NASIHARMU TA YAU (66)
Mu Kula Da Darussan Rayuwa…
__________
Ya kai MUTUM, ka sani fa RAYUWA ita ke nan. Yau kake nan, gobe kuma sai waninka, ka zama tarihi.
Bisa ga wannan yanayi na rayuwa, ka bar zafafa al’amura. Ka sassauta burinka. Ka ɗauki lamurranka da sauƙi kuma ka mu’amalanci al’umma da sauƙi. Kai ma sai ka samu rayuwa da SAUƘI
___________











