• About us
  • Advertise
  • Careers
  • Contact
Sunday, November 22, 2026
  • Login
Taskar Gizago
Advertisement
  • Gida
  • Labarai
  • Sharhi
  • Gumbar Dutse
  • Dausayin Kauna
  • Gizago
  • Sarauta
  • Sinadari
  • Adabi da Nishadi
  • Barkwanci
  • Shanshani
  • Hotuna
Taskar Gizago
No Result
View All Result
Home Gizago

TSAKANIN GWAMNA RADDA DA IBRAHIM MASARI

Ya Kamata Dattawan Katsina Su Shiga Tsakani

Bashir Yahuza Malumfashi by Bashir Yahuza Malumfashi
November 22, 2026
in Gizago
0
TSAKANIN GWAMNA RADDA DA IBRAHIM MASARI

Tsakanin Gwamna Dikko Da Elder Masari...

4
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterWhatsappEmail a Friend

TSAKANIN GWAMNA RADDA DA IBRAHIM MASARI:

Ya Kamata Dattawan Katsina Su Shiga Tsakani

Related posts

Itaciyar Isa Dika: Bishiya Mai Ɗimbin Tarihi

Itaciyar Isa Dika: Bishiya Mai Ɗimbin Tarihi

September 26, 2026
SUNANTA UMMU-KHULSUM

SUNANTA UMMU-KHULSUM

September 13, 2026

Daga Bashir Yahuza Malumfashi

__________

A matsayinta na jiha mai ɗimbin tarihi, al’adu da manyan mutane da suka taka muhimmiyar rawa wajen ci gabanta, Jihar Katsina tana bukatar zaman lafiya, haɗin kai da fahimtar juna a tsakanin shugabanninta.

Sai dai abin takaici, a yau al’amura sun nuna cewa manyan mutane biyu masu matuƙar tasiri a siyasar jihar, Gwamna Dr. Dikko Umaru Radda da Mai Ba Shugaban Ƙasa Shawara kan Harkokin Siyasa, Alhaji Ibrahim Kabir Masari, sun samu saɓani a tsakaninsu.

Abin da ya fi tayar da hankali shi ne, yadda wannan saɓani yake ƙara ta’azzara, inda muhimman jagororin biyu suke maganganu da sukar juna kafafen watsa labarai, lamarin da ke iya ƙara dagula alaƙar siyasa da zamantakewa a jihar, idan ba a gaggauta shawo kansa ba.

Wannan lamari abin takaici ne, domin duk yadda aka yi, al’ummar Katsina ce za ta iya zama babbar wadda za ta ɗanɗana kuɗarta. Masu azancin magana suna cewa, idan giwaye suna faɗa, ciyayi ne suke shan wahala.

Ma’anar wannan magana ita ce, idan manyan mutane suka shiga rikici, galibi talakawa da waɗanda ba su da hannu a rikicin ne suke fuskantar mummunan sakamako. Saboda haka, bai kamata a bar saɓanin siyasa tsakanin waɗannan manyan shugabanni ya rikiɗe zuwa wata matsala da za ta raba kan al’ummar Katsina ko ta kawo tsaiko ga ayyukan ci gaba ba.

Bambancin ra’ayi a siyasa abu ne da ake iya samu amma bai kamata ya zarce iyakar mutunci, zumunci da maslahar al’umma ba.

Addinin Musulunci ya yi umarni da samar da zaman lafiya da sasanta duk wata husuma tsakanin mutane.

Allah Maɗaukakin Sarki a cikin Alƙur’ani mai girma, Suratul Hujurat, aya ta 10 yana cewa: “Lallai muminai ‘yan uwa ne, saboda haka ku yi sulhu tsakanin ‘yan uwanku, kuma ku ji tsoron Allah, tsammaninku za a yi muku rahama.”

Haka kuma, Manzon Allah (SAW) ya bayyana muhimmancin sasanci a cikin Jami’ut Tirmizi, Hadisi na 2509. Ya ce: “Shin ba zan ba ku labarin abin da ya fi darajar azumi da salla da sadaka ba? Sai suka ce: Haƙiƙa, ya Manzon Allah. Ya ce, sasanta tsakanin masu saɓani.”

Waɗannan nassoshi sun isa su tunatar da mu cewa sasanci da haɗa kan al’umma suna daga cikin manyan ayyukan alheri a Musulunci.

A bisa wannan dalili, ina ganin ya kamata dattawa da manyan masu fafa a ji a Jihar Katsina, su tashi tsaye wajen shiga tsakani domin samar da maslaha tsakanin waɗannan shugabanni biyu.

Ina ganin ya dace a gayyaci shugabannin Ƙungiyar Tuntuɓa Ta Arewa (Arewa Consultative Forum – ACF), reshen Jihar Katsina da Sarakunan Katsina da Daura da manyan Malaman Musulunci da kuma fitattun ‘yan siyasa da dattawan jihar, domin gudanar da tattaunawar sulhu tsakanin masu girma Gwamna Dikko da Elder Masari.

A cikin waɗanda ya kamata a nemi gudunmawarsu, akwai tsohon Gwamnan Jihar Katsina, Alhaji Aminu Bello Masari da Sanata Abu Ibrahim da Alhaji Sani Zangon Daura, tare da sauran dattawa masu kishin jihar.

Waɗannan mutane suna da matsayi, gogewa da kuma mutuncin da za su iya taimakawa wajen samar da mafita cikin hikima da adalci. Bai kamata a ɗauki wannan batu a matsayin rikicin siyasa kawai ba, illa ya kamata a kallace shi a matsayin abin da ya shafi zaman lafiya, haɗin kai da makomar Jihar Katsina.

Haka kuma, ina kira ga masu girma shugabanninmu, Gwamna Dikko Umaru Radda da Alhaji Ibrahim Kabir Masari da su yi la’akari da matsayinsu na shugabanni da kuma irin tasirin da kalamansu da ayyukansu suke da shi a cikin al’umma.

Ya kamata su fahimci cewa, matasa da dama suna kallon yadda suke tafiyar da harkokinsu, suna kuma ɗaukar darasi daga halayensu. Idan manyan mutane suka mayar da bambancin ra’ayi zuwa musayar kalamai da rikici a bainar jama’a, akwai haɗarin matasa su ɗauki hakan a matsayin wata hanya ta magance saɓani.

Maimakon haka, ya kamata su zama abin koyi wajen haƙuri, juriya, mutunta juna da kuma fifita maslahar al’umma a kan muradun kansu.

Su tuna cewa akwai ‘ya’yansu da jikokinsu da kuma dubban matasa da za su yi koyi da su. Don haka ya dace su bar musu kyakkyawan tarihi da darussan da za su amfana da su.

Wani abin da ya kamata waɗannan manyan mutane su riƙa tunawa shi ne, rayuwar duniya mai wucewa ce. Mulki, matsayi, dukiya da tasirin siyasa, duk abubuwa ne da ba su dawwama.

Yau mutum yana kan mulki, gobe wani ne. Yau mutum yana da matsayi, gobe zai iya zama talaka kamar kowa.

Abin da yake dawwama shi ne ayyukan alheri da tarihin da mutum ya bari a bayan rasuwarsa.

Ya kamata masu girma, Gwamna Radda da Alhaji Ibrahim Kabir Masari, cikin ladabi da girmamawa nake roƙon ku, don Allah ku yi tunanin irin tarihin da kuke son a rubuta game da ku.

Shin za a tuna da ku a matsayin mutanen da suka yi amfani da matsayinsu wajen haɗa kan al’umma da samar da ci gaba, ko kuwa za a tuna da ku a matsayin manyan mutane da suka bar saɓani da rarrabuwar kai a tsakaninsu?

Ya masu girma shugabanninmu, wannan tambaya ce da ya kamata kowannenku ya yi wa kansa cikin natsuwa da tsoron Allah.

Daga ƙarshe, wannan kira ba na goyon bayan wani ɓangare ba ne kuma ba wai ina neman a ɗora laifi a kan wani ba ne.

Kira ne na neman zaman lafiya, fahimtar juna da kuma kare martabar Jihar Katsina.

Ina roƙon dattawa, sarakuna, malamai da sauran masu kishin Jihar Katsina, da su ɗauki wannan lamari da muhimmanci. Su yi ƙoƙarin haɗa waɗannan manyan mutane wuri guda, domin a tattauna cikin mutunci da gaskiya. a warware duk wata matsala da ke tsakaninsu.

Haka kuma, ina kira ga masu girma Gwamna Radda da Alhaji Ibrahim Kabir Masari da su kasance masu faɗin ƙirji, wajen ɗaukar matakin sulhu, domin neman afuwar juna.

Masu girma shugabanninmu, na san kun sani, don haka ku tuna da cewa, sasanci ba rauni ko kasawa ba ne. A’a, alama ce ta jarumta, wayewa da kishin al’umma.

Katsina da alummarta sun fi kowane mutum. Haka kuma zaman lafiyarta ya fi kowace rigimar siyasa. Makomar al’ummarta kuma ta fi duk wani buri na ƙashin kai.

Ya Allah ka haɗa kan shugabanninmu. Ka zaunar da jiharmu da ƙasarmu lafiya. Ka kuma ba mu shugabanni masu fifita maslahar jama’a a kan son zuciya. Amin.

__________

Bashir Yahuza Malumfashi, Marubuci, Ɗan Jarida kuma Mawallafi/Babban Editan Mujallar Taskar Gizago (online)

Previous Post

BETWEEN GOVERNOR RADDA AND IBRAHIM MASARI

Related Posts

Itaciyar Isa Dika: Bishiya Mai Ɗimbin Tarihi
Gizago

Itaciyar Isa Dika: Bishiya Mai Ɗimbin Tarihi

September 26, 2026
SUNANTA UMMU-KHULSUM
Gizago

SUNANTA UMMU-KHULSUM

September 13, 2026
HUJJA MAGANIN HAYANIYA – 1
Gizago

HUJJA MAGANIN HAYANIYA – 1

September 12, 2026

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

RECOMMENDED NEWS

Fusatattun Matasa Sun Yi Wa Mataimakin Gwamnan Zamfara Rajamu

Fusatattun Matasa Sun Yi Wa Mataimakin Gwamnan Zamfara Rajamu

October 19, 2026
Malumfashi An Yi Babban Rashi

Malumfashi An Yi Babban Rashi

May 11, 2026
The Bloomsbury Handbook of Muslims and Popular Culture: An Endorsement

The Bloomsbury Handbook of Muslims and Popular Culture: An Endorsement

October 19, 2023
SATAR AZZAKARI: Gaskiya Ko Ruɗanin Tunani?

SATAR AZZAKARI: Gaskiya Ko Ruɗanin Tunani?

October 16, 2023

FOLLOW US

BROWSE BY CATEGORIES

  • Adabi
  • Addini
  • Babban Labari
  • Barkwanci
  • Dausayin Kauna
  • ENGLISH
  • Gizago
  • Gumbar Dutse
  • Hotuna
  • Labarai
  • Nishadi
  • Noma Da Kiwo
  • Sarauta
  • Shanshani
  • Sharhi
  • Sinadarin Rayuwa
  • Siyasa
  • Ta'aziyya
  • Wasanni

POPULAR NEWS

  • Gwamnan Katsina Ya Ƙi Amsar Kyautar Raguna 100 Daga Hannun Attajiri

    Gwamnan Katsina Ya Ƙi Amsar Kyautar Raguna 100 Daga Hannun Attajiri

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • Ta Tsinci Naira Miliyan 60 A Saudiyya Ta Miƙa Wa Hukuma

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • LUWAƊI DA YARA 14: Yadda Aka Bankaɗo Asirin Kabir Ɗan Hisba

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • Sojojin Najeriya Sun Kama Makashin Sarkin Gobir

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • Tarihin Waƙar Yaƙin Tabuka

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
Taskar Gizago

Follow us on social media:

Recent News

  • TSAKANIN GWAMNA RADDA DA IBRAHIM MASARI
  • BETWEEN GOVERNOR RADDA AND IBRAHIM MASARI
  • NASIHARMU TA YAU (60)

Category

  • Adabi
  • Addini
  • Babban Labari
  • Barkwanci
  • Dausayin Kauna
  • ENGLISH
  • Gizago
  • Gumbar Dutse
  • Hotuna
  • Labarai
  • Nishadi
  • Noma Da Kiwo
  • Sarauta
  • Shanshani
  • Sharhi
  • Sinadarin Rayuwa
  • Siyasa
  • Ta'aziyya
  • Wasanni

Recent News

TSAKANIN GWAMNA RADDA DA IBRAHIM MASARI

TSAKANIN GWAMNA RADDA DA IBRAHIM MASARI

November 22, 2026
BETWEEN GOVERNOR RADDA AND IBRAHIM MASARI

BETWEEN GOVERNOR RADDA AND IBRAHIM MASARI

November 22, 2026
  • About us
  • Advertise
  • Careers
  • Contact

© 2023 Taskar Gizago - Ilimi da Nishadi

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
  • Sharhi
  • Gumbar Dutse
  • Dausayin Kauna
  • Gizago
  • Sarauta
  • Sinadari
  • Adabi da Nishadi
  • Barkwanci
  • Shanshani
  • Hotuna

© 2023 Taskar Gizago - Ilimi da Nishadi

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
This website uses cookies. By continuing to use this website you are giving consent to cookies being used.