ƘUNGIYAR HAUSAWA ZALLA: TA INA ZA A FARA KUMA DA WACE MANUFA? (3)
Daga Yahuza Malumfashi

Mece Ce Manufar Kafa Ƙungiyar Hausawa Zalla?
A wannan muƙala, a yau za mu yi ninƙaya ne a cikin kogin wata muhimmiyar tambaya, mai cewa, shin mece ce manufar kafa Ƙungiyar Hausawa Zalla? Shin alheri aka nufa ko kuwa sharri?
Masu salon magana dai sun ce, sonsomin hauka, zubar da miyau. Haka kuma sun ce, Juma’ar da za ta yi kyau, tun daga Laraba ake gane ta. Kamar kuma yadda suka ce, sanin asali, shi ke sanya kare gurgurar alli. Duka dai, masu azancin na magana sun ce, nuna mani abokinka, ni kuma in gaya maka ko kai wane ne.
Daga dukkan alamu, babu alheri, babu gaskiya, babu mutunci a batun samar da wannan ƙungiya ta Hausawa zalla. Shin wane dalili ne ya sanya na ce haka? Ku yi haƙuri ku biyo ni. Da sannu zan rarrabe maku zare da abawa. Zan bakace maku tsakanin aya da tsakuwa.
Dalili na ɗaya, me ya sanya masu ƙumajin kafa ƙungiyar nan suke ta zagaye-zagaye, suna ta kai gwauro da mari da yasassun zantuttuka a soshalmidiya, game da ƙungiyar, tun ma kafin su kafa ta?
A tsarin tunani mai kyau, idan har ƙungiyar alheri ake son kafawa, to kai tsaye za a tunkari al’amarin, bisa doron doka. Maimakon kwarmato da habaice-habaice da zage-zage da zarge-zarge da ƙullatar wasu al’umma na daban da ‘ya’yan ƙungiyar suke yi tun kafin a kafa ta, da kawai za su tafi Hukumar Yi Wa Kamfanoni da Ƙungiyoyi Rijista (CAC), su gabatar da takardar buƙatarsu; su cika dukkan sharuɗɗan da doka ta tanada, domin samun rijista salun-alun, kamar yadda duk wata ƙungiya ta Allah da Annabi take yi.
Amma ina! Maimakon haka sai masu Ƙungiyar Hausawa Zalla suka fara saƙa da mugun zare. Tun ma kafin a je ko’ina, duk inda ka ga zancensu a soshalmidiya, to zance ne mai kaushi. Zance ne ko dai na zagi ko kuma na tsokanar fitina, ko kuma na kawo saɓani da rashin jituwa tsakanin al’umma.
Kuma za ka ga cewa ba su son a yi masu wata tambaya ko ƙalubale da ya saɓa wa ra’ayinsu. Cikin lokaci za ka ga sun azazzalo da zage-zage da yarfe da halayya irin ta a-ware da nuna bambanci da baƙin ƙabilanci.
Shin duk ƙungiyar da ke nufin al’ummar ƙasa da alheri, anya za ta riƙa nuna waɗannan baƙaƙen halaye ga sauran al’umma? Kayya! – Lallai akwai lauje cikin naɗi.
Jama’a, nan zan ɗiga aya. Sai a tari kashi na gaba, domin amsa dalilan da ke tabbatar da cewa, babu shakka Ƙungiyar Hausawa Zalla ba da alheri ta taho ba.
Wassalam
__________
Bashir Malumfashi, shi ne Editan Mujallar Taskar Gizago (online).











