• About us
  • Advertise
  • Careers
  • Contact
Thursday, September 10, 2026
  • Login
Taskar Gizago
Advertisement
  • Gida
  • Labarai
  • Sharhi
  • Gumbar Dutse
  • Dausayin Kauna
  • Gizago
  • Sarauta
  • Sinadari
  • Adabi da Nishadi
  • Barkwanci
  • Shanshani
  • Hotuna
Taskar Gizago
No Result
View All Result
Home Labarai

Katsina A Makon Jiya (Kashi Na Ɗaya)

DIKKON KATSINAWA

Bashir Yahuza Malumfashi by Bashir Yahuza Malumfashi
August 10, 2026
in Labarai
0
Katsina A Makon Jiya (Kashi Na Ɗaya)

Dikkon Katsinawa (05)

24
VIEWS
Share on FacebookShare on TwitterWhatsappEmail a Friend

Katsina A Makon Jiya (Kashi Na Ɗaya)

Daga Bashir Yahuza Malumfashi
__________
Gwamnatin Jihar Katsina, a ƙarƙashin shugabancin Gwamna, Dr. Dikko Umar Radda, PhD. CON, ta samu gagarumar nasarar aiwatar da manyan ayyuka a makon da ya gabata, ayyuka masu muhimmanci da za su taɓa rayuwar al’ummar jihar da alheri kuma su bunkasa jihar baki ɗaya.

Related posts

Gwamna Radda Zai Ƙarfafa Ayyukan Gidauniyar Zanna Tukur Tingilin

Gwamna Radda Zai Ƙarfafa Ayyukan Gidauniyar Zanna Tukur Tingilin

September 8, 2026
Matasa Ku Ƙara Himma Domin Dogaro Da Kai – Gwamna Radda

Matasa Ku Ƙara Himma Domin Dogaro Da Kai – Gwamna Radda

September 6, 2026

Aiki na farko kuma mai muhimmanci da ya gudana a makon da ya gabata, shi ne inda mai girma Gwamna Dikko ya ƙaddamar da aikin faɗaɗa titin cikin garin Mashi mai tsawon kilomita uku. Wannan aiki, wani babban mataki ne na ƙara inganta ababen more rayuwa da bunƙasa tattalin arzikin jihar.

Aikin, wanda zai gudana a kan babbar hanyar Katsina zuwa Daura, yana daga cikin Shirin Sabunta Birane na gwamnatin jihar da ake aiwatarwa ƙarƙashin manufar “Building Your Future,” yayin da Kamfanin Mothercat Nigeria Limited zai gudanar da shi ƙarƙashin kulawar Ma’aikatar Ayyuka, Gidaje da Sufuri ta Jihar Katsina.

Da yake jawabi yayin ƙaddamar da aikin, Gwamna Radda ya bayyana cewa titin zai taimaka wajen inganta zirga-zirga, ƙara tsaron masu amfani da hanya, sauƙaƙa jigilar amfanin gona da sauran kayayyaki zuwa kasuwanni da rage kuɗaɗen sufuri, tare da ƙarfafa harkokin kasuwanci da tattalin arziki a Mashi da ma yankunan da ke kewaye da ita.

Katsina A Makon Jiya (01)

Aiki na biyu kuma mai muhimmanci da ya gudana a Jihar Katsina, a makon da ya gabata, shi ne wanda mai girma Gwamna ya rantsar da sabbin Manyan Sakatarori guda huɗu.

Bikin rantsarwar ya gudana ne a ranar Laraba, 5 ga Agustan 2026, a Gidan Gwamnatin Jihar Katsina. Kuma sabbin Sakatarorin da aka rantsar sun haɗa da Malam Abdu Usman, Dakta Sani Suleiman, Dakta Shamsuddeen Yahaya Suleiman da Dakta Hussaini Hamisu Yanduna.

Da yake jawabi bayan rantsar da su, Gwamna Raɗɗa ya bayyana cewa an zaɓi sabbin jami’an ne bisa cancanta, ƙwarewa da jajircewa wajen aiki, ba tare da la’akari da alaƙa, sanayya ko wani tasiri na daban ba.

Ya buƙaci sabbin Sakatarorin da su gudanar da ayyukansu cikin gaskiya, riƙon amana da adalci, yana mai bayyana cewa irin waɗannan kyawawan ɗabi’u ne za su taimaka wajen ƙara inganta ayyukan gwamnati da kuma samar da ingantacciyar hidima ga al’ummar Jihar Katsina.

Babban aiki na uku kuma muhimmi da ya gudana a Jihar Katsina, a makon da ya gabata, aiki ne na tarihi a Ƙaramar Hukumar Zango. Wannan kuwa shi ne yadda mai girma Gwamna Malam Dikko Umaru Radda ya ƙaddamar da sabon Babban Asibiti a Zango, wanda shi ne babban asibiti na farko da aka kafa a tarihin Ƙaramar Hukumar.

Bikin ya gudana ne ranar Alhamis da ta gabata, 6 ga Agusta, 2026, inda gwamnatin jihar ta bayyana aikin a matsayin wani muhimmin mataki na inganta tsarin kiwon lafiya da kuma faɗaɗa ayyukan jinya ga al’ummar jihar.

Da yake jawabi, Gwamna Radda ya gode wa Allah Maɗaukakin Sarki bisa bai wa gwamnatinsa damar kammala aikin, yana mai bayyana cewa an samar da sabon asibitin ne ta hanyar ɗaga darajar tsohuwar Cibiyar Kiwon Lafiya ta Matakin Farko da ke Zango zuwa cikakken Babban Asibiti.

Ya jaddada cewa harkar lafiya na ci gaba da kasancewa ɗaya daga cikin manyan abubuwan da gwamnatinsa ta bai wa fifiko, tun bayan hawansa mulki. Ya lissafo nasarorin da aka samu cikin shekaru uku da suka gabata, waɗanda suka haɗa da ɗaga darajar cibiyoyin kiwon lafiya guda huɗu zuwa Manyan Asibitoci, inganta wasu cibiyoyin lafiya, gyaran manyan asibitoci da ɗakunan tiyata, farfaɗo da cibiyoyin kiwon lafiya na matakin farko (PHCs) sama da 280, da ɗaukar sabbin ma’aikatan lafiya guda 804 aiki.

Wannan ne kuma ya kawo mu ga muhimmin aiki na gaba, wanda ya gudana duk a cikin wannan mako da ya gabata. Wannan kuwa shi ne, yadda Hukumar Kula da Ma’aikatan Ƙananan Hukumomin Jihar Katsina ta kafa wasu sabbin sassa guda biyu masu muhimmanci. Waɗannan kuwa su ne, Sashen Kula Da Sayayyar Kayayyaki da kuma Sashen Bunƙasa Rayuwar Mata.

Kamar yadda bayani ya gabata, an kafa sassan ne a matsayin wani ɓangare na ƙoƙarin ƙarfafa shugabanci nagari, inganta gaskiya da riƙon amana da kuma inganta ayyukan da ake gudanarwa ga al’umma a dukkan ƙananan hukumomi 34 na jihar, kamar yadda shugabannin hukumar suka bayyana.

An ƙaddamar da wannan sabon tsari ne ƙarƙashin jagorancin Shugaban Hukumar, Alhaji Usman Mamman Maska, a matsayin wani ɓangare na sauye-sauyen hukumomi da ake ci gaba da aiwatarwa, waɗanda aka tsara domin inganta ingancin aiki, daƙile almundahana da kuma tabbatar da tsarin shugabanci mai bai wa kowa dama a matakin ƙananan hukumomi.

Sanarwar ta ruwaito Gwamnan Jihar Katsina, Malam Dikko Umaru Radda, yana bayyana wannan mataki a matsayin wani sabon ci gaba a ƙoƙarin gwamnatinsa na ƙarfafa gaskiya, riƙon amana da ingancin gudanar da harkokin ƙananan hukumomi.

“Ƙarfafan hukumomi su ne ginshiƙin samun ci gaba mai ɗorewa. Za mu ci gaba da tallafa wa sauye-sauyen da ke inganta shugabanci nagari da kuma inganta ayyukan da ake samarwa ga al’umma a matakin ƙasa,” in ji Gwamna Radda, kamar yadda aka ruwaito.

Wadannan su ne kaɗan daga cikin ɗinbim muhimman ayyukan da suka gudana a Gwamnatin Jihar Katsina a makon da ya gabata, a ƙarƙashin jajircewar hadimin al’umma, Gwamna Malam Dikko Umaru Radda, PhD. CON.

Kuma da haka muke yin bankwana da fatan Allah ya kai mu ƙarshen wannan makon, domin mu ci gaba da kawo maku rahoton manyan ayyukan raya al’umma da suke gudana a Gwamnatin Dikkon Katsinawa. Mu huta lafiya.
__________

Previous Post

Ya Zama Wajibi A Tallafa Wa Matasa A Masarautar Galadiman Katsina

Next Post

Ɗalibin Jami’ar Sojoji Ya Ƙera Robot Mai Kashe Gobara

Related Posts

Gwamna Radda Zai Ƙarfafa Ayyukan Gidauniyar Zanna Tukur Tingilin
Labarai

Gwamna Radda Zai Ƙarfafa Ayyukan Gidauniyar Zanna Tukur Tingilin

September 8, 2026
Matasa Ku Ƙara Himma Domin Dogaro Da Kai – Gwamna Radda
Labarai

Matasa Ku Ƙara Himma Domin Dogaro Da Kai – Gwamna Radda

September 6, 2026
Katsina A Makon Jiya (Daga 24 Zuwa 30-08-2026)
Labarai

Katsina A Makon Jiya (Daga 24 Zuwa 30-08-2026)

August 31, 2026
Next Post
Ɗalibin Jami’ar Sojoji Ya Ƙera Robot Mai Kashe Gobara

Ɗalibin Jami'ar Sojoji Ya Ƙera Robot Mai Kashe Gobara

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

RECOMMENDED NEWS

GOBARA DAGA KOGI: ‘Yan Bindiga Sun Farmaki Fadar Gwamnatin Amurka

GOBARA DAGA KOGI: ‘Yan Bindiga Sun Farmaki Fadar Gwamnatin Amurka

November 27, 2025
Gwamnatin Kano: Rushe Gidajen Mutane Zalunci Ne

Gwamnatin Kano: Rushe Gidajen Mutane Zalunci Ne

June 17, 2023
RAMADAN KARIM: 21-1447

RAMADAN KARIM: 21-1447

March 10, 2026
Koyaushe Talakka Zai Fita Daga Ƙuƙumi?

Koyaushe Talakka Zai Fita Daga Ƙuƙumi?

June 2, 2023

FOLLOW US

BROWSE BY CATEGORIES

  • Adabi
  • Addini
  • Babban Labari
  • Barkwanci
  • Dausayin Kauna
  • ENGLISH
  • Gizago
  • Gumbar Dutse
  • Hotuna
  • Labarai
  • Nishadi
  • Noma Da Kiwo
  • Sarauta
  • Shanshani
  • Sharhi
  • Sinadarin Rayuwa
  • Siyasa
  • Ta'aziyya
  • Wasanni

POPULAR NEWS

  • Gwamnan Katsina Ya Ƙi Amsar Kyautar Raguna 100 Daga Hannun Attajiri

    Gwamnan Katsina Ya Ƙi Amsar Kyautar Raguna 100 Daga Hannun Attajiri

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • Ta Tsinci Naira Miliyan 60 A Saudiyya Ta Miƙa Wa Hukuma

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • LUWAƊI DA YARA 14: Yadda Aka Bankaɗo Asirin Kabir Ɗan Hisba

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • Sojojin Najeriya Sun Kama Makashin Sarkin Gobir

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
  • Tarihin Waƙar Yaƙin Tabuka

    0 shares
    Share 0 Tweet 0
Taskar Gizago

Follow us on social media:

Recent News

  • Shugaba Tinubu, Manyan Sojoji, Mutallab, Mangal, Sarki Sanusi II Za Su Halarci Ƙaddamar Da Littafin Janar Buratai
  • Wane Ne Ya Kashe Ɗan Shagamu?
  • SANATA BELLO MANDIYA: Mun Yi Babban Rashi – Gwamnan Katsina

Category

  • Adabi
  • Addini
  • Babban Labari
  • Barkwanci
  • Dausayin Kauna
  • ENGLISH
  • Gizago
  • Gumbar Dutse
  • Hotuna
  • Labarai
  • Nishadi
  • Noma Da Kiwo
  • Sarauta
  • Shanshani
  • Sharhi
  • Sinadarin Rayuwa
  • Siyasa
  • Ta'aziyya
  • Wasanni

Recent News

Shugaba Tinubu, Manyan Sojoji, Mutallab, Mangal, Sarki Sanusi II Za Su Halarci Ƙaddamar Da Littafin Janar Buratai

Shugaba Tinubu, Manyan Sojoji, Mutallab, Mangal, Sarki Sanusi II Za Su Halarci Ƙaddamar Da Littafin Janar Buratai

September 10, 2026
Wane Ne Ya Kashe Ɗan Shagamu?

Wane Ne Ya Kashe Ɗan Shagamu?

September 9, 2026
  • About us
  • Advertise
  • Careers
  • Contact

© 2023 Taskar Gizago - Ilimi da Nishadi

No Result
View All Result
  • Gida
  • Labarai
  • Sharhi
  • Gumbar Dutse
  • Dausayin Kauna
  • Gizago
  • Sarauta
  • Sinadari
  • Adabi da Nishadi
  • Barkwanci
  • Shanshani
  • Hotuna

© 2023 Taskar Gizago - Ilimi da Nishadi

Welcome Back!

Login to your account below

Forgotten Password?

Retrieve your password

Please enter your username or email address to reset your password.

Log In
This website uses cookies. By continuing to use this website you are giving consent to cookies being used.