NASIHARMU TA YAU (31)
MU TAUSAYA WA IYAYENMU

__________
Naila Aliyu Bunza ta ce: “Har na kai zuwa jami’a, duk lokacin da babana zai yi mani sayayya sai ya kira ni na faɗi irin abin da nake so; kafin ya siya.
Ikon Allah! Ba na son madara ta sachet, sai ta gwangwani. Kifin gwangwani kuwa, sadin kaɗai nake so. Indomi a lokacin, ba na cin cherry, na farkon fitowa kaɗai nake ci. Abubuwa da yawa dai.
Duk wannan hidima da baba yake mani, ashe wai bashi ne nake ɗauka mai nauyi, ban sani ba. Ashe za mu haifi yara mu ji yadda iyayenmu suka ji, ko ma fiye da yadda suka ji da mu.
Yanzu tausayin iyayena nake ji matuƙa. Ba na ma so su ji cewa ba na da wani abu, bare na faɗi zaɓi na.
Allah ka saka wa iyayenmu da alheri, amin.
__________











