• About us
  • Advertise
  • Careers
  • Contact
Thursday, January 22, 2026
  • Login
Taskar Gizago
Advertisement
  • Gida
  • Labarai
  • Sharhi
  • Gumbar Dutse
  • Dausayin Kauna
  • Gizago
  • Sarauta
  • Sinadari
  • Adabi da Nishadi
  • Barkwanci
  • Shanshani
  • Hotuna
Taskar Gizago
No Result
View All Result
Home Gizago

BUNKASA TATTALIN ARZIKIN NAJERIYA: Tsakanin Dangote Da Gwamnatin Tarayya

TSOKACIN MAKO

Bashir Yahuza Malumfashi by Bashir Yahuza Malumfashi
July 31, 2024
in Gizago
0
BUNKASA TATTALIN ARZIKIN NAJERIYA: Tsakanin Dangote Da Gwamnatin Tarayya

Tsokacin Mako

23
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterWhatsappEmail a Friend

BUNKASA TATTALIN ARZIKIN NAJERIYA:
Tsakanin Dangote Da Gwamnatin Tarayya

Daga Bashir Yahuza Malumfashi

Related posts

My 83rd Birthday and the Kindred Spirit

Cikar Shekaru 83 A Duniya: Ranar Da Na Ga Zumunci Da Fatan Alheri Daga Masoya

January 19, 2026
Yunkurin ‘Yan Ba-Zata/Hausawan Bogi Na Haddasa Ruɗani A Arewa (9)

Yunkurin ‘Yan Ba-Zata/Hausawan Bogi Na Haddasa Ruɗani A Arewa (9)

January 17, 2026
Matatar Man Dangote

Abu ne sananne ga kowace gwamnati da take son ganin al’ummarta ta ci gaba, ta ɗauki dukkan matakan da suka kamata, domin ganin ta bunƙasa tattalin arziƙinta. Waɗannan matakai kuwa sun haɗa da ƙarfafa wa ‘yan kasuwa na cikin gida da na waje gwiwa domin su zuba jari wajen gina kamfanoni domin sarrafa kayan masarufi, samar da ayyukan yi da sauransu.

Najeriya, a matsayinta na ƙasa mai tasowa, wacce Allah Ya hore wa yawan al’umma, wacce ke ɗauke da mutum sama da miliyan 200, wacce ke da albarkatun ƙasa da suka ƙunshi ɗanyen mai, iskar gas, tama da ƙarafa da sauran duwatsun alfarma; wacce kuma take da albarkatun ƙasar noma, babu shakka tana da tsananin buƙatar masu zuba jari a fannoni daban-daban. Hakan ya sanya ita kanta gwamnatin ƙasa, tun daga farko ta jajirce wajen kafa kamfanoni na ƙashin kanta. Waɗannan kuwa sun haɗa da kamfanin samar da wutar lantarki, kamfanin sadarwa, kamfanin mulmula ƙarafa da sauransu, duk da cewa a zamanin mulkin Olusegun Obasanjo ta sayar da su ga ‘yan kasuwa. Ta ɓangaren fetur kuwa, gwamnati ta samar da kamfanonin tace man fetur guda uku, matatar mai ta Warri, ta Fatakwal da kuma ta Kaduna.

Babu shakka albarkatun man fetur babban arziƙi ne ga kowace ƙasa. Don haka yadda Allah Ya hore wa Najeriya ɗanyen mai, abin alheri ne, domin kuwa an ƙiyasta cewa ita ce ta shida a sahun masu wannan arziƙi a duk duniya, ta farko kuma a nahiyar Afirka. Sai dai kuma wannan arziƙi da Allah Ya ba Najeriya sai ya zama ga ƙoshi ga kwanan yunwa, domin kuwa a yayin da rijiya ta ba da ruwa sai guga ta hana. Maimakon mai ya zama babbar hanyar bunƙasa almundahana, cin hanci da rashawa a ƙasa. Haka kuma sai ya mayar da al’ummarmu koma baya ta tattalin arziƙi kamar noma, haƙo ma’adinai da sauransu.

Gwamnatoci da dama, tun daga 1960 zuwa yau, sun ɗauki matakai daban-daban ta fuskar ɗanyen man fetur amma daga bisani abin sai ya zama tamkar na mai haƙar rijiya; ma’ana babu wani ci gaba da aka samu. Babban abin takaici ne a ce ƙasa kamar Najeriya, mai wadatar ɗanyen mai amma al’ummarta tana cikin ƙunci, talauci da rashi. Abin takaici ne a ce a cikin matatu uku da ake da su amma babu ɗaya da take aiki, duk kuwa da cewa a duk shekara ana kashe maƙudan kuɗi da sunan gyara su. Misali, kamar yadda wani sahihin rahoto ya tabbatar, daga shekarar 2002 zuwa 2022 (shekara 20), an kashe kimanin Naira tiriliyan 17 wajen gyaran waɗannan matatun mai na Najeriya amma babu biyan buƙata. Abin mamaki ma shi ne, shin wannan adadin kuɗin ba za su iya gina sababbin matatun mai na zamani ba? To me ya hana a gina sabbi, sai aka ɓige ga gyara da garambawul mara amfani?

Wata ayar tambaya kuma ita ce, wane dalili ne ya sanya Najeriya ta ɓige da sayo tataccen mai daga waje, duk kuwa da cewa Allah Ya wadata ta da arziƙin ɗanyen mai? A halin da ake ciki fa, akwai ƙasashen da Allah bai ba su arziƙin ɗanyen mai ba amma suna da matatun mai, duk domin su sauƙaƙa wa al’ummarsu samun wannan sinadari. A Najeriya, a kasafin kuɗin shekarar 2023 kaɗai, an kashe Naira tiriliyan 3.6 wajen biyan tallafin mai da ake sayowa daga ƙasashen waje, cikin watanni shida kacal! Wannan na nufin duk wata, gwamnati tana bayar da tallafin Naira biliyan 560 – tirƙashi!

Wani abin kulawa shi ne, shi fa ɗanyen mai ƙunshe yake da abubuwa masu tarin yawa. Kamar yadda masana suka tabbatar, akwai sinadarai sama da guda 144 a cikin ɗanyen mai, waɗanda kuma ake amfani da su wajen sarrafa abubuwa sama da guda 6000. Kaɗan daga cikinsu sun haɗa da shi kansa man fetur, man dizal, kananzir, man jirgin sama, baƙin mai, man birki, iskar gas ta girki da sauransu da dama. Maimakon a ce a Najeriya ake cin gajiyar duk waɗannan, an gwammace a sayar da ɗanyen man cikin araha, a sayo tatacce da tsada. Misalin haka, kamar babban manomi ne a ce ba zai iya girka abinci a gidansa ba, sai ya sayar da tsaba, ya sayo dafaffen tuwo a waje. Shin yaushe iyalansa za su ƙoshi daga abincin saye?

Matasan Najeriya

A tsawon lokaci, an sha zargin cewa wasu manyan jami’an gwamnati suna haɗa baki da manyan jami’an Hukumar Kula da Al’amuran Man Fetur (NNPC) da manyan dillalan mai wajen almundahana da karkatar da maƙudan kuɗaɗe zuwa aljifansu, a hadahadar shigo da tataccen man fetur daga ƙasashen waje. Wasu masu sharhi kan al’amuran yau da kullum sun bayyana cewa, irin waɗannan hamshaƙan mutane har sun kafa ƙaƙƙarfar ƙungiya ta ‘yan zagon ƙasa ga duk wani Shugaban Ƙasa da zai ƙuduri a kawo sauyi a harkar man fetur.

Dodon Mafiya

Mambobin wannan ƙungiya, su ne suka shaƙe wuyan talakkan Najeriya, suka hana a samu walwala ta hanyar arziƙin fetur da Allah Ya huwace mana. Dalili ke nan a tsawon zamani ɗan Najeriya ke fuskantar matsalar fetur, yana kwana a dogon layi a gidajen mai, domin samun fetur. Haka kuma, su ne suka hana matatun man ƙasar nan rawar gaban hatsi. Don haka, madamar ba a samu jajirtaccen shugaban da zai taka wa wannan algungumar ƙungiya birki ba, to babu ranar da za a samu sassauci a batun man fetur a Najeriya.

Domin ganin an samu tabbataccen ci gaba ta fannin ƙereƙere, noma da kiwo da kafa kamfanoni a Najeriya, shugabanni da dama sun fito da tsare-tsare tare da yin kira ga attajirai na cikin gida da na waje, domin su zo su zuba jari, su kafa kamfanoni a ƙasar nan. Kaɗan ne daga cikin ɗimbin attajiran da ake da su, suka amsa wannan kira. Ɗaya daga cikinsu, wanda ya nuna da gaske yake, shi ne attajiri mafi yawan dukiya a Afirka, Alhaji Aliko Dangote. Ya ɗauki lokaci wajen gina kamfanoni daban-daban a ƙasar nan da ma wasu ƙasashen Afirka. Ya saka hannunsa wajen harkokin sarrafa siminti da fulawa da suga da sauransu. Daga bisani kuma ya fantsama cikin harkokin mai.

Hamshaƙin attajiri Dangote, Shugaban Rukunonin Kamfanonin Dangote, ya yi ƙuru, ya tunkari gina katafariyar matatar mai, wacce aka yi ittifaƙin ita ce mafi girma da inganci a duk faɗin duniya. Ya kwashe kusan shekara goma yana aikin gina ta kuma ya kashe kimanin Dala biliyan 20 kafin kammala ta. Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari ne ya jagoranci bikin buɗe ta a Legas, a shekarar da ta gabata (2023).

Alhaji Aliko Dangote

Wasu daga cikin alfanun da wannan katafariyar matata za ta samar wa Najeriya da ma ƙasashen Afrika sun haɗa da:

√ Za ta riƙa tace gangar ɗanyen mai dubu 650 a kowace rana.

√ Za ta samar da ayyukan yi na kai tsaye da na kaikaice fiye da adadi.

√ Za ta samar da kuɗin shiga masu yawa ga Najeriya, musamman kuma za ta dakatar da faɗuwar darajar Naira, kasancewar za a daina sayo tataccen mai daga waje ta amfani da Dalar Amurka.

√ Za ta dakatar da hauhawar farashin man fetur da dangoginsa, kasancewar a cikin gida ake tace man.

√ Za ta bunƙasa harkokin noma, musamman saboda za a riƙa sarrafa takin zamani da dangoginsa.

√ Za ta magance kwararowar hamada saboda samuwar makamashin girki mai sauƙi na iskar gas, wanda haka zai sanya a daina sare itatuwa domin girki da sauransu.

√ Haka kuma matatar za ta zama ginshiƙin bunƙasa tattalin arziƙin ƙasa ta hanyoyi da dama, waɗanda aka sani da ma waɗanda ba a sani ba.

Ga duk wani mai kishin ƙasa, kamata ya yi ya yi murna da sanya albarka a wannan katafariyar matata ta Dangote. Amma ina! Bayan tiya akwai wata caca. Tuni aka fara shirya masa kutungwila da tuggu, tare da taɗiye masa ƙafa, domin ganin wannan matata ba ta samu nasara ba. Akwai zargi mai ƙarfi, cewa wannan muguwar ƙungiyar azzaluman ɓoye, su ne ke da hannu a lamarin.

A ‘yan kwanakin nan, sai da aka kai Dangote bango, ya fito ya kwarmata wa duniya, irin matsalolin da ake kawo masa, inda ta kai ga har ma ya fusata, ya ce a shirye yake ya sayar da matatar ga kamfanin NNPC, ya huta da wannan baƙar tsangwama.

Wani abin mamaki shi ne, na farko dai hukumomi sun nuna cewa ba za su sayar wa matatar Dangote ɗanyen mai ba, sai dai ya fita waje ya sayo abinsa. Ke nan an gudu ba a tsira ba. Daga nan kuma aka samu Shugaban Hukumar Kula da Harkokin Man Fetur na Tudu da na Teku – Nigerian Midstream and Downstream Petroleum Regulatory Authority (NMDPRA), mai suna Farouk Ahmed. Ya fito ƙarara yana faɗin munanan kalamai game da matatar man ta Dangote, tare da dakushe ta a idon duniya.

Babban jami’in, ya zargi matatar da cewa man dizal da ta fara tacewa, wai bai da inganci, gurɓatacce ne. Amma sai ga shi da aka zurfafa bincike, aka gano cewa ba gaskiya ba ne. Hasali ma kamfanin NNPC ne yake sayo gurɓataccen mai daga waje amma na Dangote ingantacce ne.

Shin duk me wannan yake nunawa? Abin fahimta shi ne, hamshaƙan ‘yan kasuwar mai da baragurbin jami’an gwamnati da suka daɗe suna ha’intar al’umma da sunan kwangilar shigo da mai daga waje, su ne suka shirya babban yaƙi da Dangote. Domin idan matatarsa ta yi nasara, shi ke nan an taka wa almundahanarsu birki. An toshe masu kafar wawurar dukiyar al’umma. Ke nan ya kamata shugabannin al’ummar Najeriya da su kansu al’umma, ya kamata su gane tsakanin masoyansu na gaskiya da maƙiyansu.

A kan haka, muddin dai gwamnati da gaske take, na irin kiraye-kirayen da take yi, na cewa attajirai na gida da na waje su zo su zuba jari a Najeriya, to ta ɗauki babban matakin taka wa maha’inta birki daga uzura wa Dangote da irinsa. Lallai ne al’umma su nuna goyon baya da ƙarfafa gwiwa ga attajirai masu kishi, irin Dangote domin samar da bunƙasasshen tattalin arziƙin ƙasa, ayyukan yi da walwala ga al’umma.
__________
Bashir Yahuza Malumfashi,
Babban Editan Mujallar Taskar Gizago,
Asabar 21/01/1446 (Hijiriyya)
27/07/2024 (Miladiyya)

Previous Post

REMEMBRENCE OF PHILIP SHEA: The Documentation of Northern Economic History

Next Post

NUJ Honors Gen. Buratai with Prestigious Award

Related Posts

My 83rd Birthday and the Kindred Spirit
Gizago

Cikar Shekaru 83 A Duniya: Ranar Da Na Ga Zumunci Da Fatan Alheri Daga Masoya

January 19, 2026
Yunkurin ‘Yan Ba-Zata/Hausawan Bogi Na Haddasa Ruɗani A Arewa (9)
Gizago

Yunkurin ‘Yan Ba-Zata/Hausawan Bogi Na Haddasa Ruɗani A Arewa (9)

January 17, 2026
Yunkurin ‘Yan Ba-Zata/Hausawan Bogi Na Haddasa Ruɗani A Arewa (8)
Gizago

Yunkurin ‘Yan Ba-Zata/Hausawan Bogi Na Haddasa Ruɗani A Arewa (8)

January 13, 2026
Next Post
NUJ Honors Gen. Buratai with Prestigious Award

NUJ Honors Gen. Buratai with Prestigious Award

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

RECOMMENDED NEWS

ALLAH YA JI ƘAN DSP ABBA ƊANMALAM

ALLAH YA JI ƘAN DSP ABBA ƊANMALAM

December 21, 2024
GENERAL ABACHA: A LETTER FROM HEAVEN

GENERAL ABACHA: A LETTER FROM HEAVEN

February 22, 2025
Jami’ar Bayero Ta Karrama Janar Buratai

Jami’ar Bayero Ta Karrama Janar Buratai

December 16, 2023
Kwamishina Saulawa Jajirtacce Ne – Dr. Bala Nuhu

Health: Daura sets to commission Federal Medical Center

September 9, 2023

FOLLOW US

BROWSE BY CATEGORIES

  • Adabi
  • Addini
  • Babban Labari
  • Barkwanci
  • Dausayin Kauna
  • ENGLISH
  • Gizago
  • Gumbar Dutse
  • Hotuna
  • Labarai
  • Nishadi
  • Noma Da Kiwo
  • Sarauta
  • Shanshani
  • Sharhi
  • Sinadarin Rayuwa
  • Siyasa
  • Ta'aziyya
  • Wasanni

POPULAR NEWS

  • Gwamnan Katsina Ya Ƙi Amsar Kyautar Raguna 100 Daga Hannun Attajiri

    Gwamnan Katsina Ya Ƙi Amsar Kyautar Raguna 100 Daga Hannun Attajiri

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • Ta Tsinci Naira Miliyan 60 A Saudiyya Ta Miƙa Wa Hukuma

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • LUWAƊI DA YARA 14: Yadda Aka Bankaɗo Asirin Kabir Ɗan Hisba

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • Sojojin Najeriya Sun Kama Makashin Sarkin Gobir

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • BINCIKE: Zahirin Abin Da Ke Faruwa A BBC Hausa

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
Taskar Gizago

Follow us on social media:

Recent News

  • Exposing Plans of Fake Hausa Activists & Ba-Zata Mischief Mongers to Cause Confusion and Discord in Northern Nigeria (1)
  • Cikar Shekaru 83 A Duniya: Ranar Da Na Ga Zumunci Da Fatan Alheri Daga Masoya
  • Nazari, Tsokaci Da Sharhin Littafin Tarkon Mut’a

Category

  • Adabi
  • Addini
  • Babban Labari
  • Barkwanci
  • Dausayin Kauna
  • ENGLISH
  • Gizago
  • Gumbar Dutse
  • Hotuna
  • Labarai
  • Nishadi
  • Noma Da Kiwo
  • Sarauta
  • Shanshani
  • Sharhi
  • Sinadarin Rayuwa
  • Siyasa
  • Ta'aziyya
  • Wasanni

Recent News

Exposing Plans of Fake Hausa Activists & Ba-Zata Mischief Mongers to Cause Confusion and Discord in Northern Nigeria (1)

Exposing Plans of Fake Hausa Activists & Ba-Zata Mischief Mongers to Cause Confusion and Discord in Northern Nigeria (1)

January 21, 2026
My 83rd Birthday and the Kindred Spirit

Cikar Shekaru 83 A Duniya: Ranar Da Na Ga Zumunci Da Fatan Alheri Daga Masoya

January 19, 2026
  • About us
  • Advertise
  • Careers
  • Contact

© 2023 Taskar Gizago - Ilimi da Nishadi

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
  • Sharhi
  • Gumbar Dutse
  • Dausayin Kauna
  • Gizago
  • Sarauta
  • Sinadari
  • Adabi da Nishadi
  • Barkwanci
  • Shanshani
  • Hotuna

© 2023 Taskar Gizago - Ilimi da Nishadi

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
This website uses cookies. By continuing to use this website you are giving consent to cookies being used.