• About us
  • Advertise
  • Careers
  • Contact
Thursday, January 22, 2026
  • Login
Taskar Gizago
Advertisement
  • Gida
  • Labarai
  • Sharhi
  • Gumbar Dutse
  • Dausayin Kauna
  • Gizago
  • Sarauta
  • Sinadari
  • Adabi da Nishadi
  • Barkwanci
  • Shanshani
  • Hotuna
Taskar Gizago
No Result
View All Result
Home Babban Labari

Hukumar NDLEA Ta Kama Ɗan Indiya Da Muggan Ƙwayoyi Na Naira Biliyan 3.9

BABBAN LABARI

Bashir Yahuza Malumfashi by Bashir Yahuza Malumfashi
September 17, 2025
in Babban Labari
0
Hukumar NDLEA Ta Kama Ɗan Indiya Da Muggan Ƙwayoyi Na Naira Biliyan 3.9

Gupta Ravi Kumar, ɗan Indiya da aka kama da safarar ƙwaya

5
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterWhatsappEmail a Friend

Hukumar NDLEA Ta Kama Ɗan Indiya Da Muggan Ƙwayoyi Na Naira Biliyan 3.9

Daga Bashir Yahuza Malumfashi

Related posts

Hukunta Ɗan T+adda Victor Solomon: Madalla Da Gwamnatin Jihar Kaduna

Hukunta Ɗan T+adda Victor Solomon: Madalla Da Gwamnatin Jihar Kaduna

January 14, 2026
Kishin Ilimi Ya Sa Ni Tallafa Wa Ɗalibai 110 A Malumfashi Da Ƙafur – Dokta Tukur Tingilin

Kishin Ilimi Ya Sa Ni Tallafa Wa Ɗalibai 110 A Malumfashi Da Ƙafur – Dokta Tukur Tingilin

January 4, 2026
Shi ma jami’an NDLEA suka kama shi

 

__________
Wani ɗan kasuwa ɗan Indiya, Gupta Ravi Kumar, tare da wasu ‘yan Najeriya uku: Ogunlana Noah Olanrewaju, Olushola Idrees Kayode da Bakare Korede Muheeb sun shiga hannun jami’an hukumar NDLEA, sakamakon kama su da aka yi da kwalabe miliyan biyu da dubu 248 na Tramadol (200mg/225mg) a Filin Jirgin Sama na Murtala Muhammed (MMIA), Ikeja, Lagos.

Wannan Tramadol da aka kama, kamar yadda Daraktan Watsa Labarai na Hukumar, Femi Babafemi ya bayyana, ya kai darajarta Naira biliyan 3.9 kuma an shigo da shi ne daga Delhi, Babban Birnin ƙasar Indiya. An samu maganin ne a ɓoye cikin katon-katon 114. Jami’an hukumar sun bankaɗo shi ne a wani jirgin Ethiopian Airlines da ya iso Legas a ranar Litinin, 8 ga Satumba, 2025.

Su ma sun shiga hannun NDLEA

“Yadda lamarin ya faru shi ne, bayan isowar jirgin daga Indiya, jami’anmu sun saka ido a kansa, inda cikin lokaci suka yi dirar mikiya kan wani dillalin shigo da kaya da direbobi biyu, waɗanda suka yi ƙoƙarin fitar da kayan da manyan motoci biyu ranar Juma’a, 11 ga Satumba.” A cewar Jami’in Watsa Labaran Hukumar, Femi. Ya ƙara da cewa, wannan bincike ne ya kai su ga kama ɗan kasuwar mai suna Gupta Ravi Kumar, yayin da yake ƙoƙarin karɓar kayan.

Haka kuma, a wani ƙoƙarin, jami’an na NDLEA, a ranar Lahadi, 7 ga Satumba, sun kama wani fasinja, Onyeganochi Stanley Ifeanyi, da yake kan hanyarsa ta zuwa birnin Doha a jirgin Qatar Airlines. Da suka bincika akwatinsa, sun gano tabar wiwi mai nauyin giram 900. Ya ce wani ɗan Najeriya ne da ke zaune a Qatar, Ohadiegwu Anthony Uchenna, ya ba shi akwatin don ya kai masa Doha.

Da jami’an suka tsananta bincike, sun sake cafke Uchenna, wanda ya raka shi filin jirgin. A ɗakinsa da ke Ajao Estate, an gano ƙarin giram 200 na wannan tabar. Ya amsa cewa shi ne zai dawo daga Doha daga baya ya karɓi akwatin idan Onyeganochi ya tsallake binciken tsaro.

Su ma sun shiga hannu

Shugaban Hukumar NDLEA, Birgediya Janar Mohamed Buba Marwa (mai ritaya) ya yaba da ƙoƙarin jami’an nasa da ke aiki a sassa daban-daban na ƙasar nan. Ya kuma buƙace su da su ci gaba da bin tsarin daidaito wajen yaƙi da miyagun ƙwayoyi.
__________

Previous Post

BAKIN JAƁA (4)

Next Post

Abin Da Ya Sa Na Naɗa Mataimaka 85 – Ciyaman Mukhtari City

Related Posts

Hukunta Ɗan T+adda Victor Solomon: Madalla Da Gwamnatin Jihar Kaduna
Babban Labari

Hukunta Ɗan T+adda Victor Solomon: Madalla Da Gwamnatin Jihar Kaduna

January 14, 2026
Kishin Ilimi Ya Sa Ni Tallafa Wa Ɗalibai 110 A Malumfashi Da Ƙafur – Dokta Tukur Tingilin
Babban Labari

Kishin Ilimi Ya Sa Ni Tallafa Wa Ɗalibai 110 A Malumfashi Da Ƙafur – Dokta Tukur Tingilin

January 4, 2026
Mawaƙi Kizz Daniel Ya Amshi Musulunci
Babban Labari

Mawaƙi Kizz Daniel Ya Amshi Musulunci

January 3, 2026
Next Post
Abin Da Ya Sa Na Naɗa Mataimaka 85 – Ciyaman Mukhtari City

Abin Da Ya Sa Na Naɗa Mataimaka 85 - Ciyaman Mukhtari City

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

RECOMMENDED NEWS

Yan Bindiga Sun Sako Miji Da Matarsa Bayan An Biya Naira Miliyan 50

Yan Bindiga Sun Sako Miji Da Matarsa Bayan An Biya Naira Miliyan 50

September 18, 2025
Mawaƙi Kizz Daniel Ya Amshi Musulunci

Mawaƙi Kizz Daniel Ya Amshi Musulunci

January 3, 2026
Kada Ka Karaya Da Rayuwa

Kada Ka Karaya Da Rayuwa

November 30, 2025
Daura Birnin Bayajidda: Janar Buratai Da Ayarinsa Sun Ziyarci Buhari Da Sarki

Daura Birnin Bayajidda: Janar Buratai Da Ayarinsa Sun Ziyarci Buhari Da Sarki

June 4, 2023

FOLLOW US

BROWSE BY CATEGORIES

  • Adabi
  • Addini
  • Babban Labari
  • Barkwanci
  • Dausayin Kauna
  • ENGLISH
  • Gizago
  • Gumbar Dutse
  • Hotuna
  • Labarai
  • Nishadi
  • Noma Da Kiwo
  • Sarauta
  • Shanshani
  • Sharhi
  • Sinadarin Rayuwa
  • Siyasa
  • Ta'aziyya
  • Wasanni

POPULAR NEWS

  • Gwamnan Katsina Ya Ƙi Amsar Kyautar Raguna 100 Daga Hannun Attajiri

    Gwamnan Katsina Ya Ƙi Amsar Kyautar Raguna 100 Daga Hannun Attajiri

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • Ta Tsinci Naira Miliyan 60 A Saudiyya Ta Miƙa Wa Hukuma

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • LUWAƊI DA YARA 14: Yadda Aka Bankaɗo Asirin Kabir Ɗan Hisba

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • Sojojin Najeriya Sun Kama Makashin Sarkin Gobir

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • BINCIKE: Zahirin Abin Da Ke Faruwa A BBC Hausa

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
Taskar Gizago

Follow us on social media:

Recent News

  • Exposing Plans of Fake Hausa Activists & Ba-Zata Mischief Mongers to Cause Confusion and Discord in Northern Nigeria (1)
  • Cikar Shekaru 83 A Duniya: Ranar Da Na Ga Zumunci Da Fatan Alheri Daga Masoya
  • Nazari, Tsokaci Da Sharhin Littafin Tarkon Mut’a

Category

  • Adabi
  • Addini
  • Babban Labari
  • Barkwanci
  • Dausayin Kauna
  • ENGLISH
  • Gizago
  • Gumbar Dutse
  • Hotuna
  • Labarai
  • Nishadi
  • Noma Da Kiwo
  • Sarauta
  • Shanshani
  • Sharhi
  • Sinadarin Rayuwa
  • Siyasa
  • Ta'aziyya
  • Wasanni

Recent News

Exposing Plans of Fake Hausa Activists & Ba-Zata Mischief Mongers to Cause Confusion and Discord in Northern Nigeria (1)

Exposing Plans of Fake Hausa Activists & Ba-Zata Mischief Mongers to Cause Confusion and Discord in Northern Nigeria (1)

January 21, 2026
My 83rd Birthday and the Kindred Spirit

Cikar Shekaru 83 A Duniya: Ranar Da Na Ga Zumunci Da Fatan Alheri Daga Masoya

January 19, 2026
  • About us
  • Advertise
  • Careers
  • Contact

© 2023 Taskar Gizago - Ilimi da Nishadi

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
  • Sharhi
  • Gumbar Dutse
  • Dausayin Kauna
  • Gizago
  • Sarauta
  • Sinadari
  • Adabi da Nishadi
  • Barkwanci
  • Shanshani
  • Hotuna

© 2023 Taskar Gizago - Ilimi da Nishadi

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
This website uses cookies. By continuing to use this website you are giving consent to cookies being used.