Tsakure Daga Littafin Fitilar Matasa (1)
__________

• Tarihin jajirtaccen matashi, wanda ya yarda da kansa kuma al’umma suka yarda da shi.
• Labarin haziƙin matashi, wanda ya yarda da gwagwarmayar rayuwa. Matashin da ya taso a matsayin talaka amma mai zuciyar nema.
• Labarin matashin da ya yarda da cewa ILIMI shi ne hanyar ci gaba.
• Labarin Matashin da ya yi amanna da cewa HIDIMAR AL’UMMA ita ce ginshiƙin nasarar rayuwa.
• Labarin matashin da ya haska wa matasa hanyoyin dogaro da kai da sadaukarwa.
√ Muna maganar Dokta, Injiniya Tukur Tingilin, FNSE, Manajan Daraktan Hukumar Ruwa ta Jihar Katsina.
Idan Allah ya kai mu gobe Litinin 06-09-1447 (Hijiriyya), 23-02-2026 (Miladiyya), in sha Allahu za mu fara tsakuro maku wannan littafi a Mujallar Taskar Gizago (online):
www.taskargizago.com.ng
Da kuma wannan shafi nawa na Facebook.
__________
ALLAH SA MU DACE, AMIN!













