• About us
  • Advertise
  • Careers
  • Contact
Wednesday, April 15, 2026
  • Login
Taskar Gizago
Advertisement
  • Gida
  • Labarai
  • Sharhi
  • Gumbar Dutse
  • Dausayin Kauna
  • Gizago
  • Sarauta
  • Sinadari
  • Adabi da Nishadi
  • Barkwanci
  • Shanshani
  • Hotuna
Taskar Gizago
No Result
View All Result
Home Labarai

Kasafin 2024 Ya Fifita Jaddada Ajandar Sassaita Nijeriya – Idris

Daga Wakilinmu by Daga Wakilinmu
December 4, 2023
in Labarai
0
Kasafin 2024 Ya Fitfita Jaddada Ajandar Sassaita Nijeriya – Idris

Ministan Yaɗa Labarai, Alhaji Mohammed Idris, yana gabatar da jawabi a taron

12
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterWhatsappEmail a Friend

Kasafin 2024 Ya Fifita Jaddada Ajandar Sassaita Nijeriya – Idris

Ministan Yaɗa Labarai da Wayar Da Kai, Alhaji Mohammed Idris, ya ce Kasafin Kuɗi na shekarar 2024 ya nuna lallai an fara taka tsanin samun nasarorin ƙudirorin sake bunƙasa ƙasa a ƙarƙashin Ajandar Saisaita Nijeriya ta Shugaba Bola Ahmed Tinubu.

Related posts

Ɓatanci Ga Manzon Allah: Musulmi Sun Buƙaci Gwamnati Ta Hukunta Fasto Emmanuel Garba?

Fasto Ɗan Ƙungiyar Hausawan Bogi Da Ya Zagi Annabi Ya Ɓoye

April 15, 2026
Sheikh Mutawakkil Mustapha Ya Zama Alƙalin Kotun Shari’a ta Ɗaukaka Ƙara ta Jihar Katsina

Sheikh Mutawakkil Mustapha Ya Zama Alƙalin Kotun Shari’a ta Ɗaukaka Ƙara ta Jihar Katsina

February 13, 2026

Ministan ya bayyana haka ne a ranar Asabar a Kaduna, yayin da ya ke jawabi a taron shekara wanda Cibiyar Faɗakar Da Jama’a ta Nijeriya (NIPR), reshen Jihar Kaduna, ta shirya.

Ya ce baki ɗayan kasafin 2024 an bijiro da shi ne bisa zurfafa nazarin manya da ƙananan ƙalubalen da ke fuskantar ƙasar nan, don haka ne aka tsara kasafin yadda zai fara da zaburar da hanyoyin bunƙasa ƙasa da kawo cigaba mai ɗorewa, inganta tattalin da kuma wanzar da yalwar arziki a ƙasa baki ɗaya.

Ya ce: “A cikin wannan satin ne Shugaba Bola Tinubu ya gabatar da Kasafin Kuɗi na 2024 na naira tiriliyan 27.5 ga Majalisar Tarayya, wanda shi ne kasafin sa na farko tun da ya kama mulkin sa. Kasafin kamar yadda ya gabatar da shi, bigire ne na fara taka tsanin tabbatar da cin nasarar Ajandar Saisaita Nijeriya, ta hanyar bada fifiko ga ƙudirorin gina ingantaccen tattalin arziki.

“Sannan kuma kasafin ya nuna yadda gwamnatin Tinubu ke taka-tsantsan da tsantseni wajen bada fifikon kashe kuɗaɗe a hanyoyin da su ka dace, domin ta hakan ake gina ginshiƙin tsarin tattalin arziki mai nisan zango.

“Yayin da Kasafin Kuɗi na 2024 ya tafi hannun majalisa domin yin nazari da tsettsefe shi, mu na da kyakkyawan yaƙinin cewa kasafin zai kasance matakin farko na bin turbar saisaita Nijeriya, kawo cigaba da inganta rayuwar ‘yan Nijeriya.”

Haka kuma Ministan ya ce kafin Shugaba Tinubu ya gabatar da kasafin, sai da ya yi ƙwarya-ƙwaryan kasafi, ya sa wa ƙudirori hannu sun zama doka, kuma ya kafa kwamitin shugaban ƙasa kan tsare-tsaren kuɗaɗe da tattalin arziki, kwamitin iskar gas (CNG), Shirin Bunƙasa Abinci, Shirin Tallafa wa Matsakaita da Ƙananan Masana’antu (MSME) da sauran fannoni masu muhimmanci wajen raya tattalin arziki.

Ya ce: “Muradin da ake so a cimma shi ne samar wa ɗan Nijeriya rayuwa cikin sauƙi, tare da gina tushen dawwamammen yalwar arziki.”

Ya ce tilas fa sai ‘yan Nijeriya sun bai wa wannan gwamnati uzirin cewa ta kama mulki a wani mawuyacin hali ne, amma kuma duk da haka shi Shugaban Ƙasa ya tarbi gaban kowane ƙalubalen da ake tunkara ko ya ke tunkaro ƙasar nan.

Ya ce, “‘Yan Nijeriya sun yi katarin samun shugaba wanda ke da ƙwarewa sosai a ɓangaren harkokin hadahadar tattalin arziki da kuma gogewa a gwamnatin jiha.

“Shugaba Tinubu ba mutum ne da zai yi ko gezau ba yayin da duk wani ƙalubale ya tunkare shi. Kuma da kan sa ya ce ba ya buƙatar a tausaya masa, domin shi ya nemi a ba shi shugabanci, saboda ya san zai iya.”

Previous Post

Shirin Rage Tsadar Rayuwa: Za A Fara Biyan Sabon Tsarin Albashi Daga Afrilu 2024 – Minista

Next Post

Related Posts

Ɓatanci Ga Manzon Allah: Musulmi Sun Buƙaci Gwamnati Ta Hukunta Fasto Emmanuel Garba?
Labarai

Fasto Ɗan Ƙungiyar Hausawan Bogi Da Ya Zagi Annabi Ya Ɓoye

April 15, 2026
Sheikh Mutawakkil Mustapha Ya Zama Alƙalin Kotun Shari’a ta Ɗaukaka Ƙara ta Jihar Katsina
Labarai

Sheikh Mutawakkil Mustapha Ya Zama Alƙalin Kotun Shari’a ta Ɗaukaka Ƙara ta Jihar Katsina

February 13, 2026
Bura women Celebrate Bukar Usman at 83
Labarai

Ƙungiyar Matan Al’ummar Bura Sun Karrama Dr. Bukar Usman Bisa Cika Shekaru 83

January 9, 2026
Next Post

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

RECOMMENDED NEWS

Are You Hungry for Success? Just Eat That Frog

Are You Hungry for Success? Just Eat That Frog

September 27, 2024
Auren Al-Amin Ciroma Da Wasila Isma’il: Kira Na Musamman Ga Dattawan Kannywood

Auren Al-Amin Ciroma Da Wasila Isma’il: Kira Na Musamman Ga Dattawan Kannywood

July 6, 2023
Kyautata Wa Marayu Da Mabuƙata Alheri Ne

Kyautata Wa Marayu Da Mabuƙata Alheri Ne

July 17, 2023
Governor Malam Dikko Constructs 75 New Secondary Schools Across Katsina State

Governor Malam Dikko Constructs 75 New Secondary Schools Across Katsina State

September 12, 2023

FOLLOW US

BROWSE BY CATEGORIES

  • Adabi
  • Addini
  • Babban Labari
  • Barkwanci
  • Dausayin Kauna
  • ENGLISH
  • Gizago
  • Gumbar Dutse
  • Hotuna
  • Labarai
  • Nishadi
  • Noma Da Kiwo
  • Sarauta
  • Shanshani
  • Sharhi
  • Sinadarin Rayuwa
  • Siyasa
  • Ta'aziyya
  • Wasanni

POPULAR NEWS

  • Gwamnan Katsina Ya Ƙi Amsar Kyautar Raguna 100 Daga Hannun Attajiri

    Gwamnan Katsina Ya Ƙi Amsar Kyautar Raguna 100 Daga Hannun Attajiri

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • Ta Tsinci Naira Miliyan 60 A Saudiyya Ta Miƙa Wa Hukuma

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • LUWAƊI DA YARA 14: Yadda Aka Bankaɗo Asirin Kabir Ɗan Hisba

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • Sojojin Najeriya Sun Kama Makashin Sarkin Gobir

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • BINCIKE: Zahirin Abin Da Ke Faruwa A BBC Hausa

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
Taskar Gizago

Follow us on social media:

Recent News

  • Fasto Ɗan Ƙungiyar Hausawan Bogi Da Ya Zagi Annabi Ya Ɓoye
  • Ɓatanci Ga Manzon Allah: Musulmi Sun Buƙaci Gwamnati Ta Hukunta Fasto Emmanuel Garba?
  • MARTABAR MANZON ALLAH (SAW)

Category

  • Adabi
  • Addini
  • Babban Labari
  • Barkwanci
  • Dausayin Kauna
  • ENGLISH
  • Gizago
  • Gumbar Dutse
  • Hotuna
  • Labarai
  • Nishadi
  • Noma Da Kiwo
  • Sarauta
  • Shanshani
  • Sharhi
  • Sinadarin Rayuwa
  • Siyasa
  • Ta'aziyya
  • Wasanni

Recent News

Ɓatanci Ga Manzon Allah: Musulmi Sun Buƙaci Gwamnati Ta Hukunta Fasto Emmanuel Garba?

Fasto Ɗan Ƙungiyar Hausawan Bogi Da Ya Zagi Annabi Ya Ɓoye

April 15, 2026
Ɓatanci Ga Manzon Allah: Musulmi Sun Buƙaci Gwamnati Ta Hukunta Fasto Emmanuel Garba?

Ɓatanci Ga Manzon Allah: Musulmi Sun Buƙaci Gwamnati Ta Hukunta Fasto Emmanuel Garba?

April 14, 2026
  • About us
  • Advertise
  • Careers
  • Contact

© 2023 Taskar Gizago - Ilimi da Nishadi

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
  • Sharhi
  • Gumbar Dutse
  • Dausayin Kauna
  • Gizago
  • Sarauta
  • Sinadari
  • Adabi da Nishadi
  • Barkwanci
  • Shanshani
  • Hotuna

© 2023 Taskar Gizago - Ilimi da Nishadi

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
This website uses cookies. By continuing to use this website you are giving consent to cookies being used.