NASIHARMU TA YAU (23)

__________
Ya ‘yan uwana, ko kun lura da yadda al’amuran rayuwa suka hargitse a ƙasarmu? Ko kun lura da yadda halayenmu suka canja, suka karkace zuwa son rai da rashin gaskiya? Ko kun lura yadda muka karkata zuwa ga duniya da abin duniya? Ko kun lura cewa tausayi da jin ƙai sun yi ƙaranci a tsakaninmu? Ya kamata mu yi karatun-ta-natsu, mu GYARA HALAYENMU, muddin dai muna son RAYUWARMU ta hau saiti. BARKA DA JUMA’A!
__________












