Gwamna Radda Ya Naɗa Ɗan Malumfashi Muƙamin Babban Sakatare
__________
Gwamnan Jihar Katsina, Malam Dikko Umaru Radda, ya amince da naɗin gogaggen ɗan jarida kuma masani a harkokin gudanar da kafafen yaɗa labarai, Abdul’aziz Salisu, a matsayin Babban Sakatare (Permanent Secretary).
Kamar yadda jaridar intanet, The Syndicate ta ruwaito, wannan naɗi na Malam Abdul’aziz Salisu, wanda ɗan asalin Ƙaramar Hukumar Malamumfashi ne, yana daga cikin sabbin naɗe-naɗen manyan jami’an gwamnati guda uku da gwamnatin jihar ta yi, kamar yadda wata sanarwa da Ofishin Shugaban Ma’aikatan Gwamnati ya fitar ta bayyana.
Kafin wannan naɗi, Abdul’aziz Salisu ya riƙe muƙamin Babban Manajan Rikon Ƙwarya na Gidan Talabijin na Jihar Katsina (KTTV), inda kuma ya taɓa riƙe muƙamin Daraktan Labarai da Al’amuran Yau Da Kullum.
Abdul’aziz Salisu ƙwararren ɗan jarida ne ƙwararre kuma gogagge a fannin watsa shirye-shirye, gudanar da harkokin labarai da shugabancin kafafen yaɗa labarai. Ya bayar da gagarumar gudummawa wajen bunƙasa aikin jarida da yaɗa bayanai ga al’umma a Jihar Katsina.
Sauran waɗanda aka naɗa su ne Sulaiman Adamu Gachi, daga Ƙaramar Hukumar Kankia da Muhammad Usman, daga Ƙaramar Hukumar Daura.
Muƙaddashin Shugaban Ma’aikatan Gwamnatin Jihar Katsina, Malam Mas’ud Mustapha Banye, ya bayyana cewa an gudanar da naɗe-naɗen ne bisa kyakkyawan fata da amincewar cewa waɗanda aka naɗa, za su nuna ƙwazo, jajircewa, sadaukarwa da ƙwarewa wajen sauke nauyin da aka ɗora musu, domin amfanin ma’aikatan Gwamnatin Jihar Katsina baki ɗaya.
Ya taya sabbin Manyan Sakatarorin Gwamnati murna, tare da yi musu fatan samun nasara da kuma fatan Allah ya ba su jagoranci da taimako a sabbin muƙaman da suka samu.
Ana kallon naɗin Abdul’aziz Salisu a matsayin wata alama ta karrama shi bisa tsawon shekarun hidimarsa, ƙwarewarsa ta fuskar aiki da kuma irin gudunmawar da ya bayar wajen bunƙasa harkokin kafafen yaɗa labarai a Jihar Katsina.
__________












