RAMADAN KARIM: 20-1447

__________
‘Yan uwa, ina yi maku sallama irin ta Musulunci, Assalamu alaikum warahmatullahi wabarakatuhu. Yau Litinin, Allah ya nuna mana rana ta 20 a Ramadan. Yau ma ga nasiharmu:
Yau ma dai za mu yi tsokaci ne dangane da kyautata mu’amala. Har kullum dai ya kamata mu gane, a rayuwar duniya, babu abu mai kyau, mai samar da natsuwa da zaman lafiya kamar kyakkyawar mu’amala.
Ya ɗan uwa, wani babban sirrin kyautatawa shi ne sakin fuska da murmushi a duk lokacin da za ka gana da ɗan uwanka. Shin a wurin aiki ne ko sana’a? A gida ne ko kuwa wajen wata harka da za ta haɗa ka da wasu? Ka zama mai sakin fuska. Domin masu iya magana ma sun ce, shimfiɗar fuska ta fi ta tabarma.
Allah (swt) a cikin Alkur’ani mai girma, a Suratu Abasa 80:38-39, yana cewa: “Fuskoki masu haske suna dariya.” Manzon Allah (saw), a ruwayar Tirmizi, Hadisi mai lamba 1956, yana cewa: “Murmushi sadaka ne.”
Allah ka sanya mu daga cikin masu kyautata mu’amala kuma ka ba mu ladar haka. Amin-Summa-Amin.
__________













