayen kayan maye suka zama ‘yan daba, karnukan ‘yan siyasa kuma suka zama ɓarayi. Akwai gargaɗi na musamman ga mata, cewa su yi hattara da muggan ƙawaye irin su Jummai, waɗanda suke koya wa matan aure shaye-shayen kayan maye. Dubi dai yadda Na’ima ta shiga matsala, bayan ƙawarta Jummai ta koya mata shan kayan maye.

√ Samar Da Nishaɗi:
Akwai nishaɗantarwa sosai a fim ɗin Manyan Mata, musamman kasancewar mafi yawan ‘yan wasan ƙwararru ne. A mafi yawan abubuwan da suka faru a gidan Malam Kabiru (Abubakar Waziri Bado), akwai barkwanci da nishaɗantarwa daga shi mai gidan da iyalansa, su Turai (Saratu Giɗaɗo) da Rabi (Ladidi Fagge) da Karima (Jamila Nagudu) da ɗansu, Audu Tijara. Akwai nishaɗantarwa a abin da ya faru a makarantar tsangaya, yadda Bawa (Mustapha Naburaska) ya gudanar da al’amuransa. Haka shi ma ta ɓangaren Rabi’u Rikadawa, mafi yawan maganganunsa da yanayin matakan da yake ɗauka a kan iyalansa, akwai barkwanci da saka nishaɗi. Haka shi ma Garba (Sadiq Sani Sadiq), ya nishaɗantar sosai a yanayin zamantakewar sa da matarsa Na’ima. Haka ma a zaman shi da amaryarsa, A’isha Najamu, yadda ya riƙa fuskantar matsaloli da ƙalubale daga wajenta. Dubi dai yadda a duk lokacin da ta cusa masa takaici, sai ka ji ya ce: “Well, it is allowed!”

Kiɗan taushi da waƙar da aka saka a fim ɗin, sun ƙayatar, inda bayan nishaɗantarwa kuma waƙar tana faɗakarwa tare da bayyana jigon fim ɗin – kawo gyara ga al’umma ta hanyar yaƙi da munanan ɗabi’u, kamar shaye-shaye, tallace-tallace ga yara mata da kuma tura yara almajiranci da sauransu.

√ Wasu Ƙalubale:
Wasu ƙalubale a fim ɗin su ne, akwai wasu munanan ɗabi’u da a yanzu suke addabar al’umma, waɗanda ya kamata a ce an hasko su a fim ɗin domin gargaɗi da faɗakarwa. Misali, kamar luwaɗi da maɗigo. Haka kuma ya kamata a ce an yi waiwayen baya (flashback), a hasko yadda Lantana da kishiyarta (maman Sadiya) suka yi zama a gidan Malam Adamu (Balarabe Jaji), maimakon a ce labari kawai Lantana take bayarwa, cewa kishiyar tata ta gana mata azaba.

Haka ma ta ɓangaren bokaye, ya kamata a ce an hasko yadda suke gudanar da sha’aninsu a aikace, ba kamar yadda Alhaji Tahir da abokansa suke ta faɗa da baki kawai ba, cewa bokayensu ne suka umurce su da su riƙa yin fasikanci da ‘yan mata.

Haka kuma duk da cewa akwai sauran kashi na gaba amma ya dace a ce an nuno sakamakon aikin da duk wani mutum ya aikata na rashin daidai. Muggan ‘yan siyasa irin su Bashir Nayaya da manyan ‘yan daba irin su Walƙiya da muggan masu safarar mata da yara, irin su Ladidi Tubeless da muggan masu zalunci a sansanin’yan gudun hijira, kamar Tijjani Asase da masu munafuntar matansu, irin su Zaid (Yusuf Sassen); ya kamata a nuna sakamakon da suka girba, domin al’umma su ɗauki izina daga abin da ya same su. Ma’ana, ko a can gaba ne a iya yin haka amma kada a bari fim ɗin ya ƙare nan gaba koda a kashi na ƙarshe ne, ba tare da an hukunta mugaye ba.

√ Jaruman Da Suka Rasu:
Akwai wasu manyan ‘yan wasa da suka rasu, waɗanda kuma suke taka muhimmiyar rawa a fim ɗin nan na Manyan Mata. Misali, akwai ɗaya daga cikin matan Malam Kabiru (Abubakar Waziri Bado), mahaifiyar Audu Tijara, watau Turai (Saratu Giɗaɗo). Haka shi ma mijin Bilkisu (Maryam Yahaya), Malam Hashim (Aminu S. Bono).

Dukkan waɗannan ‘yan wasa biyu sun rasu, Allah Ya ji ƙan su da rahama. Shin yaya za a maye gurabensu, ko kuwa za a canja labarin ne, a fitar da batunsu? Haka ita ma Hajiya Rayya (Halima Atete) matar Sanata Idris Sango (Bashir Nayaya), duk da cewa ita ba mutuwa ta yi ba amma ta yi aure. Shin yaya za a yi da gurbinta?

√ Me Zai Wakana A Kashi Na Uku?
A yayin da ake jiran Manyan Mata kashi na uku, ‘yan kallo sun zaƙu domin samun amsar tambayar ko me zai faru a gaba? Misali, me zai biyo bayan tonon sililin da ake yi wa Alhaji Tahir (Tijjani Faraga)?

Yadda ya yanke jiki ya faɗi, shin ya mutu ke nan ko kuwa suma ya yi, zai farfaɗo? Me kuma zai faru ga ‘yarsa, Laila Tahir (Hadiza Aliyu Gabon), wacce ita ma ta yanke jiki ta faɗi? Shin ita ma tana mutuwa ne ko kuwa za ta farfaɗo?

Mu zuba ido ga isowar Manyan Mata kashi na uku…!
____________________
Bashir Yahuza Malumfashi (08065576011), marubuci, sha’iri, shi ne Mawallafi kuma Babban Editan Mujallar Taskar Gizago (online).

 

 

 

Previous Post

Abba Gida-Gida: Why Kano State is Too Big For His Shoes

Next Post

YAU 40: ALLAH YA JI ƘAN HAJIYA ZAINAB AHMAD

Related Posts

TSAKANIN ALI JITA DA SOJABOY: WANE NE YA FI GASKIYA?
Nishadi

TSAKANIN ALI JITA DA SOJABOY: WANE NE YA FI GASKIYA?

February 15, 2026
Rasuwar ‘Yar Kannywood Jidda Fulani: Ko Furodusa Aminu Saira Ya Kyauta?
Nishadi

Rasuwar ‘Yar Kannywood Jidda Fulani: Ko Furodusa Aminu Saira Ya Kyauta?

December 27, 2025
Burna Boy: Fitaccen Mawaƙin Da Ya Rabauta Da Ni’imar Musulunci
Nishadi

Burna Boy: Fitaccen Mawaƙin Da Ya Rabauta Da Ni’imar Musulunci

November 5, 2025
Next Post
YAU 40: ALLAH YA JI ƘAN HAJIYA ZAINAB AHMAD

YAU 40: ALLAH YA JI ƘAN HAJIYA ZAINAB AHMAD

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

RECOMMENDED NEWS

KIRA NA MUSAMMAN GA JAMI’AN TSARO A MALUMFASHI

KIRA NA MUSAMMAN GA JAMI’AN TSARO A MALUMFASHI

August 3, 2024
Musulmin Kudancin Najeriya Sun Jaddada Mubaya’a Ga Sarkin Musulmi

Musulmin Kudancin Najeriya Sun Jaddada Mubaya’a Ga Sarkin Musulmi

February 13, 2026
Malam Nasir El-Rufa’i: Guga Sha Kwaramniya

Malam Nasir El-Rufa’i: Guga Sha Kwaramniya

June 10, 2023
AN DAKATAR DA MALAMIN MUSULUNCI DAGA YIN WA’AZI

AN DAKATAR DA MALAMIN MUSULUNCI DAGA YIN WA’AZI

November 19, 2024

FOLLOW US

BROWSE BY CATEGORIES

  • Adabi
  • Addini
  • Babban Labari
  • Barkwanci
  • Dausayin Kauna
  • ENGLISH
  • Gizago
  • Gumbar Dutse
  • Hotuna
  • Labarai
  • Nishadi
  • Noma Da Kiwo
  • Sarauta
  • Shanshani
  • Sharhi
  • Sinadarin Rayuwa
  • Siyasa
  • Ta'aziyya
  • Wasanni

POPULAR NEWS

  • Gwamnan Katsina Ya Ƙi Amsar Kyautar Raguna 100 Daga Hannun Attajiri

    Gwamnan Katsina Ya Ƙi Amsar Kyautar Raguna 100 Daga Hannun Attajiri

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • Ta Tsinci Naira Miliyan 60 A Saudiyya Ta Miƙa Wa Hukuma

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • LUWAƊI DA YARA 14: Yadda Aka Bankaɗo Asirin Kabir Ɗan Hisba

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • Sojojin Najeriya Sun Kama Makashin Sarkin Gobir

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • BINCIKE: Zahirin Abin Da Ke Faruwa A BBC Hausa

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
Taskar Gizago

Follow us on social media:

Recent News

  • Duniya Ba Gidan Zama Ba
  • Minista Dr. Muttaqha Rabe Darma Kana Bi Na Bashi
  • Governor Dikko Radda Commissions Community Development Projects Built by Muntari Sagir in Malumfashi

Category

  • Adabi
  • Addini
  • Babban Labari
  • Barkwanci
  • Dausayin Kauna
  • ENGLISH
  • Gizago
  • Gumbar Dutse
  • Hotuna
  • Labarai
  • Nishadi
  • Noma Da Kiwo
  • Sarauta
  • Shanshani
  • Sharhi
  • Sinadarin Rayuwa
  • Siyasa
  • Ta'aziyya
  • Wasanni

Recent News

Duniya Ba Gidan Zama Ba

Duniya Ba Gidan Zama Ba

April 24, 2026
Minista Dr. Muttaqha Rabe Darma Kana Bi Na Bashi

Minista Dr. Muttaqha Rabe Darma Kana Bi Na Bashi

April 22, 2026
  • About us
  • Advertise
  • Careers
  • Contact

© 2023 Taskar Gizago - Ilimi da Nishadi

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
  • Sharhi
  • Gumbar Dutse
  • Dausayin Kauna
  • Gizago
  • Sarauta
  • Sinadari
  • Adabi da Nishadi
  • Barkwanci
  • Shanshani
  • Hotuna

© 2023 Taskar Gizago - Ilimi da Nishadi

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
This website uses cookies. By continuing to use this website you are giving consent to cookies being used.