GODIYA
~~~~~~~
Ya Rabbi Sarki abin godiya,
Kare mu kullum mu zam lafiya.
Ƙaro daraja, tsarki da alheriya,
Ga Ɗaha Manzo mijin Mariya.
Ka ba mu komai cikin duniya,
Sanya mu zam masu kyan zuciya.
Haka ma a rana ta hisabiya,
Sanya mu Aljanna mai dausiya.
Tsanani da ƙunci da annakiya,
Wanke su kullum mu zam dariya.
Shaiɗan maƙiyinmu kullum niya,
Kare mu tarkonsa sharholiya.
Sanya mu zamo da annuriya,
Bautar Ka kullum cikin juriya.
~~~
© Bashir Yahuza Malumfashi
Lahadi, 22-08-1445 (Hijriyya)
03-03-2024 (Miladiyya).
~~~














