• About us
  • Advertise
  • Careers
  • Contact
Thursday, April 16, 2026
  • Login
Taskar Gizago
Advertisement
  • Gida
  • Labarai
  • Sharhi
  • Gumbar Dutse
  • Dausayin Kauna
  • Gizago
  • Sarauta
  • Sinadari
  • Adabi da Nishadi
  • Barkwanci
  • Shanshani
  • Hotuna
Taskar Gizago
No Result
View All Result
Home Gizago

Yunkurin ‘Yan Ba-Zata/Hausawan Bogi Na Haddasa Ruɗani A Arewa (8)

TSOKACI

Bashir Yahuza Malumfashi by Bashir Yahuza Malumfashi
January 13, 2026
in Gizago
0
Yunkurin ‘Yan Ba-Zata/Hausawan Bogi Na Haddasa Ruɗani A Arewa (8)

Jihadin Mujaddadi Shehu Ɗanfodiyo alheri ne ga al'ummar Musulmi

24
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterWhatsappEmail a Friend

Yunkurin ‘Yan Ba-Zata/Hausawan Bogi Na Haddasa Ruɗani A Arewa (8)

Daga Bashir Yahuza Malumfashi

Related posts

Malam Nasir El-Rufa’i Da Ƙalubalen Rayuwa

Malam Nasir El-Rufa’i Da Ƙalubalen Rayuwa

April 16, 2026
JOS! JOS!! JOS: Muhimmin Saƙo Zuwa Ga Musulmi Da Kirista

JOS! JOS!! JOS: Muhimmin Saƙo Zuwa Ga Musulmi Da Kirista

April 3, 2026

                     __________

Jihadin Mujaddadi Shehu Ɗanfodiyo alheri ne ga al’ummar Musulmi

Shin Jihadin Ɗanfodiyo Taimakon Musulmi Ya Yi Ko Cutar Da Su?

A ci gaba da wannan tsokaci, a yau za mu duba amsar wannan tambaya ta sama, cewa shin Jihadin Mujaddadi Shehu Usman Ɗanfodiyo (RTA), taimakon al’ummar Musulmi ya yi, ko kuwa cutar su ya yi?

Babban dalilin da ya sanya muka kawo wannan tambaya shi ne, saboda ganin yadda ‘ya’yan Ƙungiyar Hausawan Bogi, ‘yan Ba-Zata suke ta faɗi tashin jirkita tarihi kuma suke ta haƙilon su a dole sai sun ɓata shi, sun lalata ɗimbin alheran da ya haifar wa al’ummomin da ke Afirka ta Yamma da ma duniya baki ɗaya.

Kodayake ba za mu yi mamaki ba, domin kuwa ƙudurinsu shi ne, su shuka fitina da gaba tsakanin al’ummar Arewa gaba ɗaya. Ba za su kuwa iya yin haka ba, sai sun lalata tarihi, sannan za su iya haifar da shakku a zukatan al’umma. Idan ba haka ba, yaushe a wannan ƙarni na 21, wani zai yi burin komawa gidan jahilci irin na kishin ƙabilanci da maguzanci?

Game da tambayarmu dangane da alheran Mujaddadi Ɗanfodiyo kuwa, kafin mu kai ga amsarmu, muna kira ga al’umma cewa, duk mai neman sahihin labari ko tarihinsa da ayyukansa na ƙwarai, to ya binciki tarihi sahihi daga littattafan tarihi na gaskiya, waɗanda suka yi ƙoƙari waje fito da ingantattun bayanan abin ci gaba da Mujaddadi ya kawo, musamman ma dai yadda ya kafa ingantattar daula, wacce ta tsarkake al’umma.

Misali, akwai littafin Murry Last, mai taken “The Sokoto Caliphate,” wanda kamfanin wallafa na Humanities Press ya wallafa a shekarar 1967. Akwai kuma littafin da Paul E. Lovejoy ya rubuta, mai taken “Jihad in West Africa  the Age of Revolutions,” wanda kamfanin Ohio University Press ya wallafa a shekarar 2016.

Haka kuma, ga duk mai neman gaskiya game da Mujaddadi, to ya nemi littafin “Usman Danfodio: The Great Mujaddid and Reformer,” wanda Ibrahim Sulaiman ya rubuta kuma kamfanin Hudahuda Publishing ya wallafa a shekarar 1987. Akwai kuma littafi mai taken “Shehu Usman Danfodio: His Life, Teachings and Influence,” wanda shi ma Ibrahim Sulaiman ya rubuta kuma kamfanin Islamic Publications Bureau ya wallafa.

Dukkan waɗannan littattafai suna ƙunshe da sahihan tarihin Mujaddadi Ɗanfodiyo da ayyukansa. Wani abin mamaki ma, wasu marubutan, kamar Paul E. Lovejoy, ba Musulmi ne ba; wanda haka ke nuna cewa abin da suka binciko na tarihi, gaskiya ne kuma sahihai.

A waɗannan littattafai da ma wasu irinsu masu tarin yawa da ba mu ambata ba a nan ba, sun nuna cewa babu shakka Sheikh Usman Ɗanfodiyo mutumin kirki ne, malamin addinin Musulunci ne na ƙwarai, wanda ya jaddada Musulunci kuma ya yaɗa koyarwarsa a Afrika ta Yamma. Mujaddadi ne da ya kafa daular Musulunci mai kyakkyawan tsari da adalci. Tsarin da hatta sai da Turawan Yamma suka kwaikwaya kuma suka amfana da shi.

Haka kuma shaida ta tabbatar da tsarkin zuciyar Ɗanfodiyo, dangane da jihadinsa, cewa don Allah ne da manzonsa ya gudanar da shi, ba don kwaɗayin mulki ko dukiya ba. Shehu ya ƙaddamar da jihadinsa a shekarar 1804, inda ya zuwa 1808, ya cinye manyan garuruwan Hausawa na Kano, Katsina, Zariya da sauransu, inda ya kafa hamshaƙiyar Daular Sakkwato bisa Shari’ar Musulunci.

Haka kuma, bayan wannan nasara, Shehu bai zama sarki a daular ba, domin kuwa ɗansa Muhammadu Bello da ɗan uwansa Abdullahin Gwandu ne ya naɗa, suka ci gaba da mulki a daular. Shi kuwa sai ya ci gaba da ayyukansa na karantarwa da ilimantarwa, har zuwa ƙarshen rayuwarsa, a shekarar 1817.

Jama’a masu bibiyar muƙalar nan da haƙuri, yau ma a nan za mu tsaya. Sai mun sake haɗuwa a kashi na 9, inda za mu zayyano wasu daga cikin muhimman taimako da gudunmowar da Mujaddadi Shehu Ɗanfodiyo ya ba al’ummar Musulmi, waɗanda har zuwa yau kuma har duniya ta ƙare, za su ci gaba da amfana da su.

_______________

Previous Post

A Review of Philip Chikwuedo Asiodu: A Legacy of Dedication and Service

Next Post

My 83rd Birthday and the Kindred Spirit

Related Posts

Malam Nasir El-Rufa’i Da Ƙalubalen Rayuwa
Gizago

Malam Nasir El-Rufa’i Da Ƙalubalen Rayuwa

April 16, 2026
JOS! JOS!! JOS: Muhimmin Saƙo Zuwa Ga Musulmi Da Kirista
Gizago

JOS! JOS!! JOS: Muhimmin Saƙo Zuwa Ga Musulmi Da Kirista

April 3, 2026
Najeriya 2027: Matsalolin Da Za Su Iya Wargaza Takarar Obi Da Kwankwaso
Gizago

Najeriya 2027: Matsalolin Da Za Su Iya Wargaza Takarar Obi Da Kwankwaso

March 29, 2026
Next Post
My 83rd Birthday and the Kindred Spirit

My 83rd Birthday and the Kindred Spirit

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

RECOMMENDED NEWS

Nasihar Juma’a

Nasihar Juma’a

April 10, 2026
Tattaunawar Aminu Waziri Da Baturen Ingila

Tattaunawar Aminu Waziri Da Baturen Ingila

December 15, 2024
Neman Hanyar Gaskiya A Addini

Neman Hanyar Gaskiya A Addini

October 17, 2025
AREWA (A Poem)

AREWA (A Poem)

August 19, 2024

FOLLOW US

BROWSE BY CATEGORIES

  • Adabi
  • Addini
  • Babban Labari
  • Barkwanci
  • Dausayin Kauna
  • ENGLISH
  • Gizago
  • Gumbar Dutse
  • Hotuna
  • Labarai
  • Nishadi
  • Noma Da Kiwo
  • Sarauta
  • Shanshani
  • Sharhi
  • Sinadarin Rayuwa
  • Siyasa
  • Ta'aziyya
  • Wasanni

POPULAR NEWS

  • Gwamnan Katsina Ya Ƙi Amsar Kyautar Raguna 100 Daga Hannun Attajiri

    Gwamnan Katsina Ya Ƙi Amsar Kyautar Raguna 100 Daga Hannun Attajiri

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • Ta Tsinci Naira Miliyan 60 A Saudiyya Ta Miƙa Wa Hukuma

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • LUWAƊI DA YARA 14: Yadda Aka Bankaɗo Asirin Kabir Ɗan Hisba

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • Sojojin Najeriya Sun Kama Makashin Sarkin Gobir

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • BINCIKE: Zahirin Abin Da Ke Faruwa A BBC Hausa

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
Taskar Gizago

Follow us on social media:

Recent News

  • Malam Nasir El-Rufa’i Da Ƙalubalen Rayuwa
  • Fasto Ɗan Ƙungiyar Hausawan Bogi Da Ya Zagi Annabi Ya Ɓoye
  • Ɓatanci Ga Manzon Allah: Musulmi Sun Buƙaci Gwamnati Ta Hukunta Fasto Emmanuel Garba?

Category

  • Adabi
  • Addini
  • Babban Labari
  • Barkwanci
  • Dausayin Kauna
  • ENGLISH
  • Gizago
  • Gumbar Dutse
  • Hotuna
  • Labarai
  • Nishadi
  • Noma Da Kiwo
  • Sarauta
  • Shanshani
  • Sharhi
  • Sinadarin Rayuwa
  • Siyasa
  • Ta'aziyya
  • Wasanni

Recent News

Malam Nasir El-Rufa’i Da Ƙalubalen Rayuwa

Malam Nasir El-Rufa’i Da Ƙalubalen Rayuwa

April 16, 2026
Ɓatanci Ga Manzon Allah: Musulmi Sun Buƙaci Gwamnati Ta Hukunta Fasto Emmanuel Garba?

Fasto Ɗan Ƙungiyar Hausawan Bogi Da Ya Zagi Annabi Ya Ɓoye

April 15, 2026
  • About us
  • Advertise
  • Careers
  • Contact

© 2023 Taskar Gizago - Ilimi da Nishadi

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
  • Sharhi
  • Gumbar Dutse
  • Dausayin Kauna
  • Gizago
  • Sarauta
  • Sinadari
  • Adabi da Nishadi
  • Barkwanci
  • Shanshani
  • Hotuna

© 2023 Taskar Gizago - Ilimi da Nishadi

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
This website uses cookies. By continuing to use this website you are giving consent to cookies being used.