NASIHARMU TA YAU (15)

__________
A yau mun samu nasiha ce daga FASIHIN KAITA, MALAM ISHAƘA DANKAMA, wanda ya ce:
Kowane mutum da ke rayuwa a duniya, ba ka da mutum ɗaya da zai tabbatar ma cewa shi yana da yaƙinin rayuwarsa za ta kai gobe. Kuma idan har ta kai, yaya rayuwarsa za ta kasance? Idan har wata lalura ta same shi kafin goben ko goben yana da yaƙinin mutum ɗaya da zai taimake shi, lokacin da yake buƙatar taimako na tsakani da Allah zuwa ƙarshen lalurar? Ruwa cikin kofin shayi ya isa wanka ga mai hankali. Ya isa duk mutum mai hankali, ya yi ƙoƙarin zama lafiya da kowa.
__________












