GA ZAKARU 20:
NA GASAR RUBUTUN GAJERUN LABARUN HAUSA TA GIDAUNIYAR ZANNA-WALI (2025)

__________
Ina marubutan da suka fafata a Gasar Rubutun Gajerun Labarun Hausa ta Gidauniyar Zanna-Wali? To, albishirinku! Alƙalan gasa sun kammala aikinsu na tace nagartattun labarai 20 daga cikin 40 da suka fafata a zagaye na biyu. A yau Juma’a, 23-01-2026, ga sunayen ZAKARU 20 da suka samu nasara!
Waɗannan zakarun 20, dukkansu sun cancanci yabo kuma daga cikinsu ne manyan ZAKARU UKU suka yi zarra, waɗanda za su samu manyan kyaututtuka. Sauran ZAKARU 17 kuma za su samu tukwicin kuɗi da shaidar yabo, a yayin BIKIN GABATAR DA LITTAFIN.
Dukkan labaru 20 da suka yi zarra, yanzu haka ana kintsa zu, domin wallafa su a KUNDI ƊAYA (Littafi). Muna sanar da waɗannan zakaru 20 cewa su turo da taƙaitaccen tarihinsu da hotunansu (passport) a E-mail: gasarzannawali2025@gmail.com domin wallafawa tare da labarinsu a wanna littafi.
•••••••
ZAKARU 20
(Lambobin 1 zuwa 20 ba yana nufin matsayin kowa ba. Daga cikinsu ne za a fitar da MANYAN ZAKARU na 1 zuwa na 3, a lokacin Bikin Gabatar da Littafin da Miƙa Kyaututtuka).
1-YANKAN BAYA – Hadiza Ibrahim Ɗan Auta.
2-ALHAKI KWAIKWIYO – Ayuba Muhammad Ɗanzaki.
3-SITIYARIN MULKI – Na’ima Sulaiman Daƙayyawa.
4-GOBENMU – Hassana Suleiman.
5-KU DUBE MU – Zainab Abdulrahman.
6-WUTAR FANSA – Faisal Haruna Hunƙuyi.
7-TSUNTSAYEN DAJI – Mustapha Bashir.
8-SHUGABAN ƘASA – Binyaminu Zakari Hamisu.
9-ƘARAR ƘAHO A ƘAUYE – Sani Muhammad Lawan.
10-TSUGUNE BA TA ƘARE BA – Aminu Ahmad Muhammad.
11-JARUMAR UWA – Lantana Ja’afar.
12-KUNYAR ƘARSHE – Hassana Labaran Ɗanlarabawa.
13-MAKAUNIYAR AL’UMMA – Maimuna Iyami.
14-MAFITAR GOBENMU – Zainab Mustapha Musa.
15-SAKAINAR KASHI – Fatima Umar.
16-MURYAR ZUCIYA – Hamza Dawaki.
17-KUKAN ZUCI – Rahinatou Mamoudou.
18-BAKIN ZARE – Jibrin Yusuf Kaila.
19-RIBA BIYU – Khadijah Muhammad.
20-A DUBE MU – Maryam Ibrahim Liti.
_______________
Zannan Galadima, Walin Ƙafur, Cigarin Danejin Katsina, Manajan Daraktan Hukumar Ruwa ta Jihar Katsina, Injiniya Dr. Tukur Tingilin FNSE, a matsayinsa na Shugaban Gidauniyar Zanna-Wali, yana taya dukkan marubutan da suka fafata a wannan gasa murna da fatan alheri.
_______________













