• About us
  • Advertise
  • Careers
  • Contact
Friday, April 17, 2026
  • Login
Taskar Gizago
Advertisement
  • Gida
  • Labarai
  • Sharhi
  • Gumbar Dutse
  • Dausayin Kauna
  • Gizago
  • Sarauta
  • Sinadari
  • Adabi da Nishadi
  • Barkwanci
  • Shanshani
  • Hotuna
Taskar Gizago
No Result
View All Result
Home Labarai

BADAƘALAR NAIRA MILIYAN 585: Gwamnati Ta Fara Binciken Ministar Agaji – Idris

Daga Wakilinmu by Daga Wakilinmu
January 8, 2024
in Labarai
0
Kasafin 2024 Ya Fitfita Jaddada Ajandar Sassaita Nijeriya – Idris

Ministan Yaɗa Labarai, Alhaji Mohammed Idris, yana gabatar da jawabi a taron

8
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterWhatsappEmail a Friend

BADAƘALAR NAIRA MILIYAN 585: Gwamnati Ta Fara Binciken Ministar Agaji – Idris

Sakamakon ƙorafe-ƙorafe da rahotannin zargin da ake yi wa Ministar Harkokin Agaji da Jinƙai, Dakta Betta Edu, Gwamnatin Tarayya ta fara binciken yadda aka zuba naira miliyan 585.2 a asusun ajiyar wata ma’aikaciyar gwamnati, bisa umarnin ita ministar.

Related posts

Ɓatanci Ga Manzon Allah: Musulmi Sun Buƙaci Gwamnati Ta Hukunta Fasto Emmanuel Garba?

Fasto Ɗan Ƙungiyar Hausawan Bogi Da Ya Zagi Annabi Ya Ɓoye

April 15, 2026
Sheikh Mutawakkil Mustapha Ya Zama Alƙalin Kotun Shari’a ta Ɗaukaka Ƙara ta Jihar Katsina

Sheikh Mutawakkil Mustapha Ya Zama Alƙalin Kotun Shari’a ta Ɗaukaka Ƙara ta Jihar Katsina

February 13, 2026

Ministan Yaɗa Labarai da Wayar Da Kai, Alhaji Mohammed Idris, shi ne ya bayyana haka a ranar Lahadi cikin wata sanarwa ga manema labarai.

Ita dai Minista Betta Edu, ta na ci gaba da shan ragargaza daga ko’ina a faɗin ƙasar nan bayan an fallasa yadda ta bada umarnin a zuba zunzurutun kuɗi har naira miliyan 585.2 a cikin asusun banki na wata ma’aikaciyar gwamnati, wadda ita ce akawu mai kula da Kuɗaɗen Tallafin Marasa Galihu a ma’aikatar.

Dakta Edu ta fitar da wasiƙar bada umarnin zuba wa ma’aikaciyar kuɗin ne ga Akanta Janar na Tarayya a cikin Disamba, 2023, inda ta rubuta cewa a zuba kuɗin cikin asusun, duk kuwa da cewa yin hakan ya karya doka.

Duk da cewa Akanta Janar ya ce mata yin hakan karya doka ne, amma ya amince an biya kuɗin cikin aljihun asusun ma’aikaciyar, wanda ministar ta ce a zuba mata kuɗin.

Wannan ne ya jawo ce-ce-ku-ce da nuna damuwar da har Gwamnatin Tarayya ta gaggauta fara bincike.

Sai dai ita kuma Edu ta ce ba ta aikata wani laifi da ya saɓa wa doka ba, duk kuwa da cewa akwai tambayoyin da ma’aikatar ta ya kamata ta amsa, haka shi ma ofishin Akanta Janar ɗin akwai tambayoyin da ya kamata ya amsa domin warware zare da abawa.

Cikin sanarwar da ya fitar a ranar Lahadi, Idris ya ce yanzu haka gwamnati ta fara bincike, sannan kuma ta gamsu da yadda ‘yan Nijeriya su ka nuna damuwar su dangane da wannan zargi da ake yi wa ita ministar.

Ya ce: “Mu na sane da dukkan ce-ce-ku-cen da ake ta yi kuma mu na tabbatar wa da ‘yan Nijeriya cewa gwamnati ta ɗauki wannan batu da muhimmancin gaske.”

Ya ci gaba da cewa Gwamnatin Tarayya, a ƙarƙashin shugabancin Bola Tinubu, ba ta gudanar da ayyukan ta cikin ƙumbiya-ƙumbiya.

Ya ce gwamnatin za ta tura kuɗaɗe a inda ya dace kai-tsaye, domin ayyukan biyan buƙatun ‘yan Nijeriya.

Haka nan kuma Idris ya yi kira tare da bada shawara ga jama’a da cewa a maida hankali wajen samun sahihan bayanai daga Ma’aikatar Yaɗa Labarai da Wayar da Kai da ya ke jagoranta.

Hakan a cewar sanarwar sa, ya na da nasaba da ganin yadda ake ta yaɗa labarai da bayanai marasa tushe balle makama da su ka shafi Gwamnatin Tarayya.

Previous Post

ZINATU MATAR GWANMA (1)

Next Post

BIU: Ziyarar Babban Birni A Kan Tsauni (4)

Related Posts

Ɓatanci Ga Manzon Allah: Musulmi Sun Buƙaci Gwamnati Ta Hukunta Fasto Emmanuel Garba?
Labarai

Fasto Ɗan Ƙungiyar Hausawan Bogi Da Ya Zagi Annabi Ya Ɓoye

April 15, 2026
Sheikh Mutawakkil Mustapha Ya Zama Alƙalin Kotun Shari’a ta Ɗaukaka Ƙara ta Jihar Katsina
Labarai

Sheikh Mutawakkil Mustapha Ya Zama Alƙalin Kotun Shari’a ta Ɗaukaka Ƙara ta Jihar Katsina

February 13, 2026
Bura women Celebrate Bukar Usman at 83
Labarai

Ƙungiyar Matan Al’ummar Bura Sun Karrama Dr. Bukar Usman Bisa Cika Shekaru 83

January 9, 2026
Next Post
BIU: Ziyarar Babban Birni A Kan Tsauni (4)

BIU: Ziyarar Babban Birni A Kan Tsauni (4)

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

RECOMMENDED NEWS

Wawason Dukiyar Al’umma: Gwamnatin Zamfara Ta Nemi Ba’asin Tsohon Gwamna Matawalle

Wawason Dukiyar Al’umma: Gwamnatin Zamfara Ta Nemi Ba’asin Tsohon Gwamna Matawalle

June 3, 2023
An Karrama Ɗanmadamin Yusufari Da Kambin Yabo Da Girmamawa

An Karrama Ɗanmadamin Yusufari Da Kambin Yabo Da Girmamawa

November 13, 2023
Ɓatanci Ga Manzon Allah: Musulmi Sun Buƙaci Gwamnati Ta Hukunta Fasto Emmanuel Garba?

Fasto Ɗan Ƙungiyar Hausawan Bogi Da Ya Zagi Annabi Ya Ɓoye

April 15, 2026
The Bloomsbury Handbook of Muslims and Popular Culture: An Endorsement

The Bloomsbury Handbook of Muslims and Popular Culture: An Endorsement

October 19, 2023

FOLLOW US

BROWSE BY CATEGORIES

  • Adabi
  • Addini
  • Babban Labari
  • Barkwanci
  • Dausayin Kauna
  • ENGLISH
  • Gizago
  • Gumbar Dutse
  • Hotuna
  • Labarai
  • Nishadi
  • Noma Da Kiwo
  • Sarauta
  • Shanshani
  • Sharhi
  • Sinadarin Rayuwa
  • Siyasa
  • Ta'aziyya
  • Wasanni

POPULAR NEWS

  • Gwamnan Katsina Ya Ƙi Amsar Kyautar Raguna 100 Daga Hannun Attajiri

    Gwamnan Katsina Ya Ƙi Amsar Kyautar Raguna 100 Daga Hannun Attajiri

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • Ta Tsinci Naira Miliyan 60 A Saudiyya Ta Miƙa Wa Hukuma

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • LUWAƊI DA YARA 14: Yadda Aka Bankaɗo Asirin Kabir Ɗan Hisba

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • Sojojin Najeriya Sun Kama Makashin Sarkin Gobir

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • BINCIKE: Zahirin Abin Da Ke Faruwa A BBC Hausa

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
Taskar Gizago

Follow us on social media:

Recent News

  • Mu Ji Tsoron Allah
  • Malam Nasir El-Rufa’i Da Ƙalubalen Rayuwa
  • Fasto Ɗan Ƙungiyar Hausawan Bogi Da Ya Zagi Annabi Ya Ɓoye

Category

  • Adabi
  • Addini
  • Babban Labari
  • Barkwanci
  • Dausayin Kauna
  • ENGLISH
  • Gizago
  • Gumbar Dutse
  • Hotuna
  • Labarai
  • Nishadi
  • Noma Da Kiwo
  • Sarauta
  • Shanshani
  • Sharhi
  • Sinadarin Rayuwa
  • Siyasa
  • Ta'aziyya
  • Wasanni

Recent News

Mu Ji Tsoron Allah

Mu Ji Tsoron Allah

April 17, 2026
Malam Nasir El-Rufa’i Da Ƙalubalen Rayuwa

Malam Nasir El-Rufa’i Da Ƙalubalen Rayuwa

April 16, 2026
  • About us
  • Advertise
  • Careers
  • Contact

© 2023 Taskar Gizago - Ilimi da Nishadi

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
  • Sharhi
  • Gumbar Dutse
  • Dausayin Kauna
  • Gizago
  • Sarauta
  • Sinadari
  • Adabi da Nishadi
  • Barkwanci
  • Shanshani
  • Hotuna

© 2023 Taskar Gizago - Ilimi da Nishadi

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
This website uses cookies. By continuing to use this website you are giving consent to cookies being used.