• About us
  • Advertise
  • Careers
  • Contact
Thursday, April 16, 2026
  • Login
Taskar Gizago
Advertisement
  • Gida
  • Labarai
  • Sharhi
  • Gumbar Dutse
  • Dausayin Kauna
  • Gizago
  • Sarauta
  • Sinadari
  • Adabi da Nishadi
  • Barkwanci
  • Shanshani
  • Hotuna
Taskar Gizago
No Result
View All Result
Home Siyasa

Nasarar Shari’ar Zaɓe: Ya Kamata Mu Mara Wa Shugaba Tinubu Baya – Janar Buratai

Anas Saminu Ja'en by Anas Saminu Ja'en
September 11, 2023
in Siyasa
0
Nasarar Shari’ar Zaɓe: Ya Kamata Mu Mara Wa Shugaba Tinubu Baya – Janar Buratai
32
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterWhatsappEmail a Friend

Nasarar Shari’ar Zaɓe: Ya Kamata Mu Mara Wa Shugaba Tinubu Baya – Janar Buratai

Daga Anas Saminu Ja’en

Related posts

Najeriya 2027: Yadda ADC Za Ta Murƙushe APC

Najeriya 2027: Yadda ADC Za Ta Murƙushe APC

April 9, 2026
2027: SABUWAR GUGUWAR SAUYIN SIYASA A KANO

2027: SABUWAR GUGUWAR SAUYIN SIYASA A KANO

February 24, 2026

Mai girma Ambasada Laftanar-Janar Tukur Yusufu Buratai (Mai Ritaya), Betaran Biu kuma Garkuwan Keffi, tsohon Babban Hafsan Hafsoshin Sojojin Najeriya kuma tsohon Jakadan Najeriya a Jamhuriyar Benin, ya bayyana cewa nasarar da Shugaban Ƙasa Bola Ahmad Tinubu ya samu a kotun sauraren shari’ar zaɓe ginshiƙi ce ta tabbatar da dimokuraɗiyya a Najeriya.

Janar Buratai tare da Shugaba Tinubu

Haka kuma Janar Buratai ya buƙaci al’ummar ƙasa da a haɗa hannu a taimaka masa domin samun nasarar gudanar da mulki mai amfani ga ƙasa. Ya kuma bayyana abubuwa biyar dangane da Shugaban Ƙasa Bola Ahmad Tinubu, inda yake cewa:

1- A ranar 6 ga watan Satumba, 2023 ce kotu ta yanke hukunci da tabbatar da nasarar Bola Ahmad Tinubu GCFR. Ina taya shi murna bisa samun wannan nasara. Kuma wannan hukunci ya tabbatar da adalci da kuma tabbatuwar dimokuraɗiyya. Ya kamata dukkanin ɗan Najeriya ya jajirce wajan ganin wanzuwar dimokuraɗiyya a kan dukkanin aikin da yake kai, domin ciyar da ƙasa gaba. Sai mun haɗa kai za mu samar da kyakkyawar al’umma ta yadda muryar kowanne daga cikinmu za ta zama mai muhimmanci. Ku zo mu haɗa kai a ƙarƙashin inuwar dimokuraɗiyya, domin mu samar da rayuwa mai aminci a gaba.

2. Dimokuraɗiyya ita ce ta bayar da damar da kowa zai iya tsayawa zaɓe a kowace jam’iyya. Amma ya kamata mu sani da zarar an ce wane ne ya yi nasara to Shugaban Ƙasa zai kasance guda ɗaya ne. Saboda haka abu ne mai matuƙar muhimmanci ga duk ɗan ƙasa ba tare da nuna bambancin jam’iyya ba, ya zo a haɗa kai wajan goya wa Shugaban Ƙasa Bola Ahmad Tinubu baya. Domin ta haka ne za a ciyar da ƙasa gaba. Ta hanyar haɗin kai ne kaɗai za mu iya samar da ingantacciyar gwamnati. Kuma ta wannan hanyar ce kaɗai za mu iya samar da ci gaba da kuma ƙarfafa kyawawan tsare-tsare da za su amfanar da dukkanin al’ummar ƙasa.

3. Abu ne mai matuƙar muhimmanci gare mu, mu ilimantu da cewar ci gaban ƙasarmu shi ne muhimmi kuma samun nasarar jam’iyya wadda za ta taimaki al’umma tare da tabbatar da ɗorewar dimokuraɗiyya da kuma kawo ci gaba wajan haɗin kai. Ku zo mu mayar da hankali a kan abu mai muhimmanci da sa kai wajen tattauna al’amuran da za su kawo ci gaba.

4. Bugu da ƙari, kowane ɓangare na al’ummarmu yana da gudummawar da zai bayar wajan kawo ci gaban zaman lafiya, tsaro da sauran abubuwan da suka shafi ci gaban ƙasa. Jihohi da ƙananan hukumomi, shugabanninsu suna da mutuƙar muhimmanci saboda irin kusancin su da al’umma. Ya kamata su fi kawo ingantattun tsare-tsare da ayyukan da za su tabbatar da doka da oda da harkokin tattalin arziƙi, ta hanyar tabbatar da adalci, aiki tuƙuru ne na Gwamnatin Tarayya da jihohi da ƙananan hukumomi za a iya biyan buƙatun al’umma tare da bijiro da hanyoyin samar da abun yi ga mutane. Bugu da ƙari, kawo ingantattun tsare-tsare shi ne yake bayar da nasara wajan ci gaban ƙasa da sanya ido wajen ganin kowane ɗan ƙasa ya amfana da sababbin ci gaba da ake shigo da su da samar da damarmakin da za su haɓaka tare da ginuwar ƙasar. Kuma jihohi da ƙananan hukumomi dole ne su ɗauki duk nauyin da yake kansu da sauke su ta hanyoyi masu inganci domin su ne ƙashin bayan samar da ci gaban ƙasa.

5. Abu ne mai matuƙar amfani ga dukkanin ‘yan Najeriya, musamman matasa da sauran ƙungiyoyi da su goya wa gwamnati baya, wadda Shugaban Ƙasa Bola Ahmad Tinubu yake jagoranta, ta yadda ya ɗauki alƙawarin cewa zai zama mai kulawa da cika alƙawarin da ya ɗauka. Duk da cewa ana fuskantar ƙalubale iri-iri Shugaban Ƙasa ya ƙudiri aniyar fito da hanyoyi wajen samar da al’amura cikin sauƙi da kuma jagoranci nagari. A matsayinsa na shugaban da aka yadda da shi, ya sadaukar da kansa wajen kawo wa ƙasa ci gaba ta hanyar da kowa zai yi farin ciki. Shugaba Tinubu yana da kyakkyawar manufa da za ta kawo ci gaba da kawo canjin zai amfani ‘yan Najeriya. Saboda haka ne dukkaninmu ‘yan Najeriya mu taimaka wa shugabancinsa, domin samun nasara ciyar da ƙasarmu gaba.

Previous Post

RAHMA ABDULMAJID: Marubutan Hausa Sun Samu Wakilci A Gwamnatin Tinubu

Next Post

UAE Lifts Ban On Nigerian Travellers

Related Posts

Najeriya 2027: Yadda ADC Za Ta Murƙushe APC
Siyasa

Najeriya 2027: Yadda ADC Za Ta Murƙushe APC

April 9, 2026
2027: SABUWAR GUGUWAR SAUYIN SIYASA A KANO
Siyasa

2027: SABUWAR GUGUWAR SAUYIN SIYASA A KANO

February 24, 2026
Komawar Kwankwaso Zuwa APC: Gaba Kura Baya Sayaki
Siyasa

Abubuwan Da Za Su Iya Faruwa Idan Kwankwaso Ya Koma APC

September 28, 2025
Next Post
UAE Lifts Ban On Nigerian Travellers

UAE Lifts Ban On Nigerian Travellers

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

RECOMMENDED NEWS

2027 and the Rise of a Third Force: Can ADC’s Political Heavyweights Unseat Tinubu?

2027 and the Rise of a Third Force: Can ADC’s Political Heavyweights Unseat Tinubu?

July 2, 2025
Yadda Ƙungiyar NAL Ta Karrama Dokta Bukar Usman A Legas

Yadda Ƙungiyar NAL Ta Karrama Dokta Bukar Usman A Legas

August 18, 2024
Batun Jami’a A Malumfashi: Ƙarin Bayani Daga Abdullahi Ibrahim Mahuta

Batun Jami’a A Malumfashi: Ƙarin Bayani Daga Abdullahi Ibrahim Mahuta

July 8, 2023
Taron editoci: Tinubu na so a riƙa yaɗa kyawawan labarai don jawo zuba jari a Nijeriya

Ministan Yaɗa Labarai Ya Kafa Kwamitin Wayar Da Kan Al’umma, Cusa Ɗa’a, Kishin Ƙasa Da Kyawawan Ɗabi’u

December 7, 2023

FOLLOW US

BROWSE BY CATEGORIES

  • Adabi
  • Addini
  • Babban Labari
  • Barkwanci
  • Dausayin Kauna
  • ENGLISH
  • Gizago
  • Gumbar Dutse
  • Hotuna
  • Labarai
  • Nishadi
  • Noma Da Kiwo
  • Sarauta
  • Shanshani
  • Sharhi
  • Sinadarin Rayuwa
  • Siyasa
  • Ta'aziyya
  • Wasanni

POPULAR NEWS

  • Gwamnan Katsina Ya Ƙi Amsar Kyautar Raguna 100 Daga Hannun Attajiri

    Gwamnan Katsina Ya Ƙi Amsar Kyautar Raguna 100 Daga Hannun Attajiri

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • Ta Tsinci Naira Miliyan 60 A Saudiyya Ta Miƙa Wa Hukuma

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • LUWAƊI DA YARA 14: Yadda Aka Bankaɗo Asirin Kabir Ɗan Hisba

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • Sojojin Najeriya Sun Kama Makashin Sarkin Gobir

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • BINCIKE: Zahirin Abin Da Ke Faruwa A BBC Hausa

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
Taskar Gizago

Follow us on social media:

Recent News

  • Malam Nasir El-Rufa’i Da Ƙalubalen Rayuwa
  • Fasto Ɗan Ƙungiyar Hausawan Bogi Da Ya Zagi Annabi Ya Ɓoye
  • Ɓatanci Ga Manzon Allah: Musulmi Sun Buƙaci Gwamnati Ta Hukunta Fasto Emmanuel Garba?

Category

  • Adabi
  • Addini
  • Babban Labari
  • Barkwanci
  • Dausayin Kauna
  • ENGLISH
  • Gizago
  • Gumbar Dutse
  • Hotuna
  • Labarai
  • Nishadi
  • Noma Da Kiwo
  • Sarauta
  • Shanshani
  • Sharhi
  • Sinadarin Rayuwa
  • Siyasa
  • Ta'aziyya
  • Wasanni

Recent News

Malam Nasir El-Rufa’i Da Ƙalubalen Rayuwa

Malam Nasir El-Rufa’i Da Ƙalubalen Rayuwa

April 16, 2026
Ɓatanci Ga Manzon Allah: Musulmi Sun Buƙaci Gwamnati Ta Hukunta Fasto Emmanuel Garba?

Fasto Ɗan Ƙungiyar Hausawan Bogi Da Ya Zagi Annabi Ya Ɓoye

April 15, 2026
  • About us
  • Advertise
  • Careers
  • Contact

© 2023 Taskar Gizago - Ilimi da Nishadi

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
  • Sharhi
  • Gumbar Dutse
  • Dausayin Kauna
  • Gizago
  • Sarauta
  • Sinadari
  • Adabi da Nishadi
  • Barkwanci
  • Shanshani
  • Hotuna

© 2023 Taskar Gizago - Ilimi da Nishadi

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
This website uses cookies. By continuing to use this website you are giving consent to cookies being used.