• About us
  • Advertise
  • Careers
  • Contact
Thursday, March 5, 2026
  • Login
Taskar Gizago
Advertisement
  • Gida
  • Labarai
  • Sharhi
  • Gumbar Dutse
  • Dausayin Kauna
  • Gizago
  • Sarauta
  • Sinadari
  • Adabi da Nishadi
  • Barkwanci
  • Shanshani
  • Hotuna
Taskar Gizago
No Result
View All Result
Home Gizago

Yunkurin ‘Yan Ba-Zata/Hausawan Bogi Na Haddasa Ruɗani A Arewa (12)

TSOKACI

Bashir Yahuza Malumfashi by Bashir Yahuza Malumfashi
January 31, 2026
in Gizago
0
Yunkurin ‘Yan Ba-Zata/Hausawan Bogi Na Haddasa Ruɗani A Arewa (12)

Mabiya Addinin Kirista a yayin ibada a majami'an a Arewacin Najeriya

20
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterWhatsappEmail a Friend

Yunkurin ‘Yan Ba-Zata/Hausawan Bogi Na Haddasa Ruɗani A Arewa (12)

Daga Bashir Yahuza Malumfashi

Related posts

Yunƙurin ‘Yan Ba-Zata/Hausawan Bogi Na Haddasa Ruɗani A Arewa (14)

Yunƙurin ‘Yan Ba-Zata/Hausawan Bogi Na Haddasa Ruɗani A Arewa (14)

March 1, 2026
#AdalciGaWalida (01): ƘIRA GA GWAMNATIN JIHAR JIGAWA DA TA ƊAUKI MATAKIN GAUGAWA A KAN KUƁUTAR DA WALIDA ABDULHADI

#AdalciGaWalida (01): ƘIRA GA GWAMNATIN JIHAR JIGAWA DA TA ƊAUKI MATAKIN GAUGAWA A KAN KUƁUTAR DA WALIDA ABDULHADI

February 23, 2026
Mabiya Addinin Kirista a yayin ibada a majami’an a Arewacin Najeriya

 

                        __________

√ Jan Hankali Zuwa Ga Kiristocin Arewa:

A yau zan karkata akalar wannan tsokaci musamman domin aika saƙo na musamman zuwa ga Kiristocin Arewa har da Hausawa da Fulani. Kada ku ji abin banbarakwai, domin na ambata “Kirista” a laƙanin sakon. Tabbas, zuwa gare su nake wannan saƙon, sanin cewa akwai wasu mutane da dama da ba su san cewa akwai Hausawa da Fulani mabiya addinin Kirista ba.

Ya ku Kiristocin Arewa, musamman ‘yan ƙabilar Hausawa da Fulani, ina kira a gare ku domin ku fahimta da wata babbar masifa da take tunkaro al’ummar Arewa gaba ɗaya – Musulmi da Kirista da Maguzawa. A yau an samu wasu hatsabibai da Shaiɗan ya fitsare wa kunnuwa, sun haɗa kai da ‘yan tawayen Biyafara da ƙabilun Middlebelt da nufin haddasa rikici tsakanin al’ummar Arewa gaba ɗaya.

Da dama daga cikin waɗannan shaiɗanu, suna fakewa ne da Addinin Kirista da Ƙabilanci domin cin ma wannan muguwar manufa tasu. Misali, a mafi yawan zantukansu a Soshalmidiya, za ku ga suna tsokanar rigima, suna haɗa husuma tsakanin Kirista da Musulmi ko kuma tsakanin Hausawa da Fulani.

A wannan gaɓa, ina kiran ku da ku fahimci cewa wannan lamari ba alheri ba ne ga al’ummar Arewa da ma Najeriya baki ɗaya. Lallai ne ku bijire wa shaiɗanun nan, kada ku goya masu baya wajen wargaza zaman lafiyar al’umma. Ku sani cewa dukkanmu abokan zaman juna ne a maƙwabtaka da zumunci na shekaru masu yawa. Duk da cewa muna da bambancin yare da addini amma akwai amincin zaman tare da juna.

Wani babban al’amari ma da ya kamata ku gane shi ne, addinin Kirista ya haramta tashin hankali tsakanin mutane. Kuma ya haramta gaba da ƙiyayya ko nuna ƙabilanci ga maƙwabta. A addinin Kirista, kyautata wa maƙwabci yana daga cikin manyan umarnin Allah da Yesu Almasihu ya koyar. Littafi Mai Tsarki ya nuna cewa soyayya ita ce ginshiƙin rayuwar Kirista. Yesu ya ce: “Ka ƙaunaci Ubangiji Allahnka da dukan zuciyarka… kuma ka ƙaunaci maƙwabcinka kamar kanka” (Matta 22:37–39). Wannan yana nuna cewa ba za a iya raba bautar Allah da kyautata wa mutane ba, domin duk wanda ya ƙaunaci Allah dole ne ya ƙaunaci maƙwabcinsa.

Kyautata wa maƙwabci alama ce ta gaskiyar ban gaskiyar Kirista. A cikin 1 Yohanna 4:20, Littafi Mai Tsarki ya ce: “Idan wani ya ce yana ƙaunar Allah amma yana ƙin ɗan uwansa, maƙaryaci ne.” Wannan ayar tana nuna cewa ba za a iya iƙirarin ƙaunar Allah alhali ana cutar da mutane ko ana raina su ba. Kyautatawa, taimako da nuna tausayi su ne shaidar cewa mutum yana rayuwa bisa koyarwar Kirista.

Yesu ya ƙarfafa muhimmancin kyautata wa kowa ta hanyar labarin “Mutumin Kirki daga Samariya” (Luka 10:33–37). A wannan labari, Samariyawan da aka raina a wancan lokaci, shi ne ya taimaki mutumin da aka ji masa rauni, yayin da ’yan ƙabilarsa suka ƙi taimako. Yesu ya nuna cewa maƙwabci ba wai ɗan ƙabila ko addininka kaɗai ba ne amma duk wanda ke cikin buƙata.

Littafi Mai Tsarki ya kuma umurci Kiristoci da su kasance masu jin ƙai da tausayi. A Kolosiyawa 3:12 an ce: “Ku sa zuciyar tausayi, alheri, tawali’u, haƙuri da juriya.” Waɗannan halaye su ne ginshiƙan kyautata wa maƙwabci, domin suna haifar da zaman lafiya, fahimta, da haɗin kai a cikin al’umma.

Kyautata wa maƙwabci yana kawo albarka ga mutum da al’umma baki ɗaya. A Misalai 11:25 an ce: “Mai kyautatawa zai wadatu, mai shayar da wasu shi ma za a shayar da shi.” Wannan na nuna cewa alheri yana dawowa ga wanda ya aikata shi. Al’umma mai cike da tausayi da taimakon juna za ta fi kasancewa cikin kwanciyar hankali da ci gaba.

A gefe guda kuma, ƙabilanci da wariyar launin fata suna da illa mai tsanani a fahimtar Kirista. Littafi Mai Tsarki ya nuna cewa Allah bai bambanta mutane bisa launi, harshe, ko ƙabila ba. A Ayyukan Manzanni 10:34–35 an ce: “Allah bai nuna bambanci ba, amma a kowace al’umma duk wanda yake tsoronsa yana aikata adalci, abin karɓa ne a gare shi.” Wannan ayar tana soke duk wani tunani na fifita wata ƙabila ko launi a kan wata.

Ƙabilanci da wariyar launin fata suna karya dokar ƙauna. Galatiyawa 3:28 ya ce: “Ba Bayahude ko Ba’al’umma, ba bawa ko ’yantacce, ba namiji ko mace, gama dukanku ɗaya ne cikin Almasihu Yesu.” Wannan yana nuna cewa a gaban Allah, dukkan mutane ɗaya suke kuma duk wata rarrabuwar kai bisa ƙabila ko launi ba ta da tushe a koyarwar Kirista.

Illar ƙabilanci da wariyar launin fata ta haɗa da haifar da ƙiyayya, tashin hankali da rarrabuwar kai. A Yakubu 2:1 an ce: “Kada ku nuna bambanci ga mutane.” Domin nuna bambanci yana haifar da rashin adalci, yana raunana zumunci kuma yana kawo rushewar zaman lafiya a cikin al’umma.

Ƙabilanci da wariyar launin fata suna kuma hana bisharar Kiristi tasiri, domin suna saɓa wa ruhin bisharar ƙauna da sulhu. A 2 Korintiyawa 5:18, Littafi Mai Tsarki ya ce Allah ya ba mu “hidimar sasanci.” Wannan yana nufin Kiristoci an kira su su zama masu haɗa kan mutane, ba masu rarraba su ba.

Haka kuma an ƙarfafa Kirista da ya zama mai yafiya idan an saɓa masa, ba mai ramuwar gayya ko ɗaukar da sa ba. A cikin Matta 18:21–22, Littafi Mai Tsarki ya ce: “Sa’an nan Bitrus ya zo wurin Yesu ya ce, ‘Ubangiji, sau nawa zan yafe wa ɗan uwana idan ya yi mini laifi? Har sau bakwai ne? Yesu ya ce masa, ‘Ba sau bakwai nake cewa ba, sai dai har sau saba’in sau bakwai.” Wannan ayar tana nuna cewa yafiya a Kiristanci ba ta da iyaka.

A Afisiyawa 4:32, an bayyana cewa: “Ku kasance masu alheri da tausayi ga juna, kuna yafiya ga juna, kamar yadda Allah ya yafe muku a cikin Almasihu.” Wannan shi ke nuna cewa, yafiyar da muke yi wa mutane ya kamata ta zama kamar yadda Allah Ya yafe mana.

A Kolosiyawa 3:13, an ce: “Ku jure wa juna, ku kuma yafe wa juna idan wani yana da ƙorafi a kan wani. Kamar yadda Ubangiji ya yafe muku, haka ku ma ku yi.” Don haka haƙuri da yafiya su ne ginshiƙan zaman lafiya tsakanin mutane.

Misalai 15:18, an bayyana cewa: “Mai saurin fushi yana tayar da gardama amma mai haƙuri yana kwantar da husuma.” Wannan shi ke nuna mana haƙuri yana kawo zaman lafiya, yayin da fushi ke kawo rikici.

A Romawa 12:17–18, an ce: “Kada ku rama mugunta da mugunta… idan zai yiwu, gwargwadon ikonku, ku zauna lafiya da kowa.” A nan, an umurci Kirista, an kira shi zuwa zaman lafiya, ba zuwa ramuwar gayya ba.

A Matta 5:39, an bayyana cewa: “Amma ni ina gaya muku, kada ku yi tsayayya da mai mugunta; amma duk wanda ya mare ka a gefen dama na kumatu, ka juya masa ɗayan gefen ma.” Haka kuma a cikin Luka 6:29, an ce: “Wanda ya mare ka a kumatu ɗaya, ka juya masa ɗayan ma; wanda ya ƙwace rigarka, kada ka hana shi riga ta ciki ma.”

Waɗannan ayoyi suna koyar da cewa Kirista ya kamata ya rinjayi mugunta da alheri, ya guji ramuwar gayya, ya kuma nuna haƙuri da yafiya ko da a lokacin da ake masa zalunci ne.

Daga ƙarshe, addinin Kirista yana koyar da kyautata wa maƙwabci a matsayin wajibi na ruhaniya da zamantakewa, tare da ƙin amincewa da ƙabilanci da wariyar launin fata. Kyautatawa tana gina al’umma, tana kawo zaman lafiya, kuma tana nuna gaskiyar bin Kristi. Ƙabilanci da wariya kuwa suna lalata zumunci, suna karya umarnin Allah kuma suna jawo fushinsa, domin “Allah ƙauna ne” (1 Yohanna 4:8) kuma duk abin da ya saɓa wa ƙauna ba daga gare shi yake ba.

Saboda haka, lallai ne al’ummar Kirista da Musulmin Arewa su zauna lafiya, su kiyayi duk wasu shaiɗanu da za su ingiza su zuwa tashin hankali da juna. Mu gane cewa, ida fitina ta tashi, za ta shafi kowa, ba tare da la’akari da ƙabila ko addinin mutum ba. Zaman lafiya shi ne arziki, tashin hankali kuwa asara ne!

_______________

Previous Post

Sharhi Kan Littafin Tarihin Philip Chikwuedo Asiodu

Next Post

KWANAN WATAN HIJIRIYYA A YAU LITININ

Related Posts

Yunƙurin ‘Yan Ba-Zata/Hausawan Bogi Na Haddasa Ruɗani A Arewa (14)
Gizago

Yunƙurin ‘Yan Ba-Zata/Hausawan Bogi Na Haddasa Ruɗani A Arewa (14)

March 1, 2026
#AdalciGaWalida (01): ƘIRA GA GWAMNATIN JIHAR JIGAWA DA TA ƊAUKI MATAKIN GAUGAWA A KAN KUƁUTAR DA WALIDA ABDULHADI
Gizago

#AdalciGaWalida (01): ƘIRA GA GWAMNATIN JIHAR JIGAWA DA TA ƊAUKI MATAKIN GAUGAWA A KAN KUƁUTAR DA WALIDA ABDULHADI

February 23, 2026
Yunkurin ‘Yan Ba-Zata/Hausawan Bogi Na Haddasa Ruɗani A Arewa (13)
Gizago

Yunkurin ‘Yan Ba-Zata/Hausawan Bogi Na Haddasa Ruɗani A Arewa (13)

February 20, 2026
Next Post
KWANAN WATAN HIJIRIYYA A YAU LITININ

KWANAN WATAN HIJIRIYYA A YAU LITININ

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

RECOMMENDED NEWS

Jigon Ɗan Kwankwasiyya Ya Canja Sheƙa Zuwa APC  Daga Muhammad Mustapha

Jigon Ɗan Kwankwasiyya Ya Canja Sheƙa Zuwa APC Daga Muhammad Mustapha

September 28, 2023
Huɗubar Jumu’a Daga Limamin Masallacin Tumbu-Madalla

Huɗubar Jumu’a Daga Limamin Masallacin Tumbu-Madalla

July 7, 2023
ZINATU MATAR GWANMA (1)

ZINATU MATAR GWANMA (1)

January 7, 2024

Uƙubar Da Talaka Ke Ciki Ta Isa Haka Nan – ZAINAB AHMAD

August 12, 2023

FOLLOW US

BROWSE BY CATEGORIES

  • Adabi
  • Addini
  • Babban Labari
  • Barkwanci
  • Dausayin Kauna
  • ENGLISH
  • Gizago
  • Gumbar Dutse
  • Hotuna
  • Labarai
  • Nishadi
  • Noma Da Kiwo
  • Sarauta
  • Shanshani
  • Sharhi
  • Sinadarin Rayuwa
  • Siyasa
  • Ta'aziyya
  • Wasanni

POPULAR NEWS

  • Gwamnan Katsina Ya Ƙi Amsar Kyautar Raguna 100 Daga Hannun Attajiri

    Gwamnan Katsina Ya Ƙi Amsar Kyautar Raguna 100 Daga Hannun Attajiri

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • Ta Tsinci Naira Miliyan 60 A Saudiyya Ta Miƙa Wa Hukuma

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • LUWAƊI DA YARA 14: Yadda Aka Bankaɗo Asirin Kabir Ɗan Hisba

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • Sojojin Najeriya Sun Kama Makashin Sarkin Gobir

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • BINCIKE: Zahirin Abin Da Ke Faruwa A BBC Hausa

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
Taskar Gizago

Follow us on social media:

Recent News

  • Injiniya Tukur Hassan Tingilin (1978-2026)
  • RAMADAN KARIM: 16-1447
  • Exposing Plans of Fake Hausa Activists & Ba-Zata Mischief Mongers to Cause Confusion and Discord in Northern Nigeria (7)

Category

  • Adabi
  • Addini
  • Babban Labari
  • Barkwanci
  • Dausayin Kauna
  • ENGLISH
  • Gizago
  • Gumbar Dutse
  • Hotuna
  • Labarai
  • Nishadi
  • Noma Da Kiwo
  • Sarauta
  • Shanshani
  • Sharhi
  • Sinadarin Rayuwa
  • Siyasa
  • Ta'aziyya
  • Wasanni

Recent News

RAMADAN KARIM: 16-1447

Injiniya Tukur Hassan Tingilin (1978-2026)

March 5, 2026
RAMADAN KARIM: 16-1447

RAMADAN KARIM: 16-1447

March 5, 2026
  • About us
  • Advertise
  • Careers
  • Contact

© 2023 Taskar Gizago - Ilimi da Nishadi

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
  • Sharhi
  • Gumbar Dutse
  • Dausayin Kauna
  • Gizago
  • Sarauta
  • Sinadari
  • Adabi da Nishadi
  • Barkwanci
  • Shanshani
  • Hotuna

© 2023 Taskar Gizago - Ilimi da Nishadi

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
This website uses cookies. By continuing to use this website you are giving consent to cookies being used.