• About us
  • Advertise
  • Careers
  • Contact
Monday, September 21, 2026
  • Login
Taskar Gizago
Advertisement
  • Gida
  • Labarai
  • Sharhi
  • Gumbar Dutse
  • Dausayin Kauna
  • Gizago
  • Sarauta
  • Sinadari
  • Adabi da Nishadi
  • Barkwanci
  • Shanshani
  • Hotuna
Taskar Gizago
No Result
View All Result
Home Gizago

Tsakanin Maza Da Mata Wa Ya Fi Yawa A Duniya?

NAZARI/BINCIKE

Bashir Yahuza Malumfashi by Bashir Yahuza Malumfashi
August 13, 2026
in Gizago
0
Tsakanin Maza Da Mata Wa Ya Fi Yawa A Duniya?

Tsakanin Maza Da Mata: Wa Ya Fi Yawa A Duniya?

12
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterWhatsappEmail a Friend

Tsakanin Maza Da Mata Wa Ya Fi Yawa A Duniya?

Daga Bashir Yahuza Malumfashi

Related posts

SUNANTA UMMU-KHULSUM

SUNANTA UMMU-KHULSUM

September 13, 2026
HUJJA MAGANIN HAYANIYA – 1

HUJJA MAGANIN HAYANIYA – 1

September 12, 2026
Tsakanin Maza Da Mata: Wa Ya Fi Yawa A Duniya?


__________
Wani saƙo da ke yaɗuwa a kafafen sada zumunta ya yi ikirarin cewa maza sun yi ƙaranci matuƙa a duniya, tare da danganta wasu alkaluman ban mamaki da Majalisar Ɗinkin Duniya (UN). Saƙon ya yi ikirarin cewa daga cikin mutane biliyan 7.8 da ke duniya, mata sun kai biliyan 5.6, yayin da maza suka kai biliyan 2.2. Saƙon ya kuma ce idan aka ware mazajen da suka yi aure da waɗanda ke gidan yari da marasa lafiya da wasu rukunai, maza kusan biliyan ɗaya ne kawai suka rage, waɗanda za su iya yin aure. Sai dai binciken sahihan bayanan Majalisar Ɗinkin Duniya, ya nuna cewa waɗannan alkaluma ba daga Majalisar Ɗinkin Duniya suke ba kuma rahoton ba shi da inganci.

A cewar rahoton Majalisar Ɗinkin Duniya mai suna World Population Prospects 2024, yawan al’ummar duniya ya kai kusan biliyan 8.2 a shekarar 2024, ba biliyan 7.8 ba kamar yadda saƙon ya bayyana. Alkaluman Majalisar Ɗinkin Duniya sun kuma nuna cewa yawan al’ummar duniya a shekarar 2025 ya kai kusan biliyan 8.2. Mafi muhimmanci kuma, duniya ba ta ƙunshi mata biliyan 5.6 da maza biliyan 2.2 ba. Bayanai na Majalisar Ɗinkin Duniya sun nuna cewa yawan maza da mata a duniya ya kusan yin kunnen doki, sai dai maza suna da ɗan ƙaramin rinjaye a kan mata.

A shekarar 2025, adadin maza a kan mata a duniya ya kai kusan maza 101 ga kowace mata 100. Wannan yana nufin cewa a matakin duniya baki ɗaya, maza ma sun ɗan fi mata yawa.

Wannan bayanin shi kaɗai ya isa ya ƙaryata ɗaya daga cikin manyan iƙirarin saƙon da ake yaɗawa. Ba maza biliyan 2.2 ba ne duniya ke da su, sannan ba mata biliyan 5.6 ba ne. A shekarar 2025, an ƙiyasta cewa maza a duniya sun kai kusan biliyan 4.1, yayin da mata su ma suka kai kusan biliyan 4.1. Bambancin da ke tsakanin adadin maza da mata a duniya bai da yawa. Sai dai yanayin ya bambanta daga ƙasa zuwa ƙasa da kuma daga rukuni na shekaru zuwa wani.

Wasu ƙasashe suna da maza fiye da mata, yayin da wasu ke da mata fiye da maza. Haka kuma, yayin da shekaru suke ƙaruwa, mata sukan fi yawa saboda a matsakaicin bincike, mata sun fi tsawon rai fiye da maza. Saboda haka, ba daidai ba ne a ɗauki alƙaluman duniya gaba ɗaya a yi amfani da su wajen bayyana yanayin aure a wata ƙasa ko al’umma.

A wannan saƙon da aka riƙa yaɗawa, an yi iƙirarin cewa Majalisar Ɗinkin Duniya ta shawarci mata da su yi taka-tsan-tsan wajen mu’amalarsu da maza saboda wai maza sun yi ƙaranci. Babu wata sahihiyar hujja da ke nuna cewa Majalisar Ɗinkin Duniya ta bayar da irin wannan shawara. Rahoton Majalisar Ɗinkin Duniya game da yawan al’ummar duniya, ya fi mayar da hankali ne kan batutuwan ƙididdigar al’umma, kamar ƙaruwa ko raguwa da yawan jama’a da haihuwa da mace-mace, da ƙaura da tsufa da tsarin karkasuwar jama’a bisa shekaru da jinsi. Ba rahoton neman abokin aure ba ne kuma ba ya ba mata umarni da su girmama maza saboda wai maza biliyan ɗaya ne kawai suka rage da za su iya yin aure. Saboda haka, salon da aka rubuta saƙon yana nuna cewa wataƙila an ƙirƙire shi ne domin ya yaɗu a kafafen sada zumunta, sannan aka jingina shi ga Majalisar Ɗinkin Duniya, domin a ba shi ƙarin nauyi da amincewa.

Sauran alƙaluman da saƙon ya kawo, su ma ba su da ingantacciyar shaida. Saƙon ya ce daga cikin maza biliyan 2.2, an samu biliyan ɗaya da suka yi aure, miliyan 130 da ke gidan yari da miliyan 70 da ke fama da matsalolin lafiyar ƙwaƙwalwa ko wasu cututtuka, sannan ya ci gaba da cire wasu rukunai kamar marasa aikin yi, masu bambancin sha’awar jima’i, limaman Katolika, ’yan uwa ko iyaye da tsofaffi. Babu wata hujja da ke nuna cewa waɗannan alƙaluma sun fito daga wani rahoton Majalisar Ɗinkin Duniya.

Bugu da ƙari, tsarin lissafin kansa ba daidai yake ba. Mutum guda zai iya kasancewa cikin rukuni fiye da ɗaya. Misali, mutum zai iya kasancewa mai aure kuma ba shi da aikin yi ko kuma ya kasance uba kuma ya haura shekaru 65. Saboda haka, cire waɗannan rukunan daga jimillar maza ba zai iya samar da sahihin adadin mazan da ake kira “waɗanda za su iya yin aure” ba.
Wannan al’amari ya nuna yadda ake iya haɗa ɗan ƙaramin bayani na gaskiya da wasu bayanan ƙarya, sannan a samar da saƙo mai jan hankali a kafafen sada zumunta. Gaskiya ne cewa akwai bambance-bambancen adadin maza da mata a sassa daban-daban na duniya. Gaskiya ne kuma cewa wasu ƙasashe suna da gagarumin rashin daidaiton adadin maza da mata, musamman a wasu rukunin shekaru. Amma wannan ba yana nufin cewa akwai ƙarancin maza a duk faɗin duniya ba.

A matakin duniya, bayanan Majalisar Ɗinkin Duniya suna nuna ɗan ƙaramin rinjayen maza, yayin da mata suke ƙara yawa musamman a cikin rukunin tsofaffi. Fahimtar irin waɗannan sauye-sauyen na buƙatar ingantaccen nazarin ƙididdigar al’umma, ba wai yin lissafin gaugawa ta hanyar haɗa rukuni-rukuni daban-daban ba.

Saboda haka, abin da ya dace shi ne a ce kada a ɗauki wannan saƙo a matsayin rahoton ko shawarar Majalisar Ɗinkin Duniya. Iƙirarin cewa “maza sun yi ƙaranci a duniya” bai samu goyon bayan alƙaluman yawan jama’a na Majalisar Ɗinkin Duniya ba. Haka kuma, alƙaluman da aka kawo game da mazajen da suka yi aure, fursunoni, masu matsalar lafiyar ƙwaƙwalwa, marasa aikin yi, limaman Katolika da tsofaffi, ba su samar da ingantaccen lissafin adadin mazan da suke “samuwa don aure.”

Tabbas, ya kamata maza da mata su girmama juna, su kyautata wa juna, su mutunta mutuncin juna, kuma su yi mu’amala cikin adalci da tausayi. Amma ba sai an yi amfani da alƙaluman ƙarya ba wajen tabbatar da wannan muhimmiyar ƙa’ida. A wannan zamani da saƙo zai iya yawo cikin duniya cikin ’yan daƙiƙu, ya zama wajibi kowa ya koyi tantance sahihancin bayanai kafin ya yaɗa su.

Don haka, wannan saƙon da aka riƙa yaɗawa kuma aka kira shi da “Rahoton Majalisar Ɗinkin Duniya,” rubutu ne mai jan hankali a kafafen sada zumunta amma bai kamata a ɗauke shi a matsayin sahihin binciken ƙididdigar al’umma na Majalisar Ɗinkin Duniya ba.
__________

Previous Post

No, There Is No Global Shortage of Men: Fact-Checking the Viral #UN Claim

Next Post

Gwamnati Za Ta Samar Da Ingantaccen Tsarin Gudanar Da Makarantun Alƙu’rani A Jihar Katsina

Related Posts

SUNANTA UMMU-KHULSUM
Gizago

SUNANTA UMMU-KHULSUM

September 13, 2026
HUJJA MAGANIN HAYANIYA – 1
Gizago

HUJJA MAGANIN HAYANIYA – 1

September 12, 2026
Ayyukan Alheri Daga Gidan Amana
Gizago

Ayyukan Alheri Daga Gidan Amana

September 5, 2026
Next Post
Gwamnati Za Ta Samar Da Ingantaccen Tsarin Gudanar Da Makarantun Alƙu’rani A Jihar Katsina

Gwamnati Za Ta Samar Da Ingantaccen Tsarin Gudanar Da Makarantun Alƙu'rani A Jihar Katsina

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

RECOMMENDED NEWS

RAMADAN KARIM: 15-1447

RAMADAN KARIM: 15-1447

March 4, 2026
LAMENTATION FOR MAIDUGURI

LAMENTATION FOR MAIDUGURI

September 10, 2024
The Federal Capital Territory Abuja: The Past, Present and the Future

Babban Birnin Tarayya Abuja: Jiya Da Yau Da Gobe

September 19, 2023
Janar Faruk Yahaya Ya Zama Zaruman Sakkwato

Janar Faruk Yahaya Ya Zama Zaruman Sakkwato

August 15, 2023

FOLLOW US

BROWSE BY CATEGORIES

  • Adabi
  • Addini
  • Babban Labari
  • Barkwanci
  • Dausayin Kauna
  • ENGLISH
  • Gizago
  • Gumbar Dutse
  • Hotuna
  • Labarai
  • Nishadi
  • Noma Da Kiwo
  • Sarauta
  • Shanshani
  • Sharhi
  • Sinadarin Rayuwa
  • Siyasa
  • Ta'aziyya
  • Wasanni

POPULAR NEWS

  • Gwamnan Katsina Ya Ƙi Amsar Kyautar Raguna 100 Daga Hannun Attajiri

    Gwamnan Katsina Ya Ƙi Amsar Kyautar Raguna 100 Daga Hannun Attajiri

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • Ta Tsinci Naira Miliyan 60 A Saudiyya Ta Miƙa Wa Hukuma

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • LUWAƊI DA YARA 14: Yadda Aka Bankaɗo Asirin Kabir Ɗan Hisba

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • Sojojin Najeriya Sun Kama Makashin Sarkin Gobir

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • Tarihin Waƙar Yaƙin Tabuka

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
Taskar Gizago

Follow us on social media:

Recent News

  • Zan Iya Yafe Wa Gwamna Abba – In Ji Kwankwaso
  • JAGORA: Leader of the Masses
  • MALAM SULE LAMIDO: Jagoran Talakawa Ya Cika Shekaru 78

Category

  • Adabi
  • Addini
  • Babban Labari
  • Barkwanci
  • Dausayin Kauna
  • ENGLISH
  • Gizago
  • Gumbar Dutse
  • Hotuna
  • Labarai
  • Nishadi
  • Noma Da Kiwo
  • Sarauta
  • Shanshani
  • Sharhi
  • Sinadarin Rayuwa
  • Siyasa
  • Ta'aziyya
  • Wasanni

Recent News

Zan Iya Yafe Wa Gwamna Abba – In Ji Kwankwaso

Zan Iya Yafe Wa Gwamna Abba – In Ji Kwankwaso

September 20, 2026
JAGORA: Leader of the Masses

JAGORA: Leader of the Masses

September 17, 2026
  • About us
  • Advertise
  • Careers
  • Contact

© 2023 Taskar Gizago - Ilimi da Nishadi

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
  • Sharhi
  • Gumbar Dutse
  • Dausayin Kauna
  • Gizago
  • Sarauta
  • Sinadari
  • Adabi da Nishadi
  • Barkwanci
  • Shanshani
  • Hotuna

© 2023 Taskar Gizago - Ilimi da Nishadi

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
This website uses cookies. By continuing to use this website you are giving consent to cookies being used.