NASIHARMU TA YAU (02)
Daga Bashir Yahuza Malumfashi

__________
Ya ɗan uwa, a yau take JUMA’A, babbar rana mai ɗauke da ɗimbin albarkoki. Mu yawaita salati da sallama ga Fiyayyen Talikai, Manzon Allah Muhammadu – Sallallahu Alaihi Wasallam! Mu karanta Suratul Kahfi. Mu yi sadaka da sada zumunta kuma mu halarci Sallar Juma’a, tare da addu’ar neman dacewa da wannan muhimmin lokaci mai albarka da ke cikin wannan rana. Ya ALLAH ka yi albarka ga rayuwarmu. Ka ƙara mana lafiya da yalwar arziki.
__________













