Sharhi Kan Littafin Tarihin Philip Chikwuedo Asiodu
Daga Dr. Bukar Usman

__________
Sunan Littafi: Philip Chikwuedo Asiodu, CFR, CON, HLR. Kamfanin Wallafa: Mahogany Limited, 2025. Marubuciya: Patricia Otuedon-Arawore. Manazarci: Dr. Bukar Usman, OON. Yawan Shafuka: 584. Farashi: Ba a bayyana ba
__________
Gabatarwa:
An yi bikin cikar shekaru 91 na fitaccen tsohon babban jami’in gwamnati a Najeriya, Philip Chikwuedo Asiodu (Izoma na Asaba), a Legas ranar 3 ga Disamba, 2025, inda aka ƙawata taron da gabatar da wani littafi da Gidauniyar Hallmarks of Labour Foundation (HLF) ta wallafa, domin girmama shi.
Littafin mai taken Philip Chikwuedo Asiodu, CFR, CON, HLR Patricia Otuedon-Arawore ce ta rubuta shi, wadda ita ma gogaggiya ce a harkar watsa labarai kuma ita ce ta kafa wannan gidauniya a 1996, domin cin ma manufar wallafa jerin littattafai game da fitattun mutane masu yi wa al’umma hidima.
An gabatar da littafin a shahararren ɗakin taro na Metropolitan Club da ke Victoria Island, Legas. Kodayake ban samu halartar taron ba, na samu kwafin littafin a Abuja ta hannun Dr. Adegoke Adegoroye, tsohon Babban Sakatare a Gwamnatin Tarayya, wanda shi ne ya yi bitar littafin a yayin taron.
Dr. Adegoroye ya yi bita mai zurfi kuma mai gamsarwa. Duk da haka, na ji a raina cewa wajibi ne ni ma in yi nazari da sharhi kan littafin, ba wai kawai domin girmama tsohon ubangidana a Ma’aikatar Ma’adinai da Wutar Lantarki a 1971 ba, har ma domin haɗa kai wajen yabon kyawawan halayensa da nagartaccen jagorancin da ya bayar ga hidimar al’ummar Najeriya gaba ɗaya. Na yi imani cewa, saboda matsayin Izoma Asiodu mai girma, yin bitar littafi a kansa ba zai zama wuce gona da iri ba. Ya kamata a yaɗa labarin ƙwarewarsa da iliminsa da sadaukarwar da ya ba ƙasarmu da bil’adama baki ɗaya a tsawon shekaru 91 na rayuwarsa.
Littafin mai shafuka 584 ya ƙunshi jawabai da tsokaci guda 35 da Asiodu ya rubuta ko ya gabatar daga 1997 zuwa 2022, tsawon shekaru 25. Jawabai guda 14 ya gabatar da su ne a Abuja, guda takwas a Legas, biyu a Asaba, garinsu. Sai jawabi ɗaya da ya gabatar a Ibadan da wasu a garuruwan daban-daban. A 2017 ya fi gabatar da jawabai fiye da kowace shekara, inda ya gabatar da jawabai guda huɗu.
Kodayake ba a jera jawaban nasa bisa tsarin lokaci ba, akwai manyan jigogi da ake iya ganewa a ko’ina cikin littafin. Dukkansu sun mayar da hankali ne kan kyakkyawan shugabanci, hanyoyin bunƙasa ƙasa da inganta walwalar al’umma, tare da buƙatar Najeriya ta ci gaba da riƙe matsayi mai daraja a idon duniya.
Mai Martaba Dr. Yakubu Gowon, tsohon Shugaban Ƙasa kuma shugaban taron, shi ne ya rubuta gabatarwar littafin. A ciki ya bayyana Izoma Asiodu a matsayin “ɗaya daga cikin mutanen da ƙaddara ta yi amfani da su wajen tsara gudanar tarihin Najeriya.” Ya kuma bayyana cewa bayan Yaƙin Basasa, ƙasar ta buƙaci jagoranci mai inganci da hidimar ma’aikata masu gaskiya. Ya ce Philip Asiodu, wanda aka kira “Super Permanent Secretary” (Babban Sakatare Mai Abin Al’ajabi), ya kasance daga cikin manyan ginshiƙan da suka taimaka wajen tsara manufofin gwamnatinsa. (Shafi vi-vii).
Walwalar Jama’a:
Asiodu ya yi jimami sau da yawa cewa duk da yalwar albarkatun ɗan Adam da na ƙasa da Allah Ya bai wa Najeriya, ya kamata ta fi inda take a yau, wajen walwalar jama’a da mutuncinta a duniya. Ya tuno cewa a lokacin samun ’yancin kai, Najeriya ta fara da manyan buri amma ƙasashen da suka yi zamani da ita kamar Hong Kong, Singapore, Koriya ta Kudu, Taiwan, Brazil, India da Malaysia, a yau sun sha gabanta, nesa ba kusa ba. Ya tuno yadda a can baya, Najeriya ta samu damar shiga rukunin Majalisar Ɗinkin Duniya, yadda aka ware rana guda aka yi ta shagulgula, yadda Najeriya ta riƙa ƙarfafa samar da ‘yancin kai ga wasu ƙasashe, da ma yadda ta taimaka wajen kafa ƙungiyoyin bunƙasa ƙasashe.
Ya bayyana cewa abin kunya ne yadda Najeriya ba ta iya sarrafa matatun manta (oil refineries) yadda ya kamata tsawon shekaru, har ta dogara da shigo da mafi yawan tataccen man fetur daga waje. Ya danganta hakan da cin hanci da tsoma bakin ‘yan siyasa a harkokin NNPC. Har ma yarjejeniyar 1993 da kamfanonin mai na duniya guda uku, don su ɗauki gudanar da karatun, aka kasa aiwatar da ita (shafuka 154–155).
Ya yi kira ga ’yan Najeriya da su yi nazari a kan kansu tare da ɗaukar matakan gyara cikin gaggawa.
Tunanin Siyasa:
Asiodu ya yi imanin cewa ba tsarin siyasa ne matsala ba, illa yadda shugabanni ke tafiyar da shi. Ya ce abin da jami’an gwamnati ke ganin za su iya tserewa da shi ne ke ƙayyade yadda ake kashe kuɗi, ko da tsarin Shugaban Ƙasa (Presidential) ne ko na Firaminista (Parliamentary) (shafi 441).
Ya kwatanta Najeriya da Amurka ta fuskar yawan ma’aikatun gwamnati da bambancin albashi tsakanin ma’aikata da ’yan siyasa. Ya ce a yayin da Amurka take da Sassan Ma’aikatu 12 a Gwamnatin Tarayya da Sassa 6 a matakin jihohi, Najeriya tana da Sassan Ma’aikata masu tarin yawa a matakan Gwamnatin Tarayya da na jihohi. Ya kuma bayyana cewa albashin ‘yan siyasa ya yi yawa da tazara mai girma bisa ga albashin ma’aikatan gwamnati a Najeriya; wanda ba haka abin yake ba a Amurka. Ya danganta hakan da raunin jamiyyun siyasa da rashin hangen nesa na shugabanni.
Ya ɗora laifukan matsalolin Najeriya ga gazawar ‘yan siyasa, waɗanda ba su zurfafa tunani wajen tafiyar da al’amura. Haka kuma akwai ƙarancin ‘yan siyasa masu kishin ƙasa da hangen nesa a Najeriya. Ya ce jam’iyyun siyasa ba su da ingantattun manufofi (manifesto) da tsare-tsare da za su ciyar da ƙasar gaba. Ba su wallafa ingantattun manufofin da za su yi masu jagora wajen samar da mulki mai inganci ga al’umma. Babu abin da suka sanya a gaba sai son zuciya da neman biya wa kansu bukatun ƙashin kansu. Sai kuma haɗama da azurta kansu, maimakon shata hanyoyin bunƙasa jin daɗin al’umma. Sai dai kuma duk da haka, ya bayyana cewa akwai wasu tsirarun jihohi da suka samar wa al’ummarsu cigaba. (Shafi 251).
A ganinsa, Najeriya na iya samar da ingantaccen tsari da manufa ta ƙasa, wadda za ta haɗa kowa, kamar yadda Majalisar Ɗinkin Duniya ta shata. Abin da talaka ke so shi ne tsaro, matsuguni, abinci, ilimi, wutar lantarki, lafiya da sufuri. Kyakkyawan shugabanci ne, ba fafutukar mulki ba, zai haifar da haɗin kai da ci gaban ƙasa (shafuka 34–35).
Tattalin Arziki:
Asiodu ya nuna damuwa kan yadda Najeriya ke dogaro da ɓangare ɗaya na tattalin arziki, wato man fetur, duk da ƙoƙarin bunƙasa wasu sassa. Ya danganta hakan da raunin tsare-tsaren ƙasa da rashin ƙarfafawa wajen aiwatarwa. Haka kuma ya koka da yadda gwamnatoci ba su ɗorawa kan aikin da suka gada daga magabatansu. Ya ce hatta tsare-tsaren bunƙasa ƙasa (national development plan) na 1975–1980, an kauce daga aiwatar da shi. Ya ce wannan ne ya haddasa aka riƙa banzatar da ayyukan da aka faro ko aka tsara, ba tare da an kammala su ba. Ya ba da misali da aikin samar da layin dogo na zamani a birnin Legas, wanda Gwamnatin Lateef Jakande (1979-1983) ta shirya gudanarwa.
An ce halin ya ƙara taɓarɓarewa ne bayan sallaman ma’aikata da gwamnatin Murtala ta yi a shekarar 1975 da Tsarin Aikin Gwamnati (Civil Service Reform) a shekarar 1988. Lamarin ya kara haifar da mummunar rushewar ɗabi’a da ƙwarin gwiwa, watsi da tsarin bincike da tantance ayyuka da lalacewar ɗa’a da tsare-tsaren gudanarwa, tare da bunƙasar neman riba ta haramtacciyar hanya da tsananin ƙaruwar cin hanci da rashawa a tsakanin shugabannin ma’aikatun gwamnati da hukumomi da sauran jami’ai (shafi na 324).
Ya tunatar da cewa gwamnatoci daban-daban na baya sun hau mulki, ko aka tilasta musu hawan mulki, ba tare da cikakkiyar fahimtar abin da suke son yi da ikon da suka samu ba. Kamar yadda ya bayyana, rikicewar manufofi, yawan katse ko dakatar da tsare-tsare da shirye-shirye, da rashin kishin ƙasa sun zama alamar yadda ake tafiyar da mulki a Najeriya, wanda hakan ya haifar da rashin ci gaba wajen bunƙasa tattalin arziki domin fitar da ƙasarmu mai yalwar albarkatu daga ƙangin talauci (shafi na 455).
Asiodu, wanda ya kasance muhimmin jigo kuma sanannen da yake cikin harkokin gwamnati a wancan lokaci, ya jaddada cewa da a ce bayan cire Janar Gowon daga mulki a shekarar 1975, waɗanda suka gaje shi sun ci gaba da aiwatar da Tsarin Bunƙasa Ƙasa na Uku (1975–1980) cikin tsari da tsattsauran bin ƙa’ida, kuma da a ce a ƙarƙashin tsare-tsaren ci gaban ƙasa na gaba an kiyaye matsakaicin ƙimar bunƙasar tattalin arziki ta sama da kashi 10% a duk shekara na tsawon shekaru masu zuwa, da Najeriya ta riga ta kuɓuta daga talauci da koma-baya, kuma a yau da ta zama “Damisar Afirka” mai kama da “Damisar Asiya” (shafi na 500).
Ya yi kira da zuciya ɗaya ga a koma ga tsare-tsare da cikakken shirin aiwatarwa cikin tsari da ɗa’a na manufofin da aka tsara, tare da inganta su ta hanyar fifita lamurran cigaban ƙasa. A gudanar da tsare-tsaren da aka riga aka tantance cikin gaskiya da bayyana gaskiya (shafi na 470).
Hidimar Jama’a da Aikin Gwamnati:
An ce kakanninmu, a lokacin taron samar da Kundin Tsarin Mulki da aka gudanar a Landan a shekarar 1954, wanda ya gabaci samun ’yancin kan Najeriya, sun ɗauki alƙawarin tabbatar da samuwar Hidimar Jama’a mai zaman kanta kuma marar siyasa. Sun bayyana goyon bayansu da wannan kyakkyawan tsari kamar haka: “Mun ba da cikakken goyon bayanmu ga ƙa’idar da ke cewa dukkan al’amuran hidimar jama’a, ciki har da naɗe-naɗe, ƙarin girma, tura jami’ai wuraren aiki, kora daga aiki, da sauran al’amuran ladabtarwa, ya kamata a kiyaye su gaba ɗaya cikin ’yanci kuma ba tare da wani tasirin siyasa ba. Muna fatan za a ci gaba da riƙe tsohon tsarin ƙarin girma bisa cancanta, gogewa da ƙwazo, ba tare da la’akari da ƙabila ko launin fata ba.” (Shafi na 111).
Da yake duba al’amura cikin hangen nesa bisa ga tarihi da kuma kwatantawa, Asiodu ya ce tsarin aikin gwamnati da ake amfani da shi a Najeriya, an fara samar da shi cikin nasara ne tun da farko ta hannun Turawan Mulkin Mallakar Birtaniya a Indiya, wata babbar ƙasa mai yalwar bambance-bambancen al’umma kamar Najeriya. Daga nan ne aka fitar da shi zuwa ƙasar uwar gijiya, wato Birtaniya, a tsakiyar ƙarni na 19, sannan daga baya aka yaɗa shi zuwa wasu ƙasashe kamar Ostiraliya. Asiodu ya jaddada cewa babu wani dalili da zai sa wannan tsarin da yake ci gaba da yi wa sauran ƙasashe hidima yadda ya kamata har zuwa yau, ba zai yi aiki a Najeriya ba, musamman ganin cewa shugabanninmu na farko, tun kafin samun ‘yancin kai da kuma bayan samun ‘yancin kan, sun yi alƙawarin gaskiya, na tsayawa kan wannan tsari kuma haƙiƙa sun tabbatar da kiyayewa da aiwatar da shi.
Asiodu ya ba da shawara cewa, domin rage illolin da tsarkakewar ma’aikata gaba ɗaya (purge) ta shekarun 1975/1976 da kuma abin da aka kira “gyara” (reform) na shekarar 1988 suka haifar, akwai buƙatar sake motsa gwiwar Ma’aikatan Gwamnati, ta hanyar ba shugabancinta matsayi mai dacewa, tare da ba su damar daidaitawa da tsara shawarwarin manufofi. Haka kuma, ya zama dole a dawo da cikakkun tattaunawa da shawarwari tsakanin ma’aikatun gwamnati, domin a tabbatar da cewa manufofin gwamnati sun zama masu daidaito da jituwa, tare da tabbatar da saurin aiwatar da manufofin da aka amince da su. Gwamnati kuma ya kamata ta guji kafa tsarukan ma’aikata na daban-daban masu tsada, waɗanda galibi ba su da ƙwarewa sosai, yadda ake ɗaukar tarin Mataimaka na Musamman (shafi na 451–452).
Shigar “Harkokin Siyasa” cikin harkar “Harkokin Aikin Gwamnati” musamman, ta haifar da sakaci da rashin kulawa a harkar tafiyar da kuɗaɗen gwamnati da kuma naɗe-naɗen muƙamai a ofisoshin gwamnati ba tare da tsari mai kyau ba, abin da har yanzu tasirinsa yake nan. Wasu ma sun yi jayayya cewa lalacewar Aikin Gwamnati ya faro ne tun da daɗewa, tun lokacin da Yaƙin Basasar Najeriya ya ɓarke, inda wasu ƙwararru kuma gogaggun ma’aikatan gwamnati suka yi gaggawar ficewa zuwa Biyafara. Kodayake daga baya wasu sun dawo kuma aka sake karɓar su cikin aiki, abubuwa ba su ƙara zama yadda suke a da ba.
A ƙari ga haka, akwai gadon da mulkin soja ya bari na ɗaukar matakan ladabtarwa cikin gaggawa da hukunci kai tsaye, galibi ana aiwatar da su “nan take” ba tare da bin ƙa’idojin shari’a da aka daɗe ana bi wajen mu’amala da ma’aikatan gwamnati da suka aikata laifi ba. Wannan ya kawo barazana ga tabbacin zaman aiki na ma’aikatan gwamnati.
Harkokin Ƙasashen Waje:
Asiodu ya nuna cewa a farko Najeriya ta dogara ne da ƙwararrun jami’an diflomasiyya amma daga baya, shigar ’yan siyasa marasa ƙwarewa cikin tsarin da kuma taɓarɓarewar tattalin arzikin ƙasa ya rage martabar ƙasar. Irin yadda aka tafiyar da al’amarin Yaƙin Basasa da ƙwarewa, ya ƙara tabbatar da juriyar tattalin arziƙin Najeriya da kuma tsarin gudanarwar difilomasiyya. Ya ba da shawarar cewa kada fiye da kashi 20% na manyan muƙamai su kasance ga waɗanda ba ƙwararrun jami’an diflomasiyya ba (shafi 105).
Tarihin Rayuwa Da Halayensa:
An haifi Izoma Philip Chikwuedo Asiodu, CFR, CON, a birnin Legas a shekarar 1934. Iyayensa ‘yan asalin Asaba ne a Jihar Delta ta yau a Najeriya. Ya samu ilimi a makarantar Sacred Heart School, Calabar (1939–1942); Hope Waddell Training Institute, Calabar (1943); St. Paul’s School, Ebute-Metta, Legas; King’s College, Legas (1946); sannan ya tafi Jami’ar Oxford a Ingila inda ya kammala karatu da digirin B.A. (Honors) a fannin Siyasa, Falsafa da Tattalin Arziƙi (Politics, Philosophy and Economics – PPE) a shekarar 1956.
Ba da daɗewa ba, bayan kammala karatunsa, Asiodu ya fara aikinsa na hidimar jama’a a Ma’aikatar Harkokin Ƙasashen Wajen Najeriya, a shekarar 1957, a matsayin ƙaramin jami’i da muƙamin Mataimakin Sakatare, abin da ya sanya shi cikin sahun farko na ginshiƙan Ma’aikatar Harkokin Ƙasashen Wajen Najeriya bayan samun ‘yancin kai. Ya yi aiki na ɗan lokaci a Ofishin Jakadancin Najeriya a London (1958). Sannan aka tura shi a matsayin jami’in haɗin gwiwa zuwa ofisoshin Jakadancin Birtaniya a Ostiraliya da New Zealand (1959). Ya yi aiki a ofishin Jakadancin Najeriya a New York (1960), sannan kuma a Sakatariyar Ƙungiyar Haɗin Kan Afirka (OAU) a Addis Ababa (1963).
Daga baya ya koma aiki a Ma’aikatar Al’amuran Cikin Gida, inda aka naɗa shi matsayin Babban Sakatare, muƙamin da ya riƙe na tsawon shekaru 11 (1964–1975). A wannan matsayi, an tura shi zuwa ma’aikatu da dama na gwamnati, kafin daga bisani Gwamnatin Soja ta Janar Murtala Mohammed ta yi masa ritaya da wuri a shekarar 1975, yana kusan shekaru 42 a duniya.
A cewar Mista Allison Ayida, tsohon Sakataren Gwamnatin Tarayya kuma Shugaban Ma’aikatan Gwamnati, wanda kuma abokin aiki ne ga Asiodu, wanda ya nace wajen sanin dalilin da ya sa aka yi wa Manyan Sakatarori ritaya. Ya ce Janar Mohammed ya gaya wa Asiodu cewa an yi masa ritayar ne kawai domin nuna cewa gwamnati na da ikon ɗaukar mataki kan kowane ma’aikaci, komai ƙarfinsa ko matsayinsa. Kamar yadda Ayida ya faɗa, Janar Murtala Mohammed ya ce wa Asiodu:
“Kai, Philip, mun san tarihin aikinka, muna matuƙar girmama ka. Wannan gwamnati tana son ta ci gaba da amfani da aikinka amma a matsayinta na gwamnati mai ƙuduri, mun tsara mu nuna wa kowa misali cewa babu wanda yake da ƙarfin da ba za a iya sauke shi ba. Don haka muna son mu yi amfani da kai a matsayin misali” (shafi na 533).
Wannan, a fili yana nuna irin girman tasiri da ƙarfin iko da ake ɗora wa Ma’aikatan Gwamnati da kuma Manyan Sakatarori, a wancan lokaci. Bayan ritayarsa daga aiki, Asiodu ya yi aiki a fannoni daban-daban a matsayin mai ba da shawara da kuma Minista. A bayyane yake cewa, sakamakon takaici, ya ƙi karɓar muƙamin Minista a ƙarƙashin Gwamnatin Janar Sani Abacha. Sai dai daga baya ya tsayar da kansa a matsayin ɗan takarar Shugaban Ƙasa, mai yiyuwa bisa imanin cewa idan ya zama Shugaban Ƙasa, zai iya nuna jagoranci ta hanyar misali, tare da amfani da manyan albarkatu da baiwar da Najeriya take da su domin ci gaba, bunƙasa ƙasa da walwalar al’ummarta.
Shawarwarin Samar Da Cigaba:
Da yake ya samu damar yin aiki a ɓangarorin Harkokin Ƙasashen Waje da na cikin gida, Najeriya, dattijo mai daraja Izoma Asiodu yana da cikakken hangen nesa na musamman kan abin da ake buƙata, domin ciyar da Najeriya gaba. Saboda haka ya bayar da shawarwari masu yawa, daga cikinsu (ban da waɗanda aka riga aka ambata a wannan bitar) akwai:
• A magance bambanci da rashin daidaito tsakanin kuɗaɗen manyan ayyuka (capital expenditure) da na kashe-kashen yau da kullum (recurrent expenditure), ta yadda za a fifita na manyan ayyuka.
• A magance ƙarancin samar da wutar lantarki da makamashi gaba ɗaya.
• A cike babban giɓi da ke tsakanin albashin ‘yan majalisa da sauran masu riƙe da muƙaman siyasa, idan aka kwatanta da mafi ƙanƙantar albashin ma’aikata a ƙasar.
• A dawo da daraja tare da mutunta ginshiƙan ƙa’idojin Aikin Gwamnati, kamar gaskiya, riƙon amana, bayyana komai a buɗe cikin gaskiya, jarumtaka, kishin ƙasa da sha’awar yi wa jama’a hidima.
• A bunƙasa masana’antu, ta hanyar ba da fifiko ga aikin noma na zamani da masana’antun da suka danganci noma da kuma ayyukan da ke ƙara kawo cigaba, a ɓangaren man fetur da iskar gas, domin kasuwar cikin gida da kuma fitarwa zuwa ƙasashen waje.
• Ya kamata a samar da manufofin harshe da za su ƙarfafa haɗin kan ƙasa, inda kowane yaro zai zama wajibi ya koyi karatu da rubutu a harshen yankin da aka haife shi kuma ya fara makaranta a cikinsa, sannan daga baya ya zaɓi ɗaya daga cikin manyan harsuna uku na Najeriya.
• A ɗauki matakai domin ƙarfafa ‘yancin kai na ɓangaren shari’a, tare da samar masa da fasahar zamani domin hanzarta aiwatar da adalci.
A matsayinsa na Babban Sakatare, Asiodu mutum ne mai fasahar ƙirƙire-ƙirƙire sosai amma duk da haka yana bai wa ƙananan jami’ai dama su gabatar da shawarwarin manufofi, abin da ke taimaka musu wajen bunƙasa ƙwarewarsu. A matsayina na matashin jami’in gudanarwa da ke aiki ƙarƙashinsa a Ma’aikatar Ma’adinai da Wutar Lantarki (Ministry of Mines and Power) a shekarar 1971, an ɗora mini alhakin rubuta takardar tunatarwa zuwa Majalisar Ministoci dangane da rikice-rikicen da ke yawan faruwa tsakanin Hukumar Wutar Lantarki ta Najeriya (Electricity Corporation of Nigeria – ECN), wadda Mista Hsu, ɗan Taiwan yake shugabanta a matsayin Babban Manaja, da Hukumar Dam ta Neja (Niger Dams Authority – NDA) ƙarƙashin Injiniya Yahaya Dikko. Rikicin ya shafi batun samar da wutar lantarki da kuma rashin biyan kuɗaɗe daga ECN, wanda hakan ke kawo cikas ga wutar lantarki a duk faɗin ƙasar. A ƙarshe dai sakamakon wannan rikici shi ne haɗa hukumomin biyu wuri guda domin kafa Hukumar Wutar Lantarki ta Ƙasa (National Electric Power Authority – NEPA), wadda daga baya ta zama Power Holding Company of Nigeria (PHCN), ita kuma ce ta haifi kamfanonin da ake da su a yanzu da ke kula da samar da wuta (GENCOs), rarrabawa (DISCOs) da kuma isarwa (TCN).
Ya dace a yaba wa ƙirƙira da basirar Izoma Asiodu. Ya yi aiki a Ma’aikatar Masana’antu (Ministry of Industry) kafin daga bisani aka tura shi Ma’aikatar Ma’adinai da Wutar Lantarki. A lokacin da yake riƙe da muƙamai a waɗannan ma’aikatun biyu ne Najeriya, a matsayinta na ƙasa mai fitar da mai, ta shiga Ƙungiyar Ƙasashen da ke Fitar da Man Fetur wato Organization for Petroleum Exporting Countries (OPEC), sannan aka kafa Hukumar Man Fetur ta Ƙasa ta Najeriya (Nigerian National Oil Corporation).
Dangantakar Ƙashin Kaina Da Shi:
A ƙashin kaina, ina amfani da wannan dama domin sake nuna matuƙar godiyata ga Izoma Asiodu, bisa yadda ya ba da lokacinsa ya karanta rubutun littafina mai shafuka 456, mai taken My Public Service Journey: Issues in Public Policy Administration in Nigeria (Klamidas: 2019). Shi ne ya rubuta Gabatarwa (Foreword) inda ya ba da shawarar littafin a matsayin ingantaccen jagora ga duk mai sha’awar nazarin tarihin bunƙasar Aikin Gwamnati a Najeriya kuma ya lura, a cikin wasu abubuwa, cewa: “babbar manufar duk waɗannan kayan aikin, ita ce warware matsalolin jama’a cikin inganci, tasiri, da adalci ga kowa” (shafi na 19).
Baya ga haka, Izoma Asiodu ya tallafa wa gidauniyata, The Dr. Bukar Usman Foundation, ta fuskar kuɗi kuma ya ƙarfafa ayyukana na adabi. Haka kuma, uwargidansa mai daraja, Jumoke Asiodu, tana da kyakkyawar alaƙa ta kusa da uwargidana ta farko, marigayiya Mrs. Adekemi Usman (née Badejo), inda suka kasance da alaƙar uwa da ‘ya kamar ta jini, mai cike da kauna da tausayi.
Kammalawa:
Izoma Asiodu, bisa ga gogewarsa ta rayuwa, ya yi kira ga ma’aikatan gwamnati da na jama’a da su yi aiki da gaskiya da riƙon amana, yana jaddada cewa akwai lada a cikin gaskiya a hidimar jama’a. Ya ce muddin Allah ya ba ka tsawon rai, za ka tarar cewa bayan ka bar aiki, har ma mutane da ba ka san ka taimaka musu ba, ko waɗanda ba ka san sun amfana da ayyukanka ba, za su riƙa gayyatarka zuwa abubuwa daban-daban; haka kuma kamfanoni da gwamnatoci masu tsayayyen tsari kan samar wa tsofaffin ma’aikatan gwamnati ayyuka bayan ritaya, a hukumomin gwamnati da kuma a wasu fannoni daban-daban (shafi na 431).
Ya kuma jaddada muhimmancin sake sauya tunani da halayya gaba ɗaya daga ɗabi’un shugabanni da masu ruwa da tsaki, dangane da bunƙasar ƙasa ta fuskar siyasa, zamantakewa, tattalin arziƙi da ci gaban ƙasa baki ɗaya.
____________
Dr. Bukar Usman, OON, tsohon Babban Sakatare ne a Fadar Shugaban Ƙasa kuma a halin yanzu shi ne Shugaban Ƙungiyar Bunkasa Al’adun Gargajiya Najeriya (Nigerian Folklore Society).













